KISHI RAHAMA NE KO AZABA // 27

    15) DAUKAR MATAKI: Wannan ma daya ne daga cikin abubuwan da ake gane cewa kishi ya kama mutum, koda kuwa namiji ne shi ko mace. Sai dai babban matakin da namiji zai iya dauka in kishi ya maƙuro shi a wannan matattarar tamu shi ne duka, ya manta cewa matarsa ce uwar 'ya'yansa, marufin asirinsa. Bayan ya lakada mata na jaki a ƙarshe kuma ya sake ta, dalilin kebe matattararmu kuwa saboda wasu mattarun suna da bambanci ta wurin zafinsu, ko addini, ko fahimta.

    Misali: Na ga wasu a kotu ana Shari'a inda yake cewa dan da ta haifa ba dansa ba ne, ya kama ta da wani namijin ba sau daya ba ba biyu ba, a kan gadonsa. AlÆ™alin ta yi mamaki, ta tambayi matar ko haka ne, matar ta ce Æ™warai amma ai ta ba shi haÆ™uri, ta ce "Bai kamata ba kuma in da mutunci ya dauki matakin da zai ce dana ba dansa ba ne" Anan ba wani  abin da ya yi wa saurayinta da yake shigo masa gida ya sadu da iyalinsa, ban sani ba ko tsoron doka ne ko kuma su fahimtarsu ke nan a al'adance, Æ™arshe dai ya dauki matakin ture danta da cewa ba nasa ba ne.

    A wannan kotun dai wani soja ke fadin ya sami matarsa da wani mutum, har ana jayayya wurin cewa dan nasa ne ko ba nasa ba tsakaninsa da mutumin, to in soja ma bai dauki matakin duka ko ƙoƙarin kisa ba ƙila su a matattararsu abu ne mai sauƙi. Sai dai na karanta wani hadisi da Annabi SAW yake magana da sahabbansa kan wanda zai sami wani a kan iyalinsa, sai wani sahabi (Sa'ad RA) ya ce ai nan take zai zaro takobi ya fille masa kai.

    Wannan kishi ne, matakin da zai iya dauka shi ne kisa ba sai ya jira an kai wa hukuma ba. Nan take Annabi SAW ya tabbatar masa da cewa shi mai kishi ne, kuma ya fi shi kishi Allah SW ya fi su, ya ce a kishin mahalicci ne ya hana a hada shi da wani. Anan in musulmi ya yi kishi mun san inda ya dauko, koyarwa ce ta shari'a mutum ya yi kishi, sai dai irin matakin da ya kamata ya dauka shari'ar ta sake tanadar da shi.

    Ina magana da wani dan ƙasar Somalia na ce zan tafi ƙasarsu na auro mata, ya ce "Ƙila ta yarda ta aure ka, amma mu matammu ba a musu kishiya, don wallahi daya za ta iya neman ran dayar" wannan fa a matakin matan kenan, ya ce ko alama kar mutum ya yi sakacin ajiye su a gari guda, daga amaryar har uwargidan ba wace za a iya amince mata kowace a cikinsu za ta iya daukar mataki a kan dayar. Na san ko a ƙasarsu ba dan birni ba ne ƙila a ƙauye ake haka Allah ne masani amma matansu duna da kishi tunda matakin da za su iya dauka shi ne kisa.

    Anan Æ™asar mun sha ganin munanan matakai da mata ke dauka, wanda ya fi yawa shi ne zuwa wurin boka, yadda mazan ba za su iya komai ba sai  abin da suka ce suna so, sukan kashe kishiya, ko 'ya'yanta, ko su haukatar da ita ko 'ya'yanta, ko su talauta ta ko su hana 'ya'yanta ganin hantsi, ko su sa mijin ya juya mata baya, ko kuma ita ta ji ba ta Æ™aunarsa a yi ta dauki ba dadi a cikin gidan. Don me suke yin hakan? Wai kishi.

    Akwai wasu Æ™ananan abubuwa kuma kamar hada fada da matan kan yi tsakanin maigida da daya matar, ko tsakaninsa da 'ya'yanta, duka dai matakai ne da matan kan dauka. Namijin da kishi ya debo shi zai iya yi wa mace jina-jina da duk  abin da ya wawura a lokacin, ba bambanci tsakanin matattarar musulmi da wasunsu, ya danganta ne da irin mallakar kai da mai kishin yake yi.

    Na ga matattarar da mijin ya watsa wa matar guba a fuskarta duk ya ba ta mata wai yana kishi. Sai dai zancen kisa ga alama kowani bangare na yi, ba a jima ba aka yi shari'ar wata Hausa/Fulani anan Nigeria wai ta kashe maigidan a dalilin kishi, ke nan a ko'ina ana samu. Amma matakin da ya fi shahara a matattatarmu shi ne mijin zai yi batanci kuma zai yi saki, wata ƙila kuma rabuwa ta dindindin, ita kuma mace matakin da za ta dauka shi ne komawa gida ta ce ba za ta dawo ba har abada duk bikon da zai yi da ban haƙuri.

    Anan Zan Dakata Sai Mun HaÉ—u a Rubutu Na Gaba.

    **************************
    Daga:  Baban Manar AlÆ™asim
    **************************

    Wannan É—aya ne daga cikin rubuce-rubuce da ke cike da faÉ—akarwa da ilimantarwa, waÉ—anda ake samarwa daga Zauren Markazus Sunnah. Ku bibiye su a kafafensu na sada zumunta domin samun Æ™arin bayani. Amsoshi ba ta da haƙƙin mallakar waÉ—annan rubuce-rubuce, amma tana É—ora su ne da izinin Baban Manar AlÆ™asim.

    Kishi Rahama Ne Ko Azaba

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.