Matsayin auren da miji kan tafi ya bar matarsa na tsawon shekaru!

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu Alaikum, tambayata ita ce: Yaya hukuncin Auren da miji sai ya yi tafiya tsawon shekara 4 ba shi nan, idan ya dawo yanayin wata 1 sai ya koma har Sai ya sake yin wasu shekaru 4 ko kasa da haka ko fiye da haka? Ita kuma matar nan ta gaji da wannan yanayi, shi ne ta ce ya sake ta, gashi duk tsawon shekarun da zai yi babu wani ɗan'uwansa ko mahaifiyarsa da za ta bibiye su ita da yaranta guda 4, ko wani taimako su yi mata, kuma Abin da mijin nan yake ba ta ba ya isansu, amma dangin mijin suna zaginta wai ta mallake shi komai yana yi mata, Ina fatan malam zai fahimci tambayata, Allah ya kara hasken ilimi.

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa'alaikumus salam. 'yar uwa auren da miji kan yi tafiya na tsawon shekaru ba tare da sun haɗu da matarsa ba ingantacce ne, hakan bai ɓata auren ba. Amma idan ya kasance matar tana cutuwa da wannan hali da mijin nata ke barinta a ciki, to a nan tana da zaɓin kai ƙara zuwa ga alƙali domin ya lizimta wa mijin dawowa, idan kuwa alƙali ya lizimta masa dawowa amma ya ƙi dawowa, to a nan alƙali yana da damar ya saki matar ko ya ɓata auren.

    Daidai ne mijin yana da uzuri na rashin dawowa ko ba shi da uzuri, duka hukuncin ɗaya ne, bambancin shi ne idan ya kasance yana da uzuri to ba shi da laifi a kan ƙin dawowar da ya yi, idan kuwa ba shi da wani uzuri, to yana samun zunubi da ƙin dawowar da ya yi, saboda hakan yana cutar da ita.

    Amma idan ita matar ta yarda da hakan, kuma tana cikin yanayin da akwai aminci, ba ta rasa komai na rayuwa ba, to babu laifi idan ta ci gaba da zama a haka. Wasu malaman suna ganin tsawon lokacin da mutum ke da damar tafiya ya bar matarsa ba tare da ta gan shi ba shi ne wata huɗu, wasu kuma suna ganin wata shida ne, wannan na ƙarshen shi ne abin da Sayyiduna Umar Allah ya ƙara masa yarda ya yi hukunci da shi.

    Don haka, wannan aure na wannan mata da mijinta kan tafi ya bar ta na tsawon shekaru huɗu aure ne ingantacce, amma idan matar ba ta gamsu da hakan ba, to haƙƙinta ne ta nemi ya dawo, idan kuma ta nema ya ƙi dawowa tana da damar ɗaukaka ƙara zuwa ga alƙali.

    Duba Kasshaful Ƙiná'i Anil Iƙná'i (5/193) don ƙarin bayani, ko Almausú'atul Fiƙhiyya Alkuwaitiyya (29/63).

    Allah Ta'ala ne mafi sanin daidai.

    Jamilu Ibrahim, Zaria.

    Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/BXjuXb1WxX99NV3OsXPnLV

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑��𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.