Ticker

6/recent/ticker-posts

Musan Hukunce-Hukuncen Fiƙhu 24 - Hukuncin Susa Ga Mai Alwala / Sallah

Susa anan ana nufin mutum ya sosai gabansa alhali yana da alwala macece ko namiji.

 Idan mutum ya sosa gabansa bada niyyar jin daɗi ba, kawai saboda ƙaiƙaiyi alhalin yana da alwala, sai kuma yaji daɗi bayan ya sosa ɗin, to alwalarsa ta karye.

 Idan mutum ya sosa gabansa alhali yana da alwala da niyyar jin daɗi sai kuma baiji daɗin ba, to shima alwalarsa ta karye saboda ALLAH yana duba ne izuwa niyya.

 Idan mutum ya sosa gabansa bada niyyar jin daɗi ba, sai kuma baiji daɗin ba, to alwalarsa tana nan.

 Haka zalika idan a cikin sallah ne mai sallah ya sosai gabansa bada niyyar jin daɗi ba sai kuma yaji daɗi to sallarsa ta ɓaci, kuma sai ya sake alwala.

 Idan mai sallah ya sosa gabansa bada niyyar jin daɗiba kuma baiji daɗinba, sallarsa tana nan, amma dai ba'aso ya tsawaita susar.

 Wannan hukuncin yana kan mace ko namiji, babu banbanci a cikin hukuncin mata ko maza.

ALLAH ka bamu ikon aiki da  abin da muka karanta.

ALLAH ka gafarta mana zunubanmu baki ɗayanmu Ameen.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments