Matsalar Rashin Jin Daɗin Saduwa A tsakanin Ma'aurata

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalumu alaikum, Allah ya karawa malam kaifin basira, Malam ina so ka taimaka mun ina neman shawara da mafita a garaka, jiya na cika wata ɗaya da aurena amma wallahi tunda mukayi aure banajin daɗin saduwa da matana itama jiya take fadamun cewa batajin daɗin saduwa dani, tana yarda danine dan batason saɓamun amma wallahi tana sona kuma ba ta tunanin zata iya rabuwa dani, kuma nima haka nakeji wallahi nafijin daɗin na rinka kallonta da ace ina saduwa da ita, dan haka nace Bari na kawo kukana ko zan samu maslaha, na gode.

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    To Shawarata ta farko ita ce ku ziyarci babban asibiti domin ku yiwa likitan bangaren haihuwa (Ganaecologist) bayanin abinda ke damunku. Ina zaton in Shã Allahu za ku samu shawarwari daga garesu.

    Bayan haka kuma daga cikin abubuwan da za ku kula dasu akwai :

    1. Gabatar da wasanni sosai kafin saduwa. Sannan da nuna kulawa da Ƙauna atsakanin juna (shima yana Ƙara nishadi atsakanin ma'aurata).

    Kada ya zamto baka da lokacin da za ka janyo matarka jikinka kuyi hira ko tattaunawa da juna ko ka sumbaceta atsawon wuni baki ɗaya, sai dai in saduwa za ka yi da ita.

    2. Abu na biyu idan tana da matsalar ciwon sanyi yana da kyau ku maganceshi domin samun nishadi atsakaninku.

    3. Hakanan shafar Aljanu , musamman jinnul ashiƙ (namijin dare) idan yana tare da mace yakan ɗauke mata sha'awa, yakan hanata jin daɗin jima'i kuma ya sanya mijinta ya kasa samun gamsuwa da ita.

    Manyan alamominsa sun haɗa da ciwon kai, faduwar gaba, mafarkin saduwa, ko firgita, ko kasala wajen yin ibada, da sauransu.

    WALLAHU A'ALAM

    Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Za ku iya bi ta Links ɗin mu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/Cnf26Ƙ8MPƙz9yUYU1nxƙRƙ

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.