Mahaifiyarta Ta Tsine Mata Ba Da Haƙƙi Ba

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu alaikum Malam ina da tambaya, wata ce take jinyar mahaifiyarta sai likita ya ba da doka, kuma idan aka karya wannan dokar zai haifar da wata matsala, amma ita mahaifiyar ba ta son bin dokan, idan kuma 'yarta ta sa ta bin dokar sai ta yi ta mata Allah ya isa har ma ta kai ga ta tsine mata, to dan Allah Malam ya za ta yi kuma ya hukuncin furucin da tai mata?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa'alaikumus Salamu. Allah ba ya kama rai sai da abin da ya zama laifi ne, ita kuma wannan yarinya ba laifi ta yi ba, tana ƙoƙarin ta ga mahaifiyar nan tata ta kiyaye dokar lafiya ne don ta sami lafiya su ci gaba da yin ingantacciyar rayuwa tare, ga shi kuma Allah Maɗaukakin Sarki ya ce:

    "KADA KU KASHE KAWUNANKU, LALLAI ALLAH YA KASANCE MAI JINƘAI NE A GARE KU". Suratun Nisá'i, aya ta 29.

    Wannan ya sa yarinyar ba ta son mahaifiyar nan tata ta yi sanadin rasa ranta ta hanyar saɓa wa dokar lafiya, saboda wannan dalili, wannan tsinuwa ba za ta kama yarinyar ba inshá Allah saboda manufar yarinyar ba son ta ɓata wa mahaifiyar rai take yi ba.

    Saboda haka ina ba ta shawara idan akwai waɗanda mahaifiyar tata take jin maganarsu, ko aminanta, ta sanar da su don su riƙa ba ta shawara a kan kiyaye dokokin maganin da aka gindaya mata, don ki sami sauƙin shawo kanta wajen kiyaye tsarin magungunan.

    Allah ne mafi sani.

    Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.

    Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/GcU1I5wjOB18K4PA6eURƘƘ

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.