𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Malam Wacce mijinta yake saurin inzali kafin buƙatarta ta biya mai yakamata suyi don maganin matsalar?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Gaskiya wannan ba ƙaramar matsala ba ce domin kuwa ita take sa rashin zaman lafiya a tsakani yawanci ma'aurata kuma akwai cutarwa mai yawa kususan ga matar, domin ita mace akwai wani ruwa da ke fesowa a gabanta kafin ta yi inzali shi kuma wannan ruwan asit ne domin zafi ne da shi idan ta yi inzali wannan ruwan maniyi shin e yake sanyaya shi to idan har ba tai inzali ba wannan ruwan zai sabbaba mata ciwon mara da tsatstsagewarta da matsala a farjinta, kuma zai sa ta tsani miji. don haka Manzon Allah ﷺ ya ce:- "Idan ɗayanku ya sadu da matarsa to kada ya tashi har sai ta biya buƙatarta kamar yadda yake so ya biya buƙatar sa".
Abin da akafi so ga kowanne miji da mata kowanne ya yi iya yinsa don ya gamsar da ɗan'uwansa, ba wai kowa ya dinga ƙoƙarin biyawa kansa buƙataba wanna shi ne abin da yake haifar da matsalar.
Mafita shi ne, a biyo hanyoyi da muka yi bayani a baya kafin jima'i wato ɗan saƙo kamar yadda Manzon Allah ﷺ ya yi bayani.
(abu na biyu) kasancewar sha'awar mace tana kaiwa minti goma 10 ta namiji minti biyar 5 to sai ya sami kanwa ya sa a bakinsa ya dinga tsotsa kamar alawa a lokacin jima'in wannan zai sa sha'awarsa shima takai har minti goman 10 ta inda zasu yi dai dai idan aka yi haka za'a sami mafita.
WALLAHU A'ALAM
Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah, ta fahimtar magabatan kwarai.
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/Cnf26Ƙ8MPƙz9yUYU1nxƙRƙ
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi.
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.