Layya Da Kuɗin Bashi

     𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Shin ya halatta mutum ya ci bashi dan yin layya?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    الحمد لله، سبحانك اللهم لا علم لنا إلا ما علمتنا إنك أنت العليم الحكيم.

    Layya ba Dole bace, Saboda ba'a ruwaito dalilai na Shari'a akan Wajabcinta ba, Masu cewa wajibice dalilansu raunane.

    Maj-mu'u fatawa bin baaz (18/36)

    Wadanda sukace: wajibice sun shardanta sai in kana da wadata

    Duba Hashiyatu Ibnu Abideen (9/452).

    Da Masu cewa dolece da Masu cewa sunnah ce, Ba wajibi bane karɓar bashi dan siyan Abun layya, domin ba dole bace.

    Anso Mutum ya nemi Bashin ya sayi Abun layya idan yana da tabbas ɗin zai iya biya, kamar Ma'aikaci sai ya karɓi bashin Abun layya kafin ya karɓi Albashinsa Aƙarshen wata. idan yasan yana da Taurin bashi ko bashi da halin biya, Abunda yafi masa kada yaci bashin.

    Domin za ka shagaltar da kanka cikin nauyin bashi akan abunda ba tilas ne ba.

    Shaikul Islam Ibnu taimiyyah rahimahullahu ya ce: Idan kana da Halin biyan bashi saika nemi bashi dan kayi layya, Wannan Abune mai kyau, Amma ba dolene ka aikata hakan ba.

    Maj-mu'u fatawa (26/305).

    Tare da cewa yana cikin masu cewa wajibi ce.

    Ala Ayyi halin dai idan kanada halin da za ka iya biyan bashi ya halatta ka nema dan kayi layya.

    WALLAHU A'ALAM.

    Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah, ta fahimtar magabatan kwarai.

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi.

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.