Ticker

Nazari A Kan Itaciyar Kuka A Bahaushiyar Al’ada

 Kundin bincike da aka gabatar a Sashen Koyar Da Harsuna Da Al’adu, Tsangayar Fasaha Da Al’adu, Jami’ar Tarayya Gusau, don samun shaidar kammala digiri na ɗaya (BA.HAUSA), 2021.

Nazari A Kan Itaciyar Kuka A Bahaushiyar Al’ada

SADAM YUSUF

SADAUKARWA

Na sadaukar da wannan aiki mai taken “Nazari a Kan itaciyar Kuka a Bahaushiyar Al’ada” ga Mahaifina, marigayi Alhaji Yusuf Muhammad da Mahaifiyata, Hajiya Sa’adatu Sa’adu Zurmi, waɗanda su ka haife ni, sannan su ka ba ni tarbiya da cikakkiyar kulawa domin ganin na zama mutumin ƙwarai dangane da harkokin rayuwata a kodayaushe.

Haka kuma, wannan aiki sadaukarwa ne ga ɗan uwan mahaifina Alhaji Isiaka Muhammad Zurmi, watau wanda ya riƙe ni, kuma riƙo na amana sannan ya taimake ni wajen ganin cigaban karatuna da ma cigaban rayuwata baki ɗaya, tare da sauran iyayena da ƴan’uwana da kuma abokaina.

Har ila yau, na sadaukar da wannan aiki ga dukkan malamaina na makarantar firamare da sakandare da kuma jami’a.

GODIYA

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah maɗaukakin sarki mai kowa mai komai mai rahama mai jin ƙai zuwa ga bayinsa. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad (S.A.W.) da sahabbansa da zuri’arsa da dukkan waɗanda su ka bi shi har zuwa ranar sakamako.

Bayan haka, ina miƙa godiyata da jinjina zuwa ga mahaifina marigayi Alhaji Yusuf Muhammad, bisa irin jajircewar da ya yi na ganin cewa na samu ilimin addini da kuma na zamani a rayuwata. Kuma ina ƙara gode ma sa a kan irin addu’o’in da yakan yi mani dare da rana a lokacin rayuwarsa. Ina mai addu’ar Allah (SWT) Ya jiƙan sa da rahama, kuma ya gafarta masa, sannan ya saka masa da mafificiyar aljanna (maɗaukakiya), amin. Haka kuma, ina mai miƙa godiya da jinjina zuwa ga mahaifiyata dangane da irin namijin ƙoƙarin da takan nuna a kaina na ganin cigaban rayuwata har zuwa ranar da rai zai yi halinsa.

Haka kuma, ina miƙa godiya da jinjina ga Malamina, wanda kuma shi ne ya duba wannan aiki nawa, watau Dr. Adamu Rabi’u Bakura, bisa jajircewa da ƙoƙarin ganin ya ɗora ni a kan hanya don samun nasarar kammaluwar wannan aiki nawa. Godiya ta musamman ga Dakta , Allah Ya biya shi kuma Ya saka masa da Aljanna a ranar gobe ƙiyama, amin.

Bugu da ƙari, ina miƙa godiya ta musamman ga Malamaina waɗanda su ka yi mini riƙo na amana da mutuntawa tare da ba ni shawarwari a kan harkokin karatuna domin ganin na samu nasara. Waɗannan malamai sun haɗa da: Farfesa A.M. Bunza, Farfesa M. Tsoho Yakawada, Farfesa Aliyu Musa, Farfesa Balarabe A., Farfesa M. L. Amin, Dr. Adamu Malumfashi, Dr. Tahir, Dr. Nazir I. Abbas, Dr. Musa Fadama, Malam Isa S. Fada, Malam Musa, Malam Aliyu Rabi’u Ɗangulbi, Malama Halima Kurawa, Malama Bilkisu, Malam Bashir Abdullahi, Malam Abu-Ubaida Sani, Malam M. Arabi da sauransu. Ina roƙon Allah ya saka masu da mafificin alkhairi, amin.

Har ila yau, ina miƙa godiyata ta musamman zuwa ga yayyena da ƙannena da kuma abokaina, bisa ga irin gudummuwar da sukan ba ni da kuma addu’o’in da sukan yi mani, kamar su; yaya Shehu, yaya Shamsu (aye), yaya Buhari, yaya Abdullahi (namama), da anty zainab (abu), anty Nafisa. anty Farida, anty Rabi (ayina), anty Turai, anty Zulaiha (baby), anty Balki, anty Uwani, da Mustapha Ishaq, Uwaisu, Mahmud, Sufiyanu, Abubakar, Suleman (Lorenzo), Zulaiha, Fati, Maryam, Safiya, Aisha, Umma da ma waɗanda ban samu damar ambaton sunayensu ba, kuma da fatan za su yi haƙuri da ni.

Sannan kuma, ina miƙa godiya zuwa ga abokan karatuna kamar su; Abbas Muhammad (gidan dawa), Mahadi Al-mustapha (yaya I’g), Abudulrashi Bala, Abdulrashid Isma’il, Yusuf Muhammad Kwalli, Ibrahim Garba, Makiyu Balarabe, Bashiru Lauwali, Abdulrahaman Tukur, Kabiru Zuru, Amir Tijjani, Husaini Yari Morai, Jamilu Officer, Abdulmalik Mai Biredi, Saudatu Dalhatu, Binta Gambo, Rabi S. Zamfara, Asiya Suleman, da sauransu. Allah ya saka masu da alkhairi kuma Allah ya albarkaci karatunmu, amin.

