Ticker

MAFITAR MATA 02

MAFITAR MATA 02

Mafi Yawan Matan '‘Yan Wuta Ne

Dalili Na 3

Rashin Yin Sallah Akan Lokacin Ta

Manzon ALLAH {s.a.w} Ya ce: Kada ku hana mata zuwa masallatai, amma ɗakunansu su sukafi alkhairi a garesu.

 Wannan hadisi yana nuni da halaccin zuwan mata masallaci, amma kuma suyi sallah a cikin ɗakunansu su kaɗai yafi falala agurin ALLAH sama da suje masallaci.

 To amma da yawa basa kiyaye yinta akan lokacinta a cikin gidajan nasu, sunaji ana kiran sallah amma baza su tashi suyi sallah akan lokacinta ba.

 Yinta akan lokacinta wajibi ne, wulaƙantata da ƙinyinta akan lokacinta yana daga cikin manyan zunubai.

 ALLAH TA'ALAH ya ce: Mene ne ya shigar daku wutar saƙar?

 Sai su kace: Bamu kasance daga masu yin sallah ba, bamu kasance muna ciyar da miskinai ba,

 Mun kasance muna ƙaryata ranar sakamako, har mutuwa ta zo mana.

[ Muddasir Ayata: 42-47]

 ALLAH TA'ALAH ya ce: Sai wasu jama'u suka maye bayansu, suka tozartar da sallah, suka biyewa sha'awe-sha'awe da sannu za su haɗu da azabar Gayyu.

[ Maryam Ayata: 59].

 ALLAH TA'ALAH ya ce: Azabar Wailu ta tabbata ga masu yin sallah waɗanda sune masu rafkanuwa ga barin yin sallarsu.

[Ma'un Ayata: 4]

 Manzon ALLAH {s.a.w} Ya ce: Abinda ke tsakanin bawa da shirka shi ne barin sallah.

[Muslim da Tirmizi].

 Manzon ALLAH {s.a.w} Ya ce: Duk wanda yabar sallah da ganganci, to alƙawarin ALLAH ya kuɓuta daga gareshi.

 Umar bin kattaɓ (R.A) Ya ce: Babu rabo a musulunci ga duk wanda yake wulaƙanta sallah.

 Ibrahim Al-Nakfiy (R.A) Ya ce: Duk wanda yabar sallah to ya kafirta.

 Ga ayoyi da hadisai nan barkatai da suke bayani akan hukuncin mai wasa da sallah, wanda baya yinta akan lokacinta.

 Mata kuji tsoron ALLAH bakwason yin sallah akan lokacinta, kuna zaune kuna kallon TV bazaku tashi kuyi sallah ba.

 Amare da ƙawayen amarya kuji tsoron ALLAH saboda anyi muku kwalliya a fuska sai kuƙi yin sallah akan lokacinta, wai saboda kada kwalliyarki ta goge, to da wutar jahannama za a ƙone wannan fuskar da kikaƙi wanketa ki bautawa wanda ya halicceki akan lokaci.

 Annabi {s.a.w} ya ce: Duk wanda yaji an kira sallah kuma yaƙi zuwa yayita akan lokacinta, alhali lafiyarsa ƙalau babu wata larura, to ko ya yi ALLAH bayaso.

 Don haka rashin kiyaye sallah akan lokacinta yana ɗaya daga cikin abinda yake jefe mutum cikin jahannama.

ALLAH ka bamu ikon aiki da abinda muka karanta.

ALLAH ka gafarta mana zunubanmu baki ɗayanmu Ameen.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments