Ticker

6/recent/ticker-posts

KISHI RAHAMA NE KO AZABA // 33

6) GASA: Gasa na daya daga cikin manyan abubuwan dake baiyana kishi a wannan matattarar tamu ta malam Bahaushe, in ka duba tsakanin maza za ka tarar da shi wurin masu yin aiki tare. Sai dai kishin ya fi bayyana ne ƙarara a tsakanin mata don su ko ba tare suke ba za a gani. Yanzu ba ri mu sako tambaya: Shin gasa ke haifar da kishi a tsakanin ma'aurata ko masoya, ko kuma kishin ne ke haifar da gasar? A wasu lokutan mata kan maida hankulansu ne kan  abin da ya shafe su kawai. Daga lokacin da aka ce sun koma ƙarƙashin namiji guda to daganin kishi zai shiga, sai gasa ta biyo baya. A wannan nazarin kenan, wanda yake sabanin haka tabbas zai ba da wani nazarin daban.

Koda yake babu gardama in aka ce mata na kishi da junansu kishi na gasa kuwa ko ba sa tare ƙarƙashin miji guda, ma'ana haduwar gidan haya ce kawai kamar yadda ya gabata a karatun baya. Irin wannan kishi na gasa kan bayyana ko a tsakanin mace da uwar mijinta, a yi ta dauki ba dadi maigidan bai iya yin komai ba.

Akan sami wace za ta dauki kishi don ganin  abin da uwar mijinta ke yi, ko kuma ita uwar mijin ta dauki ƙahon zuƙa ta dora wa uwargida. In dai uwargida ta ga maigidanta yana son wani irin nau'in abinci da mamansa take dafawa, kuma yana yawan zuwa wurinta ya ci, wannan ƙalu bale ne a wurin matar, ya zama dole ta koyo irin wannan dahuwar don ta dawo da mijinta inda ya kamata a ya ci, tunda ya yi aure ai wannan aikin ya fita daga kan uwan-miji ya dawo kanta.

Ba yadda za a ce tana kallon  abin da uwarmijinta ke yi ta zuba ido zuciyarta na tafarfasa ita ba kishiyarta ba. In uwar-miji uwa ce, za ta zaunar da ita ta koya mata yadda za hada komai, ko ta ba yaronta shawarar ya turo matarsa ta koya mata? Amma in ya zamanto uwar-miji na kallon  abin da matarsa take masa ita ma tana kwaikwayo dan ta janyo shi kusa wannan kishi ne. Baban Manar ya warware wannan matsalar a littafinsa na UWAR MIJI. Gazawa ce babba ba ma a matattarar Hausa/Fulani ba har a duniya gaba daya uwar-miji ta koma kishi da matar da.

Maza kan dauki gasa tsakanin kiyoshi a matsayin abu mai kyau, don a ƙarshe mijin kan huta kuma ya sami  abin da yake so. In wani abu yake buƙata alla-alla dayar take yi ta ga kishiyarta kasa ko ta ce ba za ta yi ba ita ta dauka. Da wata za ta ce ba za ta yi girki ba ya cewa dayar ta yi nan take za ta daura tukunya har da gayya, tana yi tana jefa magana don dai ta baƙanta wa dayar "Mu ai ko kwana saba'in aka nema a wurinmu yi tsab za mu yi shi ... yo mu da muke so a bar mana gidan ma mu yi aikinmu mu kadai!" Ta san da wace take yi.

Mata kan yi fada idan wace ba ranarta ba ta wanke ban-daki ta yi shara ta zuba ruwa a butar maigida. Kamar matan da suke su hudu a gidan mijinsu in suna gida daya za ka taras kowa da butarta a dakin maigida. Wace take da girki butarta ce za ka samu shaƙe da ruwa. wace ba ranar girkinta ba in ta zuba ruwan to rigima take nema. Koda kuwa ta dauka cewa fage ne na gasa wace ba ta shirya ba to ta ja da baya. Na tuna lokacin da wata cikin mata hudu ta ce ba za ta yi girki ba a ranarta, nan take maigidan ya ba wa mai bi mata girkin.

Abinda ke faruwa shi ne in mace ba ta yi girki ba maigida ba zai kwana a dakinta ba, nan fa aka tsallake wace ta ƙi. Da girki ya zagayo ta ce ba za ta yi ba 6×6=12. Ta sami kusan mako biyu ke nan ba ta tare da maigidan ashe ta shiga wani hali. Maigidan na dawowa ta kulle ƙofa tana ciki a ƙarshe dai ba ta iya jurewa ba tunda ta taro yaƙin da ya fi ƙarfinta. Da a ce ita kadai ce ko don ta gasa maigidan za ta jure duk wata wahala.

Maza kan yi amfani da wannan damar wurin hada mata a gida daya, tsakani da Allah wannan fakewa ce da guzuma don a harbi karsana, ko a ina mace take mijinta zai iya bin ta ba sai suna gida guda ba. Ba na tsammanin za a hada mata da yawa a gida guda don a yi maganin kishi, a zahiri in ma ba kishin a lokacin za a samu. In mata na gidajensu ko wace daban ba ta san  abin da yake wakana a daya gidan ba da sauƙi, amma matuƙar idanunsu na kan juna to sai yadda hali ya yi.

Anan Zan Dakata Sai Mun Haɗu a Rubutu Na Gaba.

**************************
Daga:  Baban Manar Alƙasim
**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin rubuce-rubuce da ke cike da faɗakarwa da ilimantarwa, waɗanda ake samarwa daga Zauren Markazus Sunnah. Ku bibiye su a kafafensu na sada zumunta domin samun ƙarin bayani. Amsoshi ba ta da haƙƙin mallakar waɗannan rubuce-rubuce, amma tana ɗora su ne da izinin Baban Manar Alƙasim.

Kishi Rahama Ne Ko Azaba

Post a Comment

0 Comments