 

TSAKURE

Nazarin itatuwa da tsirrai na ƙasar Hausa ba sabon abu ba ne a fagen ilimi.Don haka a yayin gudanar da wannan bincike an duba littafai, muƙalu tare da yin hira da wasu masana don ganin wannan bincike ya inganta. Wannan bincike mai taken “Nazari a Kan Itaciyar Kuka a bahaushiyar Al’ada” ya yi koƙarin bayyana ma’anar magani, maganin gargajiya da kuma ma’anar bahaushiya. Har ila yau an yi bayani a kan itaciyar kuka da nuna matsayin tag a al’ummar Hausawa. Bugu da ƙari binciken ya bayyana yadda ake sarrafa itaciyar kuka tun daga ganyenta, sassaƙenta, ƴaƴnta da saiwarta. Haka kuma binciken nada matuƙar muhimmanci domin zai taimakawa ƴan uwa ɗalibai da ma sauran masu nazari musamman ta fuskar itatuwa ko tsirrai na ƙasar Hausa.

BABI NA ƊAYA: GABATARWA

1.0 SHIMFIƊA

 Wannan babi zai yi bayani ne a kan muhimmin abubuwa da suka haɗa da manufar bincike, hasashen bincike, farfajiyar bincike, matsalolin bincike, muhimmin bincike tare da bayyana matsalolin da aka fuskanta yayin gudanar da wannan bincike.

1.1MANUFAR BINCIKE

Wannan binciken kamar sauran da suka gabace shi ya na da manufofi waɗanda ake fatar cimma a yayin da aka kamala wannan aiki kamar haka:

a. Tabbatar da cewa akwai amfani a cikin itaciyar kuka

b. Fito da irin magungunan da ta ke yi a gargajiyar Bahaushe

c. Tabbatar da ita a matsayin abinci kuma magani a ƙasar Hausa

d. Bayyana yadda ake amfani da ita wurin haɗa maganin gargajiya na

  Hausa

e. Bayyana Gudunmuwar itaciyar kuka wurin haɓaka tattalin arzikin

   ƙasar Hausa

1.2 HASASHEN BINCIKE

Wannan bincike na hasashen bayyana matsayin itaciyar kuka a idon Bahaushe, shin itaciya ce kamar sauran itatuwan da mu ke da su ƙasar Hausa ko ta na da wani matsayi na daban.?

Haka kuma ya na daga cikin hasashen wannan bincike bayyana itaciyar kuka a matsayin itaciyar magani ba itaciyar abinci kawai ba.

Duk a cikin hasashen wannan bincike na fito da yadda ake amfani da wasu sassan itaciyar wurin haɗa maganin gargajiya na Hausa.

Bugu da ƙari wannan binciken na hasashen bayyana irin yadda itaciyar ke nuna tarihin kafuwar wasu tsofaffin birane na ƙasar Hausa.

1.3 FARFAJIYAR BINCIKE

Kasancewar komai na duniya na da iyaka banda sarautar Allah. Haka ma wannan bincike ya na da ta shi iyaka, don haka za a gudanar da wannan bincike a gundumar Zurmi. Domin ganin yadda su ke sarrafa itaciyar kuka a rayuwarsu ta yau da kullum, ta fuskoki da dama.

1.4 MATSALOLIN BINCIKE

Haƙiƙa komai za a yi sai an samu nasara da akasin ta, a yayin gudanar da wannan bincike an ci karo da wasu matsaloli, sai dai ba su taka kara su ka karya ba. Domin kuwa ba su hana a gudanar da wannan bincike cikin tsanaki ba. Zamani irin wannan da ake yiwa al'adu da tarihi riƙon sakainar kashi dole a samu matsaloli wurin tattara bayanai irin wannan. Daga cikin matsalolin da aka ci karo da su a lokacin gudanar da wannan bincike sun haɗa da:

a. Rashin tsaro, domin akwai wasu mutane da ya kamata a tattauna da su amma rashin tsaro ya sa sun yi ƙaura daga mazauninsu na dindindin.

b. Rashin kuɗi kasancewar bincike ne da ya ke buƙatar tattaunawa mai tsawo da masana tarihi da maganin gargajiya, mutane ba su sakin jiki su ba da bayani don a tunaninsu ba sa samun na goro.

c. Ɓoye wasu bayanai da wasu daga cikin masu bayar da maganin gargajiya su ke yi.

d. Mutuwa da wasu tsofaffi su ka yi, waɗanda ya ke sun san sirrin da ke cikin itaciyar.

e. Riƙon sakainar kashi da wasu masu ba da maganin gargajiya ke yiwa sana'ar, wasu daga cikin masu bayar da magani saye suke yi hannun wasu, basu su ke haɗa maganin da kansu ba.

f. Kutsen ƴan haye cikin sana'ar magani. Wannan babbar matsala ce da ta ke abkuwa a cikin sana'ar ba da maganin gargajiya, domin ba su da cikakken sirrin maganin da su ke bayarwa saboda ba gado su ka yi ba.

1.5 MUHIMMANCIN BINCIKE

Nazari irin wannan mai ƙoƙarin fito da alfanun da ke ƙunshe cikin itaciyar kuka zai taimakawa ɓangarori da dama na manazarta itatuwa, tsirrai, da kuma masu nazarin maganin gargajiya na ƙasar Hausa.

Muhimmancin wannan bincike shi ne taskace bayanai don wasu idan sun zo su ɗora.

Ana fatar an tattarawa manazarta maganin gargajiya na Hausa wata taska da za su iya amfani da ita a wajen nazarin maganin gargajiya na ƙasar Hausa.

Manazarta itatuwa su ma za su samu taskar da za ta taimaka ma su wajen yin nazarin itaciyar cikin sauki da inganci.

Haka kuma masu bincike a kan magani a cikin adabin Hausa su ma wannan bincike zai taimaka wajen haskaka masu hanyoyin da za su gudanar da ayyukansu cikin sauƙi da inganci.

Bugu da ƙari ana fatar wannan bincike zai taimaka wajen masu nazarin al’adu da abincin ƙasar Hausa

1.6 HANYOYIN GUDANAR DA BINCIKE

 Kasancewar wannan bincike za a gudanar da shi ne a fagen al’ada don haka ya kyautu a ce an gudanar da shi ta hanyar tattaunawa, da tambayar masana magani da itatuwa na ƙasar Hausa. Duk da haka an duba wasu ayyukan bincike da masana da manazarta al’ada su ka yi kamar:

1. Wallafaffun littafai

2. Muƙalu

3. Kundayen bincike

4. Takardun da aka gabatar a taron ƙarawa juna sani

5. Da kuma bincikar shafin yanar gizo na intanet (internet)

6. Haka kuma an yi rangadin tattaunawa da wasu masu ba da maganin garjiya, tare da tuntuɓar wasu a wayoyin salula da manhajar wasof (whatsapp).

 

 

1.7 NADEWA

  Haƙiƙa komai ya yi farko sai ya yi ƙarshe, wannan shi ne ƙarshen wannan babi, wanda a cikinsa ya ke ƙunshe da gabatarwa tare da bayyana manufar wannan bincike ya kuma fito da hanyoyin da aka bi a yayin gudanar da wannan bincike, bugu da ƙari babin ya kawo matsalolin da aka ci karo da su a yayin tattara bayanai.

BABI NA BIYU: BITAR AYYUKAN DA SUKA GABATA

2.O SHIMFIDA

Wannan babi ya na ƙunshe ne da bayanai a kan bitar ayyukan da suka gabata na manazarta da masana a fagen ilimi, waɗan da hannu ya samu kaiwa gare su ayayin gudanar da wannan bincike, tare da bayyana hujjar cigaba da bincike. Kamar yadda zamu gani a cikin wannan babin.

2.1 BITAR AYYUKAN DA SUKA GABATA

 Masu hikimar magana sun ce " Nagaba idon na baya. Waiwaye adon tafiya". Kasancewar duk wani aiki da mutum zai yi, to akwai matuƙar wahala a ce ba a riga an yi irinsa ba. Wannan ne ya sa ya zama wajibi ga mai nazari da ya kawo ayyukan magabata da su ka yi aiki irin nashi ko mai kama da shi domin kafa hujjar cigaba ko faɗaɗa nasa binciken. Masana da manazarta sun yi bincike mai tarin yawa dangane da itatuwa da tsirrai da suka jiɓincin maganin gargajiya na ƙasar Hausa, wannan ne ya sa zan yi waiwaiye a kan wasu bincike da su ka yi kamanceceniya da wannan, wanda masan malamai da ɗalibai su ka gudanar.

 

WALLAFAFFUN LITTAFAI

Idanmu soma da wallafaffun littafai akwai masana da dama da suka wallafa littafai a kan maganin gargajiya da itatuwan ƙasar Hausa. Kamarsu:

Bakura,A.R dawasu (2019) sun wallafa wani littafi mai suna ‘Muhallin Zogala a Magungunan Gargajiya a Ƙasar Hausa’. Inda wannan littafin kaco kam ɗinsa ya na bayani ne a kan irin magungunan da ake yi da itaciyar ta zogala a ƙasar Hausa.

Jinju (1990) a cikin littafinsa mai suna ‘Maganin Gargajiya Na Afirka Tare Da Mai Da Ƙarfi A Kan Nazarin Itatuwan Magani Na Hausa’. Awannan littafi ya yi ƙoƙarin bayyana asalin magani da ire-iren masu ba da magani na ƙasar Hausa, tareda kawo wasu daga cikin itatuwan a kasar Hausa wanda ake amfani da su wurin haɗa maganin gargajiya. A wannan littafi ya ambaci itaciyar kuka da irin maganin da ake haɗawa da ita, sai dai bai zurfafa bayani ba dangane da irin magungunan da itaciyar take yi ba.Wannan ne ya sa zan faɗaɗa nawa binciken a kan irin magungunan da itaciyar ke yi.

Adamu,M.T (1998) shi ma a littafinsa mai suna ‘Asalin Magungunan Hausawa Da Ire-irensu’ . A wannan littafin ya yi ƙoƙarin bayyana asali da irin nau’o’ in magungunan gargajiya, sai dai shi ma bai ambaci wani sirrin magani da ke cikin itaciyar kuka ba.

MUƘALU

Idan mu ka zo kan muƙalu kuwa, akwai masu tarin yawa, sai dai zamu dubi wasu daga cikin waɗanda Allah ya sa hannu ya kai gare su. Kamar haka:

Karofi,Isah.A (2016) mai taken ‘’Gudunmuwar da Ganyen Bahaushe ke Bayarwa Wajen Samar da Magani’’ A cikin wannan muƙala ya yi ƙoƙarin kawo ire-iren ganye na ƙasar Hausa da ake amfani da su wurin samar da magani. Kash! Sai dai Karofi (2016) ɗin bai yi bayanin irin magugngunan da ake amfani da ganyen kuka ba wurin samar da su.

A wani bincike da Maryam da Yusuf (2017) su ka gudanar mai taken ‘’Nazari a Kan Ciyawar Rai-Dore’’ wannan binciken nasu ya yi bayani ne a kan itaciyar rai-ɗore da inda ake samun ta tareda kawo sinadaran da ke cikinta. Shi ma dai wannan binciken kamar wanda ya gabaceshi ne a wannan sashin domin kuwa bai yi bayani a kan itaciyar kuka ba.

Zulaihat (2017) ita ma ta yi wani nazari mai kama da wannan mai taken ‘Sauye-sauyen Zamani a Kan Sana’ar Ƴar Mai Ganye’ in da wannan bincike ya yi bayani a kan irin tasirin zamani wurin gudanar da sana’ar ,ƴar mai ganye a ƙasar Hausa. Shi ma dai haka ba ta yi bayanin sinadaran da ke cikin itaciyar kuka ba.

Ɗiso (2017) shi ma ya gabatar da wata takarda mai taken ‘Nazari a Kan Wasu Magungunan Hausawa Na Gargajiya’ .A wannan binciken nasa ya yi bayani a kan wasu tsirrai da itatuwa da ake amfani da suwurin maganin gargajiya, sai dai shima a binciken an yi wanka da kamar jirwaye domin kuwa babu in da a ka ambaci wani magani da itaciyar kuka ke yi.

Shira,M.B da Abdu,M.A (2017) suma sun yi wani bincike mai taken ‘Tsuntsaye a Mahaɗin Maganin Gargajiyar Bahaushe shi ma wannan bincike babu in da ya yi bayani a kan irin magungunan da ke cikin itaciyar kuka.

2.2 HUJJAR CIGABA DA BINCIKE

Idan mu ka dubi ayyukan da su ka gabata za muga cewa ko kaɗan ba su wadatar ba idan dai har a kace ana son sanin amfani da itaciyar kuka ke da shi wurin maganin gargajiya na Hausa. Jinju (1990) ya ɗan tsakuro wani abu kaɗan daga cikin amfanin itaciyar kuka a maganin gargajiya sai dai bai zurfafa bayaninsa ba.

Wannan ne ya sa na ga ya

kamata in yi wannan bincike na nazari a kan itaciyar kuka a Bahaushiyar al’ada, domin fito da irin ɗimbin sinadaran da itaciyar ke ɗauke da su a wajen samar da maganin gargajiya. Waɗanda shi bai kawo a cikin bincikensa ba.

2.3 NAƊEWA

   A wannan babi an yi waiwaye adon tafiya ne a kan wasu daga cikin ayyukan masana da suka gabata domin kafa jujja, tare da bayyana hujjar cigaba da wannan bincike duk a cikin wannan babi.

 

BABI NA UKU : MAGANIN GARGAJIYA A BAHAUSHIYAR AL’ADA

3.0 Shimfiɗa

   Wannan babi zai yi bayani ne a kan ma'anar al'ada, da ma'anar maganin gargajiya, tare da bayyana wasu daga cikin adabin baka na Hausa da su ke magana a kan magani, kamar : Tatsuniya, karin, magana, kirari da kuma waƙar baka.

Kamar yadda za mu iya cewa Bahaushiyar al’ada na nufin tsantsar gargajiyar Bahaushe a tunaninsa da ayyukansa.

3.1 MA’ANAR MAGANI

   Magani na nufin duk wata hanya da ake bi don neman waraka ko kariya daga wata cuta ta ciki ko ta waje. Masana da dama sun tofa albarkacin bakinsu dangane da ma’anar magani kamar irinsu:

Bunza, (1990-shf na 134) ya bayyana cewa “Magani wata hanya ce ta warkar da ko kwantar da rage cuta ta ciki ko ta waje ko wadda aka samu ta hadari. Ko kuma neman ɗaukaka ta daraja ko buwaya ta hanyar siddabaru da sihirce-sihirce.’’

Sallau (2010) "Kalmar magani tana nufin duk wata dabarar yi wa cuta ta jiki ko ta zuci barazana don kawar da ita, ko a rage mata karfi, ko a yi mata riga-kafi."

 Shi kuwa Gulbi, (2004) cewa ya yi " Magani shi ne duk wata hanya da za a yi amfani da ita domin riga-kafin cuta, ko rage raɗaɗinta, ko ma a kawar da ita gaba daya, ko a warware wata matsalar rayuwa. Galibi Bokaye, da Malaman tsibbu, da wasu da suka yi fice a sana’o’in gargajiya, da kuma wasu mutane na musamman suke bayarwa. Wannan hanyar tana iya kasancewa ta kimiyar zamani, ko kuma a gargajiyance (watau hanyar tsafi da tsibbace-tsibbacen al’umma).

 Kamusan Hausa, (2006:shf.316) ‘’Magani shi ne, abin da ake sha ko shafawa a jiki ko daurawa a jiki ta hanyar yin allura, don neman samun lafiya.’’

 Ingawa, (1984:25) a tasa fahimtar ya nuna cewa ‘’Magani hanya ce ta neman kawar da cuta ko wace iri ko kuma neman kariya daga gare ta ko kuma neman gwanancewa da ƙwarewa kan wani abu.’’

Gobir, (2013:365) cewa ya yi ‘’Wata hanya ce ta kawar da, duk wata cutar jiki ko ta zuciya, ko neman ɗaukaka, ko kariya daga makaru da jifa da sihiri ko siddabaru.’’

Adamu, M. T (1998) ya bayyana cewa‘’ Magani shi ne duk wata abu da za a yi, ko wata hanya ko kuma dabara da za a bi don gusar da cuta daga jiki ɗungum, ko kuma kwantar da ita don kawo jin daɗi ga jiki tare da sauwaƙe duk wata wahala da damuwa da ita cutar kan iya samarwa ne ta hanyar mai ilimin magunguna tare da cututtula wanda shi ake kira mai magani.’’

 Bugu da ƙari ya bayyana cewa shi magani an raba shi zuwa manyan ɓangarori guda biyu :

(a) Magunguna na Ɗabi'a: Irin wannan waɗannan su ne waɗanda ido kan gani kuma a yi amfani da su zuwa ga ciwo kai tsaye. Kamar itatuwa, sassaƙe-sassaƙe, ciyayi, ƙasusuwa, gashi, fatu, ƙasa da dai sauransu.

(b) Magunguna na Addu'a: Irin waɗannan kuwa su ne waɗan da ba a amfani da su zuwa ga ciwo kai tsaye. Irin waɗannan sun haɗa da karance-karance, wuridai, janye-janye, nafiloli, fawadai, rubutun sha, laya, guru, ɗamara, kambu, rataye da dai ire-irensu.

A fahimtar Tukur (1988) kuwa cewa ya yi " Magani shi ne duk wani abu da ɗan Adam kan yi don samun warkarwa da buƙata da ɗaukaka a rayuwarsa ta kullum don kuwa ɓangaren rayuwar ɗan Adam duk tafiya take wajen fafitikar neman maganin warkar da cututtuka da kwantar da damuwar zuciya, in ya samu, sai kuma ya shiga neman maganin ɗaukaka da kariya wajen abokan hamayya. Haka rayuwar ɗan Adam take tafiya kullum. In ya yi maganin wannan buƙatar yana buƙatar wancan."

Yahaya (1992) kuma a tasa ma’anar ya nuna " Magani wata hanya ce wadda ake amfani da ita don kuɓutar da rai daga wata cuta da ya kamu da ita wadda ta ɗarsu a sassan jiki. "

3.1.1 MA'ANAR MAGANIN GARGAJIYA

 Maganin gargajiya a ra'ayin wasu masana kamar Alhasan da wasu (1988) Zurmi (2004), Imam, A. H (2017) Sallau (2000). Sun bayya na shi kamar haka:

Alhasan da wasu (1988) Zurmi (2004) sun bayyana " Maganin gargajiya shi ne yin amfani da itatuwa ko rubutu ko addu'a ko surkulle don warkar da wata cuta, ko neman wani amfani, ko gusar da sharri, ko haddasa wani abu saboda biyan buƙata."

Sallau (2000) cewa ya yi " Ƙoƙarin kawar da cuta ko wace iri daga jikin mai fama da ita, ko kwantar da ita, ko kuma neman kariya daga kamuwa da cuta, ko abokan hamayya ko maƙiya, ko kuma neman gwada bajinta da ƙwazo da ɗaukaka da daraja a idon mutanevta hanyar tsatsuba da sihirce-sihirce masu ban tsoro da mamaki da al'ajabi."

Imam, A. H (2017) " Maganin gargajiya shi ne maganin da al'ummar Hausawa suka gaje shi iyaye da kakanni. Kafin Hausawa su sadu da wata al'umma, suna yin amfani da sassaƙe ko saiwoyi ko ganye ko gadali da sauransu. In kuma ciwon na waje ne sai a shafa masa magani, kamar ƙurji ko kumburi, in kuma ya yi ruwa sai a yi masa sakiya. Haka kuma ana yin ƙaho da wasu hanyoyi na warkar da majinyaci cutar da take damunsa ta ciki da ta waje.

A tawa fahimta maganin gargajiya na nufin duk wata hanya ko dabara da al'ummar Hausa ke bi wurin biyan kowace irin buƙata ta rayuwa, wadda su ka gada iyaye da kakanni ta hanyar amfani da ganye, saiwa, sassaƙe, fure, ƙasa duwatsu da wasu sassa na tsuntsaye ko dabba domin biyan buƙatunsu na yau da kullum.

 

 

3.1.2 MAGANI A ADABIN BAKA NA HAUSA

 Kasancewar adabin baka na Hausa ya shafi komai na rayuwar Hausawa daga haihuwa zuwa mutuwa, wannan ne ya sa tilas a samu ɗuriyar maganin Hausawa a cikinsa. Kamar a cikin waƙa, karin magana, tatsuniya, kirari, da wasu daga cikin maganganun azanci, da makamantan su kamar yadda zamu gani.

 

3.1.2.1 MAGANI A WAƘOƘIN BAKA NA HAUSA

Makaɗa da mawaƙan ƙasar Hausa na ambatar magani a cikin waƙoƙinsu na yau da kullum, har ma wasu na kiransa da wani suna na daban saboda nuna ƙwarewa da nakaltar harshe a lokacin da su ke aiwatar da waƙoƙinsu. Kamar: Makaɗa Kassu Zurmi ya kira magani da kalmar ' tambaya, gari, tuƙe, karhu, ƙi-bugu.' A cikin waƙarsa da ya yiwa Daɗi.

 Ga wasu kaɗan daga cikin ɗiyan waƙar kamar haka:

Jajora: Don dai ba ni da ƙwazon "tambaya"

          : Da Ancana bai tarbe ni ba.

          : Ah ah Katakare ni ka tambaya,

          : In ka raga "tuƙe" ƴammani.

          : Gandau in ba ka yi,

          : In ka raga "Kambu ƴammani."

          : Ko hwadama ni kai,

          : In ishe Isa ɗan maɗi,

          : Su nij ji su na ta hwa Isa,

          : Kai ko ƴamman "ƙi-bugu."

          : Ina Gugurugu ɗan Mande,

          : Ah ku ni ka tambaya,

          : Kowar raga "gari" so ni kai.

Haka shima makaɗa Gambo ya ambaci magani da kalmar tambaya a cikin waƙar Tsoho Tudu.

Jagora  : Ɗan dahi Manu

        : Wanga da ag Gambere ɗaure

        : Ko bataliyas soja tas shiga daji

        : In gaya maka Manu Dahi na ɗan taya ta.

       : Yac ce min: mis samu Gambo?

       : Nac ce: "Tudu Tsoho yat taɓa ni"

      : Yac ce : Maganar banza da wofi..

     : In akwai ta da daɗi ka tai da kanka

     : Ai ba mu tcarma "tambaya" ba.

3.1.2.2  MAGANI A TATSUNIYA

 Tatsuniya na daga cikin rassan adabin baka na Hausa, wadda take tsokaci a kan al'ummar Hausawa da bayyana al'adunsu. Wannan ne ya sa itama za a iya samun tatsuniya mai ɗauke da jigon magani.

Kamar:

(a). Tatsuniyar Ruwan bagaja

(b). Tatsuniyar Ɓorai

3.1.2.3 MAGANI A MAGANGANUN AZANZI

Rukunin maganganun azanci a adabin bakan Bahaushe rukuni ne da ya ke da rassa da yawa wanda ke nuna irin hikima ko fasahar Hausawa wajen sarrafa harshensu a lokacin da su ke magana. Wannan rukuni ya ƙunshi fasahohi irin su: Almara, karin magana, salon magana, baƙar magana, habaici, ba'a da tatsuniya. Ga misalin yadda magani ke rausayawa a wasu daga cikin su.

 Almara :

Almara wata gajeruwar ƙagaggen labari ce da ake bayarwa, sannan a ɓuƙaci mutum ya faɗi amsa ko ya yi zaɓi tsakanin abubuwan da aka ambata. Galibi almara kan ƙare da : "In kai ne ya ya za ka yi? " Ko kuma " Cikin su wanne ya fi....?" A irin wannan nau'i na zuben adabin baka, hoton magani yakan fito ƙarara kamar dai yadda ya ke a rayuwa ta zahiri. Misali:

Wani magidanci ne mai mata biyu da ƴaƴa da yawa ya kwanta rashin lafiya shekara da shekaru ciwo ya ƙi ci, ya ƙi cinyewa. An yi maganin duniyar na amma Allah bai sa an dace ba. Uwar gidansa ita aka bari da ɗawainiyar jinya. Ita ke kwashe kashi da fitsarin da ya ke yi, ita ke ba shi magani, ta yi abinci da kula da yara ta tsabtace gida da dai duk sauran aikace-aikacen gida. Ita kuma amaryar ita ke fita ta na aikin ƙarfi, ta sami kuɗi ta sawo abinci a ci a gidan. A cikin wannan hali aka kasance shekara da shekaru. Ana nan sai wata rana aka sami wani mai maganin da ya ba da tabbacin ya na da maganin wannan cutar. Sharaɗin kawai da ya bayar wanda ya nuna sai an yi shi maganin zai ci shi ne, sai majinyaci ya saki mata ɗaya daga cikin matan nan nasa. To idan kai ne majinyanci wacce za ka saka?

A wannan almara an kawo matsala, aka nuna magani ya kasa samuwa cikin sauƙi. Wannan da ma al'ada ce ta ciwo. Bahaushe ya yarda da cewa, magani sai dace. Bayan da aka samu magani kuma, sai almarar ta ƙara fito da wata al'adar bayar da magani a rayuwar Hausawa. Wato kafa sharaɗin amfani da magani. Haƙiƙa wannan misali ya tabbatar da nason magani a adabin bakan Bahaushe.

 Karin Magana :

Karin magana kamar yadda magabata su ka nuna, dabara ce ta dunƙule magana mai yawa a cikin zance ko ƴan kalmomi kaɗan cikin hikima. (Ɗangambo 1984:38). Fasaha ce da kan ƙarawa zance armashi da bayyana halayen rayuwar Bahaushe na haƙiƙani. Hausawa sun yi fice ainun wajen amfani da karin magana a zantuttukansu na yau da kullum. Kamar yadda sha'anin ya yi ta watayawa a tatsuya da almara, haka ya sami ranar shanya a karin magana.

Ga wasu kaɗan daga cikin Karin Magana da su ke ɗauke da magani kamar haka :

(a). Magani da kuɗi wuyar sha

(b). Maganin biri karen Maguzawa

(c). Maganin a faɗi a tashi

   (d). Haƙuri maganin zaman duniya

   (e). Maganin maƙi gudu ban kashi

   (f). Shiru maganin mai tsince

   (g). Karen bana shi ke maganin zomon bana

    (h). Da tsohuwar ake magani

    (i). Da kura na da maganin zawo da ta yiwa kanta

    (j). Magani a sha ka ba don yinwa ba

    (k). Haihuwa da yawa maganin annoba

    (l). Gobara daga kogi maganinta Allah

 3.2 MA'ANAR BAHAUSHIYA

Kalmar Hausa idan an mata ƙari na ɗafa ƙeyar -awa a ƙarshenta a samar da kalmar Hausawa. Haka kuma an yiwa tushen kalmar Hausa - Haus- ƙari na ɗafa goshi na ƙwayar ma'anar ba- a gabanta da sauya baƙin ƙarshe na tushen kalmar daga s>sh tare da canja wasalin ƙarshe na kalmar daga a>iya a lokaci guda dokin samar da kalmar Bahaushiya ta mata, tilo.

3.3 MA’ANAR AL’ADA

 Al’ada kalma ce da aka aro ta daga Larabci aka mayar da ita yar gida, a Hausa ma’anarta ita ce sabbaben abu wato abin da aka saba da shi. Al’ada na nufin hanyar rayuwar ƴan Adam daga haihuwarsu zuwa mutuwa, wanda ya shafi addini, kasuwanci, bukukuwa, sana’a da dai sauran abubuwan da suka shafi rayuwar ɗan Adam gaba ɗaya.

Masana da manazarta da dama sun ba da ma’anar al'ada kamar:

Magaji (2001) cewaya yi ‘’ Al’ada ita ce hanyoyin da al’umma ta ke gudanar da rayuwarta waɗanda suka haɗa da abinci da sutura da muhalli da gine-gine da sadarwa da wasanni da sauran muhimman abubuwa na wannan al’umma.’’

