MATSALAR RASHIN RUWAN NI'IMA A GABAN MACE

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu alaikum warahmatullah, Allah ya ƙarawa Malam lfy, Malam wata ƙawata ke cikin damuwa sai take gayamin nace to in Allah ya yarda zan tannayar mata  abin da yafi da cewa da matsala ta, Tace wai da tana waje saurayinta yana ƙaunarta sosai yanzun sun yi aure sai take ganin uwa baya wani kulawa da ita yanda ya kamata kuma uwa sonta ya ragu agareshi, amma tace ita  abin da tafi zargi yake sa hakan uwa ba ta masa  abin da yakeso ne na mu'amala ta aure shi yanaso ko yaya ya tabata yaƙa tachanza ma'ana har yakai da tun yana ɓoye mata ya fara cewa me ya sa baya ganin ruwa daga gabanta shi ya ce yana buƙatar hakan ya gani sosai, ita kuma babu wannan abunda yakeso din sannan kuma ya ce me ya sa daya fara tabata batayin uwa zata fita hayyacita, hakan ya janyo da ya biya buƙatarsa mintuma 5 shikenan zai rabu da ita, shi ne take cewa tasan hakan zai jayo mata wani ƙin kulawa da ita ko kuma kullum cikin samun matsala, malam dan Allah wace shawara za ka ba ta a game da wannan ta damu sosai, amma tana dauke da ciki me yakamata za ta yi?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa'alaikumusslam Warhmatullah.

    Gaskiya ya kamata ta sani cewa ba duk namiji ne yake bawa mace kulawa kamar yadda yake ba ta a waje ba ma'ana kafin aure.

    Kuma dayawa yanzu auren sha'awa akeyi bana tsantsar so da ƙaunaba, to kagayan yadda soyayya zata dore a gidan aure ai sai dai haƙuri.

    Sannnnan rashin ni'ama da take fama dashi shi ne yakamata ta nemi magani, amma tunda tana da ciki ba komai zata shaba sai dai ta yi haƙuri idan ta haihu sai ta gyara jikinta.

    Sanan wanan rashin ni'ima bazai zama hujjaba har ya daina ba ta kulawa, kawai dai halinsa haka yake, domin akwai maza da daga sanda suka san matarsu a ya mace zaki ga sun rage kulata ba kamar daba, haka halittarasu take basu da ƙarfin sha'awwa, irinsu kuwa sai dai a mallakesu.

    Sanan  abin da yasa baya ganin tana nuna jin daɗi har yaga ta fita hayyacinta to wannan laifinsa ne domin da ya iya sarrrafa mace ta yaga yadda zata canja ta fita hayyacinta, sabida haka sai ya koyi yadda ake sarrafa mace.

    Tayi haƙuri ta cigaba da bashi kulawa sosai don shima ya tausaya mata ya kula da ita...

    Allah ta'ala yasa mudace

    Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah, ta fahimtar magabatan kwarai.

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/J1hm5Tw12uYBƙfaiPwf28l

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi.

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

     

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.