12) Mallaka: To dama shugabanci a gida na maigidan ne, me ya sa wasu matan ke ƙoƙarin karbewa daga hannunsa ya koma nasu? abin da mutane ke zato shi ne uwargida na son ta riƙa karbe duk abin da ya samo ne sai wanda ta miƙa masa. Da ta ce ba ni kaza nan da nan zai je ya nemo jiki na rawa ya ba ta. Amma daga baya an fara gano cewa ba wannan ne kadai ke sa su nemi mallake mijin ba, akwai abubuwa da dama masu kama da juna.
Bincike ya nuna cewa irin matan da suka sami kan namiji ba shi kadai suke mallaka ba har da sauran matan da ke ƙarƙashinsa da ma uwayensa gaba daya, haka za a zauna in ba su da zarafin korar sauran. An sami gidan da kishiya ba ta iya dora abinci sai 'yar mowa ta ba ta abin da za ta dafa, bayan kuwa dukansu matan mutun guda ne. An kai matsayin da kishiya ke iya ladabtar da matar maigida saboda ta saba umurninta, ko a gaban maigidan ne sai dai ya zura ido ba abin da zai iya.
In tana son wani abu sai dai ta biyo ta hannunta, in kuwa ta wuce kai tsaye ta tambayi shi nan take zai ce ta koma ta biyo ta hanyar da ta dace. Ka iya cewa matar ta auri mutum biyu, mijinta da matarsa. Akwai wani a gida a karkara inda uwargidar ce ke ba da duk abubuwan da ake buƙata, daga icce har kudin cefane, in girki za a yi ita ce mai yi sai ta ga dama amaryar ta girka, in ba haka ba kuma ita za ta dafa. abin da ban sani ba kuma ba damar tambaya shin shimfidar ma ita ke karbewa ko ta tsaya a girkin ne kawai? Ko ma ya abin yake masu mallakar mazan ba don kudin maigidan ba ne kawai, har da mallake kishiya in tana ciki, ko a hana ta shigowa.
Galibin wadanda suka mallake mazan kiyoshinsu ba su jin dadi. Kodai su azabtar da kishiyar da hannunsu, ko su ja da baya su turo maigidan ya zartar da abin da suke buƙata, komai girmansa komai iliminsa kuwa. Ga cutarwa a zahiri amma ba wanda ya isa ya tunkari mijin ya gaya masa gaskiya saboda an riga an tura masa aljani ya rikita masa ƙwaƙwalwa. Wadanda za su iya tunkarar uwargidar su yi mata magana ko sun yi sai ta ce ba laifinta ba ne, mijin ne, ita ma haka yake mata, ta yi duk ƙoƙarinta ne ta gaji ta watsar, a zahiri kuwa da umurninta yake yin komai ta riga ta shanye shi a allo.
Irin wannan in ka ga amaryar ta sami sauƙi to dayan uku ne: Ko dai tsafin da aka yi ya karye, ko wace ta yi ta mutu, ko kuma an saki wace ake wahalarwar, wannan ne kawai. Da yawa za ka ga wadanda suke mallake mazan ma sun fi kama-sayar, to don me suke mallake su me suke buƙata a wurinsu? Kawai mallake gidan suke so su yi gaba daya, wanda mijin ma yana ciki, abin da suke so shi za a yi. Wasu kan ce wallahi suna neman maganin mallakar ba wai don su riƙa cutar da mijin ne ba, kawai dai ba sa son a kawo musu wata ne da za ta wargaza musu gida bayan sun yi shekara da shekaru suna neman gyara shi.
Amma fa manufarsu gidan ya ci-gaba da zama ƙarƙashinsu ne, ba wata maganar ƙara aure da mijin zai fuskance su da ita, sai in sun ga dama su ce masa bismilla, da a ce uwayen wani mijin sun fi ƙarfinsa suka takura shi kan sai ya ƙaro mata, uwargidan za ta zuba musu ido amaryar ta shigo, ko tsabar wahala ta fitar arziƙi ta isa ta fitar da ita. Galibin abubuwan da suke faruwa ke nan a gidajenmu. Shi ya sa wani lokacin nake ganin raba wa mata gida abu ne mai matuƙar amfani, wasu kan cutu don suna rayuwa ne a gida daya.
Na taba ganin wani maigida yana ta huci da kumburi wai matarsa ta yi masa satar wani abu, da aka bincika sai ya ce uwargidarsa ce ta gaya masa, wani kuma ya riƙa bin matarsa a boye ya kuma zuba wadanda za su riƙa saka mata ido, ya zarginta da bin maza, shi ma wai uwargidar ce ta gaya masa abin da kishiyar take yi. Wasu duk wulaƙancin da suke wa matansu za ka taras kiyoshinsu ne suka gaya musu. Ba cewa na yi ba sa fadar gaskiya ba kishiya ce fa. Akwai wani ƙanin miji da ya ji amaryar na cewa wallahi sai ta fitar da uwargidar bayan tana da yara da yawa.
Nan fa ya yi maza ya fada wa yayansa abin da ya ji, yayan ya dauki mataki sai dai duk da haka sai da ta yi nasarar shiga tsakaninsu. In kana neman gaulan namiji ka sami wanda sha'awa ta gama da shi to ka yi fatiha kawai ka tashi. Da kunnena na ji wanda yake cewa "Wallahi in matata na son ta mallake ni da kaina zan kai ta wurin malamin" ka ga a hankalce wannan ai zararre ne ko? kamata ya yi ya rabu da ita gaba daya idan ya gano saboda ba ta gida da take yi ko za ta yi, wai shi zai kai ta da kansa. Wannan yaranta ce ko hauka?!.
Anan Zan
Dakata Sai Mun Haɗu a Rubutu Na Gaba.
**************************
Daga: ✍ Baban Manar Alƙasim
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin rubuce-rubuce da ke cike da faɗakarwa da ilimantarwa, waɗanda ake samarwa daga Zauren Markazus Sunnah. Ku bibiye su a kafafensu na sada zumunta domin samun ƙarin bayani. Amsoshi ba ta da haƙƙin mallakar waɗannan rubuce-rubuce, amma tana ɗora su ne da izinin Baban Manar Alƙasim.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.