Mutum ne ya yi wa matarsa zihari, a maimakon ya yi kaffara sai kawai ya sake ta, ya sake wani auren. Ya matsayin wannan sakin da matsayin auren?.

TAMBAYA:

Mutum ne ya yi wa matarsa zihari, a maimakon ya yi kaffara sai kawai ya sake ta, ya sake wani auren.

Ya matsayin wannan sakin da matsayin auren?.

AMSA:

Auransa na biyun ya inganta saboda basu da alaƙa da juna.

Wasu Malaman sun tafi akan cewa mutuƙar saki uku ne, to wancan ziharin ya warware,

 Amma idan saki ɗaya ne kuma ya yi kome, to bai halatta ya taɓa ta ba, har sai ya yi kaffarar ziharin, kamar yadda Ibnu Khudamah ya faɗa a cikin Al-Mugni.

 Saboda haka kaffarar zihari ita ce '‘yan baiwa ko mutum ya yi azumin wata biyu a jere babu hutu, wato azumin kwana sittin, ko kuma ya ciyar da mutum sittin mabuƙata.

ALLAH shi ne mafi sani.

ALLAH ka gafarta mana zunubanmu baki ɗayanmu Ameen.

Duk mai neman ƙarin bayani ya yi mana magana ta private.

 ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

 

 

Post a Comment

0 Comments