Ticker

LAYYA KO BIYAN BASHI?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Shin da yin layya da biyan bashi wanne yafi?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

الحمد لله.

Biyan Bashi shi ne yafi, kuma shi ne yake dole sama da yin layya, saboda dalilai Masu Yawa.

1- Biyan Bashi dolene, Layya kuma Sunnah ce Mai ƙarfi, ba'a gabatar da Sunnah akan wajibi, har a wajan waɗanda suke ganin layya wajibice, sunce biyan bashi shi ne abun gabatarwa akan layya, domin layya a wajan waɗanda Sukace dolece, tana Zama tilas ne akan mai iko, Mai bashi kuma ba Mai iko bane.

2- A cikin biyan bashi akwai kubuta daka nauyin dake kan mutum, wajan ayyana layya kuma shagalane da nauyin, babu shakka Sauke nauyi shi ne yafi sama da shagala dashi.

3- Bashi Haƙƙin bayine, Layyah haƙƙice ga Allah da Mawadaci, A wannan hali za'a gabatar da hakkin bayine

4- Cigaba da Zaman bashi akan mutum akwai haɗari babba, saboda tsoran kada sai ranar alƙiyama za'a biya da kyawawan ayyukan mutum.

Acikin haka akwai haɗari domin a wannan halin mutum yana cikin tsananin buƙatar kyakkyawan aiki koda ɗaya ne.

Da Wannan zai bayyana gareka cewa biyan bashi yafi sama da yin layya, saidai idan bashi yana da lokaci maitsawo, ta yanda wanda ake bin bashi yana da mafi rinjayen zaton zai iya biyan bashin a lokacin da aka deba masa, idan ya yi layya, ko ya ranci abunda zai iya biya koda a lokacin bai biyaba, Babu laifi akansa ya yanka layya gwar-gwadon Abunda Allah ya buda masa, zai samu lada da Sakamako Awajan Allah.

Kamar yanda bayani yazo acikin littafin Sharhin Mumti'i (8/455).

WALLAHU A'ALAM.

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah, ta fahimtar magabatan kwarai.

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments