Ticker

    Loading......

Na Yi Zina Da Mijin Makobciyata, Shin Yaya Zanyi In Tuba?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum Malam muna a gidan haya ne, mu biyu ne, ni mijina ya yi tafia tsawon shekara ɗaya to malam sai mijin matar da muke tare, matarsa bata nan sai ya shigo dakina ya nemeni ahaka muka aikata fasikanci. na ji bana iya jurewa shi ne na sanar da mijina amma ban faɗa mai mun yi zina ba. Nace mai ya nemeni dai amma naƙi amincewa, to ya kira mijina ya nema afuwa kuma yace kar matarsa taji. Malam na tuba nayi astagafirillahi to amma na kasa nutsuwa. Malam mene ne hukunchin mu?. Bissalam.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

Allah Maɗaukakin Sarki, mai yawan gafara ne mai jin Ƙai. Amma idan har mutum ya aikata babban laifi kamar Zina, cewarsa ASTAGHFIRULLAH Kaɗai ba zai wadatar dashi ba. Har sai mutum ya tuba zuwa ga mahaliccinsa.

Kuma tuba daga manyan laifuka irin su zina, akwai wasu sharuda da suka wajabta mutum ya kula dasu kafin tuban nasa ta zama cikakkiyar tuba irin wacce Allah yake nufi.

Ga sharudan kamar haka:

1. Wajibi ne kiyi nadama bisa miyagun laifukanki na baya. Ki dubi girman Ubangijinki Allah wanda zaki tsaya agaban zatinsa aranar tsaiwa (wato Alƙiyamah) kuma zaki amsa tambayoyi game da kowanne mummunan aikin da kika aikata.

2. Sannan ki ɗaukar ma kanki alkawari tsakaninki da Allah cewa har abada ba zaki sake komawa cikin wannan laifin ba.

3. Ki kaurace wa duk wata hanya ko dalilin da zai iya kaiki zuwa ga sake afkawa cikin irin wannan kuskuren. Misali kamar cigaba da yin chatting da wannan makobcin naku, ko tura masa text da sauransu.

Bashi da haƙƙin samun gaisuwa daga gareki. Don haka ki kaurace wa yin kowanne irin zance dashi, komai kankantarsa.

Nan gaba idan mijinki zai yi tafiya, ku rika tafiya tare dashi, ko kuma ya rika dawowa bayan wata guda ko watanni biyu. Amma bai kamata ya barki a gidan haya, shi kuma yaje ya zauna awani garin har tsawon shekara guda baku tare ba.

Idan kina da wasu Ƙawayen da kika tabbatar suna aikata irin wannan laifin, to ki kaurace musu ki dena shiga cikinsu ko yin chatting dasu.

Idan kina shiga shafukan batsa ko facebook groups na batsa, ko Whatsapp na batsa, to kiji tsoron Allah ki fita ki dena shiga.

Daga karshe kuma ki yawaita istighfari da ayyukan alkhairi waɗanda za su goge miki wannan mummunan laifin da kika aikata abaya.

WALLAHU A'ALAM.

Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/Cnf26Ƙ8MPƙz9yUYU1nxƙRƙ

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam


Post a Comment

0 Comments