Musan Hukunce-Hukunecn Fiƙhu 25 - Game Da Bin Liman Sallah Daga Gida Ko Wani Guri

    Duk wanda yabi liman sallah daga cikin gida ko daga cikin rumfarsa ta kasuwa bashi da sallah, ko mace ko namiji.

     Gwarama ka yi sallarka kai kaɗai bakabi liman ba, amma mutuƙar kasan hukuncin hakan kuma kabi liman daga gida, to baka da sallah, amma ga wanda bai sani ba, babu komai a kansa, amma daga lokacin daya sani to hukuncin yahau kansa.

     Haka kuma duk wanda yabi liman sallah daga harabar masallaci alhali cikin masallacin bai cikaba, shima bashida sallah, kamar yadda wasu keyi a sallar juma'a ko a sallar asubah, sai suƙi haɗa sahu da mutane su koma can gefe su saka abin sallarsu subi liman daga can nesa, duk wanda ya yi haka baida sallah.

     Duk wanda ya shiga cikin masallaci ya koma gefe ya ƙirƙiri nasa sahun, alhalin sahun dake gabansa bai gama cika ba, to shima wannan bashida sallah.

     Hadisi ya tabbata daga Manzon ALLAH {s.a.w} wani tsoho ya zo gurin Annabin ALLAH {s.a.w} yace ya Rasulillah ni na kasance makaho kuma banida ɗan jagora, kuma hanyata batada kyau shin zan iya sallah ta a gida?

     Sai Manzon ALLAH {s.a.w} yace masa, eh zaka iyayin sallarka a gida, bayan tsohon ya juya ya tafi, sai Manzon ALLAH {s.a.w} ya kirawo shi ya ce:

     Shin kana jiyo kiran sallah daga inda kake? Tsohon yace eh, ina jiyowa,

     Sai Manzon ALLAH {s.a.w} ya ce: Kazo masallaci idan kaji kiran sallah.

     Wannan hadisin yana mana nuni da wajabcin yin sallah a jam'i a cikin masallaci, sannan kuma tunda ba'ayiwa tsoho kuma makaho wanda baida ɗan jagora rangwame ba, to babu wanda za'ayiwa rangwame.

     Sannan kuma hukuncin bai ware iya maza ba, har mata, domin wasu matan suna bin liman sallah daga cikin gida, wacce take wannan itama batada sallah, daga lokacin da kika san wannan hukunci saiki fara kiyayewa,

     Dama su mata ba a wajabta musu zuwa masallaci ba, an sauƙaƙa musu yin sallarsu a cikin gidajensu, kuma ko sallar juma'a ce bata zama wajibi a kansu sai sunje masallaci ba, su zauna a cikin gidajensu suyi sallar azahar ya wadatar musu.

    ALLAH ka bamu ikon aiki da abinda muka karanta.

    ALLAH ka gafarta mana zunubanmu baki ɗayanmu Ameen.

    Duk mai neman ƙarin bayani ya yi mana magana ta private.

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

     

     

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.