Mafitar Mata 05- Mafi Yawan Mata '‘Yan Wuta Ne

    DALILI NA 6

    CAKUƊUWA DA MAZA

    Daga cikin abinda yake jawowa mata shiga wuta a ranar alkiyama shi ne cakuɗuwa da maza, domin su mata babbar fitina ce mai jawo fushin ALLAH.

    ALLAH TA'ALAH ya ce: Suna gaggawar ɓarna a doron ƙasa ALLAH baya son maɓarnata.

    [Ma'idah Ayata: 64]

    Manzon ALLAH {s.a.w} ya ce: Banbar wata fitina a bayana ba mafi cutarwa ga mazaje kamar mataye.

     Manzon ALLAH {s.a.w} ya ce:

    Duniya wani fage ne na ni'ima, ALLAH TA'ALAH ya zaunar daku ne a cikinta domin yaga yadda zakuyi, don haka kuji tsoron ALLAH, ku kiyayi mata.

     Domin farkon fitinar banu isra'il ta kasance ne daga mata.

    [Sahih Bukhari]

     Manzon ALLAH {s.a.w} Ya ce:

    Kada mace ta yi tafiya sai da muharraminta, kuma kada wani namiji ya shiga gidanta sai inda muharraminta a tare da ita.

    [Bukhari da Muslim]

    Muharraminta shi ne ɗan uwanta jini, kamar ya yayanta ko ƙaninta, mahaifinta ko wani dai daga danginta wanda aure ba zai shiga tsakaninsu ba.

     Amma ƙanin mijinta haramun ne ya zo ya zauna suyita hira da matar yayansa mutuƙar baligi ne, sai dai idan akwai mijinta a gurin.

     Mata suna cakuɗuwa da maza a cikin kasuwanni, basa kiyaye jikinsu daga haɗa jiki da mazan daba nasu ba.

     Mata na cakuɗuwa da maza a guraren biki musamman gurin da aka haɗa da kiɗa da waƙa ananma ana saɓawa ALLAH sosai, dama kuma kiɗa haɗe da waƙa haramun ne, ko da ta yabon ALLAH da Manzon ALLAH {s.a.w} ce, indai an saka kiɗa to ta haramta.

     Mata na cakuɗuwa da maza a cikin abin hawa kamar motar haya ko Keke Napep shima anan zaka ga yadda mata ke jingina da jikin namiji, basa iya kame kansu a cikin abin hawa, tunda larura tasa dole sai an cakuɗu a cikinsa, amma dai kowa sai yaji tsoron ALLAH gwargwadon iko.

     Mata na cakuɗuwa da maza a lokacin zaɓe na siyasa ko wani taro wanda bana addini ba, ko a makarantu ana cakuɗa, ko da kuwa a taron addini ne bai halatta mata su cakuɗa da maza ba, kowa ya zama ya ware da jikinsa guri daban.

    ALLAH ka bamu ikon kiyayewa, ka kuma bamu ikon aiki da abinda muka karanta.

    ALLAH ka gafarta mana zunubanmu baki ɗayanmu Ameen.

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

     

     

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.