Ticker

Mijina Yana Zagina Ni ma Ina Ramawa.

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum. Malam miji ne baya kyautatawa matarsa har ma wani lokaci ya zage ta, ita kuma sai ta rama. To meye hukunci wannan auren?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

wa alaikissalam. dan ya zageki bai kamata ki ramaba, kamata ya yi kiyi masa nasiha idan nasihar zata kwanto wata fitinar saiki nemi na gaba dashi ya yi masa Faɗa, amma bai kyautu mace ta dinga zagin mijinta dan ya zageta ba, Zagin miji ko cutar dashi da harshe, wannan yana daga cikin manyan laifuka a Musulunci (wato Kaba'ira).

Manzon Allah ﷺ ya lissafa matan da suke yin haka a cikin Manyan 'yan wuta. (ya Allah ka

tsaremu).

Manzon Allah ﷺ ya ce: Masu zagegeniya guda biyu toh zunubin yana komawa kan wanda yafarayi. Amma kuma karamci shi ne kada ki rama idan aka zageki. Musamman tsakanin Miji da Mata idan mijin ya zageki toh kada kirama wannan shi ne karamci domin su Mutanen kirki basa yin zagi kamar yadda Annabi ﷺ yafaɗa. Toh kuma idan aka zagesu basa ramawa domin Allah ta'ala shi ne da kansa Yace kuyi haƙuri domin yin haƙurin shi ne alheri ga masu haƙuri. Amma lefin wanda yarama zagi bekai lefin wanda yafara yin zaginba. Amma kuma lada da falalar wanda aka zageshi ya yi haƙuri be ramaba toh ba a kwatanta darajar me haƙurin akan wanda yafara yin zagin.

Imamul Bukhari kansa ya buɗe babi makamancin haka a cikin littafinsa Al-adabul mufrad.

 Allah na masani

Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/GcU1I5wjOB18K4PA6eURƘƘ

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments