Matsayin Kiran Sallah Da Iƙama Ga Mata

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum, malam ina da tambaya, shin mace idan za ta tsayar da sallah kiran sallah za ta fara yi ko kuma ikama za ta yi, sannan ta yi kabbara ta yi addu'ar buɗe sallah?

na gode a huta lafiya.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus salám, Ibn Ƙudama ya ce: "Ba a wajabta wa mata yin iƙama da kiran sallah ba, wannan ita ce fahimtar Ibn Umar da Anas da Sa'idu binul Musayyib, da Hassan da Ibn Seereen, da Annakha'iy, da Atthauriy, da Malik, da Abut Thaur, da As'háburra'ayi. Ban san wani saɓani game da hakan ba".

Almugniy (1/302)

Da aka tambayi Shaikh Abdul'aziz bn Abdullahi bn Baaz a kan cewa shin ya halasta mace ta yi kiran sallah da iƙama idan za ta yi sallah ko kuwa?

Sai Shaikh ya ba da amsa da cewa: "Ba a shar'anta wa mace yin kiran sallah da iƙama a sallarta ba, wannan al'amari ne na maza kaɗai, amma su mata ba a shar'anta masu yin kiran sallah da yin iƙama ba, za su yi sallarsu ce kawai ba tare da kiran sallah da iƙama ba, sai dai wajibi ne a kansu su kiyaye lokacin sallah, da yin khushu'i, da daina yin wasanni a cikin sallah kamar yadda yake a kan namiji...".

Majmu'u Fataawá Ibn Baaz (10/356).

Wannan sai ya nuna cewa ba a lizimtawa mace kiran sallah ba, haka nan ma ba a lizimta mata yin iƙama ba idan za ta yi sallah, kawai mace za ta ɗaura ninyar sallar da ta nufaci yi ne a zuciyarta, sai ta yi kabbarar harama ba tare da iƙama ba kamar yadda bayanin waɗancan malamai ya gabata. Haka nan ko da jam'i ne matan za su yi wa kansu, shi ma ba a shar'anta masu kiran sallah da iƙama ba kamar yadda Fataawál Lajnatid Dá'ima suka bayyana cewa:

"Ba a sunnanta wa mata yin iƙama a sallarsu ba, daidai ne sallar sun yi ta daban-daban ne, ko kuma ɗayansu ce ta yi masu sallar, kamar yadda ba a shar'anta masu yin kiran sallah ba".

Dubi Fataawal Lajnatid Dá'ima (6/87).

Allah S.W.T ne mafi sani.

Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.

Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/CƘ9TMXMrWDx1y7sYye2znU

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam


Post a Comment

0 Comments