Abdulmumin (2004) ya nuna ‘’ Al’ada na nufin hanyar rayuwa da ta zama karbabbiya ga mafi yawan jama’a wannan sun haɗa da tufafi da abinci da sauransu.’’

Dangambo (1984) ya bayyana ta da ‘’ Al’ada ita ce abinda aka saba yi yau-da-gobe.’’

Umar (1989) a ta sa ma'ana ya nu nuna‘’ Al’ada ta na nufin wata sabbabiyar rayuwa ce wadda akasarin jama’a na cikin al’umman Hausawa suka amince da ita.’’

Abdullahi (1984) kuma a tasa ma'anar ya nuna ‘’ Al’adu dai su ne dukkan hanyoyin rayuwa na al’umma; watau kenan al’adu sun ƙunshi dukkan abubuwa da su ka shafi zaman kowace al’umma.’’

Bargery (1984) ya fassara kalmar da cewa ‘’ Al’ada ta na nufin dabi’a ko halayya ko kuma hanya ta rayuwar jama’a.’’

Mahdi (1980) ‘’Al’ada ita ce baki ɗayan fasahar wata al’umma, abubuwan da su ka yi ko su ke yi da waɗanda suka faru gare su ( na alheri ko akasin haka) da buƙatunsu, haka kuma da nasarar da su ka samu a ƙoƙarinsu na shekara da shekaru wajen mallakar abubuwan da su ke kewaye da su domin biyan bukatunsu.’’

3.4 NAƊEWA

Kamar yadda mu ka gani a wannan babi an yi bayani ne a kan ma'anar bahaushiya, da al'ada, ma'anar magani da maganin gargajiya, da kuma kawo wasu kaɗan daga cikin adabin baka na Hausa wanda ya ke magana a kan magani. Haka kuma duk a cikin wannan babin an bayyana irin yadda wasu daga cikin Makaɗan Hausa su ka kira kalmar magani a cikin wasu ɗiyan waƙoƙinsu. Kamar: Makaɗan Kassu Zurmi da Makaɗan Muhammadu Gambo Fagada.

 

BABI NA HUƊU : ITACIYAR KUKA A IDON BAHAUSHE

4.0 SHIMFIƊA

Wannan babi zai yi bayani ne akan itaciyar kuka a idon Bahaushe, matsayinta da inda ake samunta tare da bayyana amfanin ta, da kuma la'akari da yadda Hausawa su ke sarrafa ta a al'amurransu na yau da kullum.

4.1 MA’ANAR ITATUWA

    Ƙamusan Hausa (2006) ya bayar da ma’anar itace da “Bishiya ko ice.”

Abdullahi (1989) ya bayar da ma’anar itatuwa da “Wani nau’in halitta da ke fitowa a wani wuri ko muhalli waɗanda sukan fara daga tsiro ta hanyar shuka ko dasawa ko kuma fitowa da kansu. Sannan ya yi tsawo tare da manya-manyan rassa da yawan ganye da kuma dogayen jijiyoyi waɗanda suke nutsewa cikin ƙasa domin samun ruwa. Ya ƙara da cewa wasu itatuwan sukan yi tsawo sosai, wasu kuma gajeru ne.

4.1 ITACIYAR KUKA

Kuka itaciya ce mai tsayi da faɗi kuma ta na da ganye mai launin kore, kuma ta na da ƴaƴa, waɗannan ƴaƴan idan suna farkon fitowa ana kiransu 'guliya' idan kuma suka girma an kiransu 'ƙwame' (kwalaba). Ana samun itaciyar a ƙasashe da dama da ke farfajiyar Afirka, ƙasar Hausa na ɗaya daga cikin yankunan da Allah ya albarka ce su da ita.

Itaciyar na daga cikin itatuwa masu yawancin rai a doron ƙasa, akan samu wata itaciyar ta yi tsufan da za a ce shekarunta sun kai ɗari biyar (500) koma fiye da hakan.[1]

4.1.1 KUKA : MA'AUNIN WANZUWAR GARURUWA A ƘASAR HAUSA

Tun shekaru aru-aru da suka shuɗe babu shahararrun gine-gine da za a samu a ƙasar Hausa, da ke iya zama wani ma'auni na tabbatar da wanzuwar tsohuwar rayuwar rayuwar wata al'umma a ƙasar Hausa fiye da rukunin kukoki.

Bincike ya tabbatar da cewa duk inda aka samu itatuwan kukoki sun jeru reras, ko sun yi da'ira, ko wani abu mai kama da haka, to babu ko tantama gari ya taɓa wanzuwa a wannan muhallin. Hasali ma ana sanin ana fahimtar daɗewar gari gami da tumbatsarsa daga kukoki.[2]

 

Bishiyar Kuka

4.1.2 KUKA : A MATSAYIN MA'ADANAR RUWA

Al'ummomin da suka gabata, musamman waɗanda ke kan hanyar zuwa Sudan data Togo daga ƙasar Hausa, sukan yi amfani da itaciyar kuka domin adana ruwa. Itaciyar kan aje ruwa sama da ganga dubu (1000 later) a gindinta. Wannan ne ya sa wasu daga cikin al'ummar Hausawa su ke sara jikin itaciyar domin adana ruwa, su na sayar wa mutanen da ke tafiya ƙasa, musamman waɗanda ke zuwa aikin hajji ta ƙasa a wancan zamanin.[3]

4.1.3 KUKA: A MATSAYIN MAƊAURI

Kafin bayyanar fasahar zamani al'ummomi da suka shuɗe sukan sarrafa itaciyar kuka domin samar da maɗauri ta hanyar yin igiya da ɓawon kuka domin ɗaure dabba ko kaya.

