Mahaifiyata Tace Zata Tsine Min Idan Ban Auri Wanda Take So Ba, Alhali Bana Sonsa. Shin Zan Iya Bijire Mata?

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Malam ina tambayane ina da wanda nakeso to sai wani ɗan gidan masu kuɗi yace yana sona nikuma nace bani sonsa saboda yana shaye shaye sai yabi tawajen mahaifiyata itakuma tace in ban aureshiba sai ta tsine mun malan idan nabijire mata naki aurenshi tsinuwan zata bini?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    الحمد لله.

    Uwa bata da hakkin zabarwa 'yarta mijin da 'yarta zata Aura, Saboda haka duk wata tsinuwa da uwa zataiwa 'yarta akan tabijire mata wajan auran ɗan shaye shaye mara tarbiyyah ko da baya shaye shaye amma bashi da addini ko kuma baida dabi'u, to dankin bijirewa mahaifiyarki akan kin aurensa tsinuwarta ba'abun da zatai miki kuma duk fushin dazatai dake akan hakan babu wani tasiri dazayi arayuwarki domin bijerewar dakikai addini Kikayi biyayyane ga abun da Allah da manzansa suke so, Manzan Allah sallallahu Alaihi wasallam kuma yabayyana mana cewa (Babu biyayya ga wani abun halitta kowaye a cikin saɓawa mahalicci,) Dan haka uwa ta tilastawa 'yarta auren wani fasiki ba hakkin ta bane, ko da ba fasiki bane amma bashi 'yar takesoba bashi ne zuciyarta tanustsu dashiba wannan saɓawa Allah da manzansane, Kuma babu wata tsinuwa dazataiwa 'yarta akan hakan tabi ta.

    Kuma shari'ar musulunci bata kawo dukiya amtsayin ma'aunin da mace zata zaɓi miji dashi ba, biyewa dukiya wajan zabar miji shike haifar da fitintunu dayawan rigima atsakanin ma'aurata domin mafi yawancinsu sukan wula kanta matanne, saboda gani suke saboda dukiyarsu aka sosu dan hakan sai abun da kika gani.

    Ita mace idan aka tilasta mata zama dawanda bai mata arantaba ko da ya mallaki duk duniyar nanne Bala'i zai zame mata, dan tsinuwa cikin bijirewa abun da saɓawa mahaliccine baya da wani tasiri akan mutum

    Abun da shari'a tai umarni shi ne lallaine waliyan yarinya ko ita kanta tatsaya ta nutsu tazabi ma'abocin Addini kuma mai dukiyar dazata iya rikesu na harkokin yau da kullum, saboda Fadin Annabi sallallahu Alaihi wasallam lokacin dayake baiwa fadimatu bintu ƙais Yardar Allah takara tabbaya a gare ta shawara lokacinda taje tana neman shawararsa dangane da mutane uku da sukazo neman aurenta, ya ce: amma Mu'awiyyah mutum ne talaƙa bashi da dukiya, bashi da abun da zai iya rike rayuwarsa data iyali, muslim 1480.

    Amma basharadi ne namiji ya zamto dan kasuwa mawadaci ba, abun da kawai ake bukata yakasance yanada wani aiki ko sana'a ko dukiyar dazata dauke dawainiyarsa tayau da kullum dakuma ta iyalinsa ci dasha, tufatarwa kulada lafiya karatu magani, ba tare dasuna tambaya ko roko ba, wannan shi ne ma'abocin dukiyar da Annabi yake nufi, wanda baida abun da zai dauke wannan shi ne ake cewa wanda baida dukiya, ba irin tunanin dayake zuwa kwakwalen muba idan ance mutum mai dukiya.

    Dan haka idan aka samu ga wani saurayi mai dukiya amma fasikine baidamu da sallah ba baisan darajar matarsa da mutuncintaba ko kimar auren ba, agefe daya kuma gawani mai addini amma baikai wancan dukiya ba indai zai iya rike dawainiyar aure wajibi ne dole ashari'a azabi mai addini mara dukiya akyale mawadaci mai arziki

    Annabi sallallahu Alaihi wasallam yacewa Fadimatu bintu ƙais amma kin ga abu jaham baya dauke sandarsa daka kafadar mata, ma'ana mai yawan dukan matane, dan haka mai shaye shaye ma zai iya dukan idan ya duri barasarsa sannan ba zaisan mutunciki ba tarbiyyar 'ya'yanki zata koma hannun marasa mutunci irinsa.

    Dan haka bin mahaifiyarki akan saikin auri miji wanda yake shaye shaye, ki kyale wanda baya shaye shaye kuma shi ne kikeso wannan baya cikin hakkin biyayyar iyaye dake kanki dan haka binta akan wannan laifine maigirma, saɓa mata akai kuma bin umarnin Alllah ne damanzansa.

    Idan Allah da manzansa sukayi umarni to umarni kowa wurgi ake dashi abi nasu, idan kuwa aka dauki nawani akayi wurgi dana Allah da manzansa to ajira fitina da bala'i da musifa darashin kwanciyar hankali darashin albarka arayuwar duniya data lahira Allah yatsaremu.

    Tsinuwar mahaifiyarki intakai cikin kumfar kogi akan kin bijirewa wannan umarnin nata narantse da Allah baza ta yi wani tasiri akanki ba, kuma Allah ba zai fushi dakeba zakiga Albarka arayuwarki, Allah ma ba zai karbeta ba danba hakkin tabane.

    Muna rokon Allah maɗaukakin sarki mai iko akan komai yasaukaka miki al'amuranki yabaki ikon amincewa da zabar miji nakwarai mutumin kirki akan mutumin banza wanda dukiyarsa ta rudi mahaifiyarki, Ya azurtaki damiji nagari, da zurriya mai albarka domin shi mai ikone akan komai.

    WALLAHU A'ALAM

    Zauren Tambaya da Amsa Abisa fahimtar magabata Nakwarai. Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.