Mene ne Zihari?

Zihari wata ɗabi’ace da Larabawa keyi tun zamanin Jahiliyyarsu ta farko, don su cutar da matansu.

 Da zarar ɗayansu ya gaji da mace, sai ya dube ta ya ce:

 Kin haramta a gareni kamar yadda gadon bayan mahaifiyata ya haramta gare ni.

 Ko kuma yace mata: Kin haramta a gareni kamar yadda `’yar uwata ta haramta gareni.

 Wannan muguwar al’ada na ɗaya daga cikin al’adun jahiliyyar Larabawa da suka yaɗu a cikin wannan al’umma a yanzu.

 Shari’ah ta haramta wannan al’ada da duk wani abu mai kama da ita, da ke cutar da mata.

ALLAH TA'ALAH ya ce:

Waɗanda keyin Zihari daga cikinsu game da matansu, su matan-nan ba uwayensu ba ne, uwayensu kam sune waɗanda suka haife su.

 Suna faɗar abin ƙyama na magana da ƙarya, kuma haƙiƙa ALLAH mai yafewa ne, mai gafara

[ Mujadalilah Ayata: 27]

 Hukuncin duk wanda ya aikata irin wannan laifi a matsayin kaffara, a shari’ar musulunci, shi ne irin kaffarar wanda ya kashe wani a kan kuskure, ko ya sadu da matarsa a cikin watan azumi da rana.

 Kuma haramun ne ya kusanci matar sai bayan ya yi kaffara.

 ALLAH TA'ALAH ya ce:

Waɗanda keyin Zihari game da matansu, sannan su koma wa abinda suka faɗa, to akwai `’yanta baiwa a gabanin su shafi juna.

 Wannan anayi maku wa’azi da shi, Kuma ALLAH mai ƙididdigewa ne ga abinda kuke aikatawa.

 To, wanda bai samu abinda zai `’yanta baiwa ba, sai ya yi azumin wata biyu jere a kafin su shafi juna,

 Sannan wanda bai sami ikon yi ba, to, sai ya ciyar da miskinai sittin.

 Wannan domin kuyi imani da ALLAH da Manzonsa, Kuma waɗannan hukunce-hukunce iyakokin ALLAH ne, Kuma kafirai suna da azaba mai raɗaɗi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam.

Post a Comment

0 Comments