4.1.4 DABARUN HAWAN ITACIYAR KUKA

Itaciyar kuka na da mutuƙar wahala wurin hawan ta ba kamar sauran itace ba. Wannan ne ya sa Makaɗa Kassu Zurmi ya ambace ta a waƙar da ya yi wa ƴan Jabanda. Ga ɗan waƙar:

      Jagora: Ban hana yaro hawan kuka ba na Ahmadu,

            : Amma hwa ya santale takalmi.

A wannan ɗan waƙa ya nuna cewa kuka ba ta hawuwa da takalmi, dole idan ana so a hau ta lafiya sai an cire su.

Hausawa na da dabaru da su ke bi wurin hawan itaciyar, waɗanda su ka haɗa da:

(a). Akan yi amfani da gatari mai kai biyu, gaba tsini baya kaifi ana sarawa sai a  cakawa sai a riƙa a hau.

(b). Akan yi amfani da kwashe a sara jikin itaciyar ayi matakai.

(c). Akan yi amfani da igiya, a jefa saman itaciyar sai a riƙa ta a hau.[4]

 

4.1.5 WASU ZANTUKAN HIKIMA GAME DA ITACIYAR KUKA

Zantukan hikima maganganu ne gajeru da aka gada kaka da kakani, wanɗanda aka tsara cikin hikima da nuna ƙwarewar harshe. Ga su kamar haka:

(a). Kuka baki shekara ba miki.

(b). Kuka uwar iskoki kowa ya hauki zai ga takansa.

(c). Kuka kin wuce runguma sai sara.

(d). Kuka mai hana kukan yaro.

(e). Miyar kuka Bahaɗejiya idan ta kwana ta fi giya tsiya.

(f). Kuka mai rabon tuwon gayya.

(g). Kuka baƙar miya in baki sha ba a gidan ubanki ki sha gidan miji.[5]

 

4.2 IN DA AKE SAMUN ITACIYAR KUKA

     Muhalli shi ne wuri na gida ko gona ko wani wurin da jama’a ke zaune a cikinsa (CNHN, 2006:318).

Muhalli waje ne da al'umma da dabbobi da tsirrai ke rayuwa. Muhalli ya ƙunshi abubuwa kamar yanayin sarari, ƙasa,tudu, tsauni, bakin gulbi da cikin gida.

Kasancewar komai da muhallinsa, kuka na cikin itacen da akan iya samu a cikin itatuwan gida da na daji. Daga cikin muhallan da akan iya samun itaciyar kuka a gundumar Zurmi da sauran sassa na ƙasar Hausa sun hada da: gona, fadama (lambu), bakin gari, cikin gari harma akan iya samun ta a a cikin gida.

Saɓanin wasu itatuwa da a daji akafi yawan samun su, kamar: kalgo, ɗorowa, giginya, goriba, aduwa da sauransu.

 

4.3 MATSAYIN KUKA A GARGAJIYA

Gargajiya dai na nufin ɗabi'a ko wani kaya irin na zamanin da. (Kano,2006 : 159).

A Hausa akan kira garjiya da wasu kalmomi kamar:

1. Gado daga tsohon zamani. Hali ko al'ada mai asali tun da.

2. Abinda ba wannan zamanin aka tsire shi ba.

3. Abinda al'umma ta gada daga zamanin da ya shuɗe,(Abubakar, 2015:156).

A gargajiyance, Hausawa na kallon itaciyar wata itaciya ce ta daban, domin kuwa duk sun yi imani da cewa icce ne wanda ya ke wurin zama ne na aljannu.

"Kuka a al'adun mutanen duniya da Afirka da Turai da Asiya sun ce mazaunin iskoki ne. " (Bunza 2000:11).

 

4.3.1 KUKA A MATSAYIN ABINCI

Wikipedia ta bayyana abinci da cewa "Abinci wasu sinadarai ne na ƴaƴan itatuwa da tsirrai, waɗanda ake sarrafawa ta hanyar dafawa domin ya gamsar da yunwar ɗan Adam."

 A wata ma'anar kuma ta bayyana abinci da cewa duk wani abu da za a ci, sannan kuma ya bai wa jiki sinadaran da ya ke buƙata domin samun ƙarfi. Yawancin abincin da ake ci a kan samo shi daga tsirrai da kuma dabbobi.[6]

Duba da waɗannan ma'anoni na abinci da su ka gabata mu na iya cewa Hausawa sun ɗauki itaciyar kuka a matsayin itaciyar abinci. Saboda dalilai kamar haka:

(a). Akan yi amfani da ganyen kuka ɗanye ko busasshe wurin yin miyar tuwo

(b). Akan burke ƴaƴan kuka a haɗa da suga a sha.

(c). Akan haɗa garin ƴaƴanta da nono a sha.

(d). Akan yi amfani da garin kuka wurin haɗa ɗan wake.[7]

 

4.3.2 KUKA A MATSAYIN MAGANI

Masana da dama sun tofa albarkacin bakinsu dangane da ma'anar magani.

Ingawa (1984:25) ya bayyana magani da cewa " Hanya ce ta neman kawar da cuta kowace iri, ko kuma neman kariya daga gare ta ko gwanancewa da ƙwarewa kan wani abu."

Idan mu ka dubi wannan ma'anar da aka bayar ta magani, zamu iya cewa itaciyar kuka itaciyar magani ce. Saboda dalilai kamar haka:

(a). Akan sarrafa ganyenta wurin haɗa magani daban-daban.

(b). Akan yi amfani da sassaƙenta wurin yin maganin cutuka da dama.

(c). