Ticker

6/recent/ticker-posts

KISHI RAHAMA NE KO AZABA // 25

13) FUSHI: Wani lokaci masoyi kan riƙi abokin zamansa a zuciya saboda wani  abin da bai tabbatar ba, koda yana cikin fara'a da mutane da ya hadu da shi sai ka ga ya murtuke fuska. Mace kan yi ta hira da kiyoshinta da yaranta cikin raha da annashuwa, da zarar ta ji shugowar maigidanta sai ka ga komai ya canja. Nan za ta ba ta rai ta hada fuska. In magana ya yi da ita sai ta ga dama ta ba shi amsa, in kuma maras tarbiyya ce ta jefa masa duk  abin da ya fito bakinta.

Sau tari hakan kan faru a lokacin da ta lura yana kallon hotunan mata a wayarsa, ko kuma ta kama shi yana hira da wata ta kafar sadarwa ita kuma ba za ta iya titsiye shi a kan haka ba. Wata ta taba zuwa tana ta kuka wai ta kama mijinta yana kallon fima-fiman batsa, wata kuwa tashin hankali ta shiga wai mijin yana wasa da gabansa, duka dai damuwa ne a dalilin kishinsu da  abin da mazan ke yi don dukansu sai da suka ce meye amfaninsu a gidan mazajensu bayan ba tare suke ba. Akwai matar da ta dena magana da mijin na tsawon wuni guda cur wai don ya yi kuskurenta da sunan kishiyar. Kishi ne dai.

Ana lura da irin wannan fushi a matsayin alama dake nuna kishin mutum, kamar mace in ta yi shi takan lura da  abin da ka fi so ta fito maka tanan. Na sha ganin inda uwa kan kirbi yaranta a dalilin fushin da take yi da babansa. In ta fusata ba mijin ba kowa ya shiga ciki, don ba  abin da ya hada ta da yarantar 'ya'yanta, tana iya ƙin dafa abinci saboda kawai maigidan ya fahimci inda ta kai, in ma ya tambaye ta ko ta dafa abinci nan take za ta gaya masa cewa ba ta dafa ba. Ba kuma wani dalili.

Wani lokacin za ka taras da yaran suna kuka alamar yunwa ta gallabe su, amma ita ko a jikinta, in ya ce "Me ya sa?" cikin sauƙi za ta ce ya je gidan daya matar ko budurwarsa ya dauko musu abinci ai ba ita kadai ce ba tare da shi. Na sha ganin mazajen dake fita waje don su sayo wa yaransu abinci bayan ga uwarsu na zaune a cikin gida lafiyarta lau dafawan ce kawai ba za ta yi ba. Abin haushi irin wannan fushin ba ƙarewa zai yi ba tunda kishin ba mutuwa zai yi ba. Wani sa'in matar kan ƙi dafa abinci in mijin ya dafa ta lanƙwame shi gaba daya kuma ta yi mursisi.

Duk irin wannan fushi ba wani abune mai damuwa sosai ba wanda mace za ta ƙare a kan dan kishiya shi ne mai damuwa sosai. Yaron da bai da laifi bai san  abin da ke tsakaninki da mamansa ba, in ma kika yi masa riƙo na sosai zai zata ke ce mahaifiyarsa. Na ga matar da kishiyarta ta mutu wurin haihuwa lokacin tana da ƙaramin goyo, haka ta hada su a matsayin tagwaye ta shayar da su ta yaye su lokaci guda ba ta rabewa tsakaninsu, har lokacin da yaron ya kamu da cuta mai tsanani bayan ya dan tasa.

Matanan duk ta hana kanta sukuni ita ce nemo wannan da wancan ba za ka taba sanin cewa dan kishiya ba ne, sai wata rana yaron duk da ƙaramar shekararsa yake cewa "Mama duk  abin da kike min na gode" daganan ya ce ga-garinkuna. Tsakani da Allah ko mu mun tausaya sosai ganin tashin hankalinta bayan ga danta na cikinta yana lafiya ba  abin da ya same shi. Duk lokacin da fushin kishiya zai tsallaka kan yaron da bai ji ba bai gani ba mummunan kishi ne wanda zai iya halakar da mace ya hana ta shiga aljanna.

Akwai nau'in dukan da mace ke yi wa yaron kishiyarta wai don ta yi fushi, a zahiri ko kusa ba za ta yi wa danta ba, wani irin fushi ne zai sa mace ta tsattsaga yaron kishiya da reza, ko ta saka shi ya kwana a ƙasa ba riga a kan tiles lokacin sanyi wai don ya yi mata fitsari a kan gado? Akwai abubuwa masu ban mamaki da mata ke yi lokacin da suka fusata a kan dan kishiya wanda ko kusa ba za su kwatanta rabinsa ba a kan yaransu. A taƙaice dai kishin uwayensu ya tsallako kansu kenan.

Kamar maza in suka yi irin wannan fushi mafita kawai su bar gidan hankali kwance, namijin da zai yi fushi a kan kishi in dai zai yi magana za ta iya kaiwa ga zargi, wannan kuwa yana da babban tasiri a tsakanin ma'aurata. Wani fada yake yi kawai don ya saka dokar cewa kar ta kai magariba a waje, dalili ya sa ta kai kusan issha, da ya zo yi mata fada ta daga harshenta a kansa a ƙarshe ya ce "Mace in ba mazinaciya ba mai zai sa ta kai har issha a waje, me take yi?" Sam bai nufin  abin da ya fada, fushi ne ya kai shi ga wannan kishi.

A ƙarshe auren ya nemi lalacewa, an gyara amma matar ba ta manta ba. Fushi ya kai su haka, da ta yi shuru da shikenan zai yi fade-fadensa a wuce wurin, wasu masu kishin ai ce wa matan suke subar gidan kafin gari ya waye kar su dawo gida sai gari ya yi duhu don kar wasu mazan su gansu. ke nan ko a kishin akwai sabani, wani kan yi saki a kan dalilin da wani mai kishin yake umurni da a yi. Duk wanda ya fusata ya yi shuru saboda tsoron abkawa ga nadama a lokacin da abu ba zai gyaru ba.

Anan Zan Dakata Sai Mun Haɗu a Rubutu Na Gaba.

**************************
Daga:  Baban Manar Alƙasim
**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin rubuce-rubuce da ke cike da faɗakarwa da ilimantarwa, waɗanda ake samarwa daga Zauren Markazus Sunnah. Ku bibiye su a kafafensu na sada zumunta domin samun ƙarin bayani. Amsoshi ba ta da haƙƙin mallakar waɗannan rubuce-rubuce, amma tana ɗora su ne da izinin Baban Manar Alƙasim.

Kishi Rahama Ne Ko Azaba

Post a Comment

0 Comments