Ticker

KISHI RAHAMA NE KO AZABA // 26

14) BOYE-BOYE: Wani abu dake saurin daga kishin bangarori guda biyu shi ne wani ya fara fahimtar cewa dayan na boye masa wani abu, da a ce mace ba ta damu da wayar mijinta ba, in zai bar ta a falo ya shiga wanka ba  abin da zai ja hankalinta har ta buƙaci kusantarta balle ta ce za ta duba wani abin. Amma idan ta ga ya garƙama wa wayar kwado za ta fara tambayar kanta to me ya sa ya kulle wayar?

Kodai yana neman wata ne? To bare a ce ya kasa daga wayar saboda tana wurin, yana ta kallonta, ko in ya dauka ya fita, bayan a da ba haka yake yi ba, ƙila yakan bar mata ta yi 'game' ko ta yi dube-dubenta yanzu me ya sa yake ƙin ba ta? Me yake boyewa? Wannan zai jawo kishinta ta fara fito na fito da shi da ƙoƙarin daukar wayar don sanin wace yake soyayya da ita. Me ya sa yake ƙoƙarin canja batu a lokacin da ta same shi yana tsakiyar magana? Duk wadannan alamu ne da suke nuna rashin gaskiya.

Macen da wani namiji ya fara magana da ita bayan tana da aure ko tana da wanda take so, ta tsawatar da shi cewa ita fa matar aure ce ya ƙi ji. To wannan yana so ne ya jefa ta a matsala, zai iya ba ta mata aure ba  abin da ya dame shi, koda kuwa bai da niyyar aurenta ya dai aiwatar da  abin da yake so.  abin da ya dace anan kawai ta fara fada wa maigidan kai tsaye ga  abin da yake faruwa kar ta boye komai. Boyewar ita ce babbar matsala gare ta kuma za ta iya ba ta mata aure. Shi maigidan ya san tana da waya, kuma ya san cewa kowa zai iya bugo mata.

Kenan bugo mata da wancan ya yi ba matsala ba ce, boyewar da ta yi ce matsala. In ma ba ta iya gaya masa ba za ta iya bari in ya bugo ta ba shi lokacin da ta san maigidan yana gida, da ys bugo a lokacin ta hada su ta ga ƙaryar rashin kunya. In duka wannan ba zai yiwu mata ba, ta ba maigidan wayarta ta ce in an bugo kar ya daga har sai wanda ya bugo din ya fara magana. Ta ce wani ne ke son ya dame ta. Wannan ba zai sa maigidan ya dauke ta maras gaskiya ba.

Asali kar ta taba boye masa wani abu, don in ya binciko daga baya ransa zai yi mummunan baci, kishi zai taso masa wani ma zai kai shi ga zarginta da ƙulla wata alaƙa a bayan idonsa. In yara take da su ta gaya masa gaskiya don ko ba jima ko ba dade zai sani. Mun yi magana a baya ta dalilan da suke sa namiji ya saki mace in ya gano cewa ba budurwa ya aura ba. Kishi ke kai shi ga yin haka, ta yadda wani ya riga shi inda yake zaton cewa shi ne na farko. A taƙaice in an sa idon kula wannan ma kishi ne.

Akwai wanda na ji ya ce ba zai auri bazawara ba, da na tambaye shi dalili sai ya ce "Ragowa ce fa! Ai ka dauko sabuwa fal a leda alhaji" shi ma kishin ne dai. Ko a 'yammata kar ta boye wa wanda take so komai, in wani ya bullo mata daga baya ta fada wa wanda take so komai ko ya zo ya same su ba wata matsala, amma lokacin da za ta fara ƙoƙarin boye masa da cewa abokin karatunta ne, ko yayanta ne, ko saurayin ƙaninta ne. Duk lokacin da ya fahimci gaskiya daga baya abin ba zai yi kyau ba.

Galibi kishin maza kan taso ne ya yi tsanani sosai lokacin da suka fahimci 'yan matan na boye musu wani abu, kamar dai akwai boyayyiyar soyayya tsakaninta da wanda take boyewar. Anan dole mu raba abin zuwa gida biyu, misali: A Kano in ba a daura aure da kai ba komai zai iya faruwa, mace allura ce a cikin ruwa mai rabo ka dauka. In namiji ya yi kishi mai zafi a lokacin da ya fahimci tana boye masa wata alaƙa ba laifi.

A Zaria mace ba ta da ƙarfin da za ta shiga cikin maganar aure, in uwayen suka ce sun ba da ita ba kasafai za ta iya kawo wani ba bare har a kai ga matsayin boye-boye. Nan ba dole ne ma saurayin ya fahimci akwai wani da ake masa boye-boye ba. Wannan hassashen fa na galibin  abin da yake faruwa ne ba wai kowa haka yake ba. Ana samun 'yan canje-canje daga Kano zuwa Zaria. Ko ya abin yake babu wani dalili da mace za ta riƙa boye wa saurayinta wani abu, ko shi ya boye mata.

Anan Zan Dakata Sai Mun Haɗu a Rubutu Na Gaba.

**************************
Daga:  Baban Manar Alƙasim
**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin rubuce-rubuce da ke cike da faɗakarwa da ilimantarwa, waɗanda ake samarwa daga Zauren Markazus Sunnah. Ku bibiye su a kafafensu na sada zumunta domin samun ƙarin bayani. Amsoshi ba ta da haƙƙin mallakar waɗannan rubuce-rubuce, amma tana ɗora su ne da izinin Baban Manar Alƙasim.

Kishi Rahama Ne Ko Azaba

Post a Comment

0 Comments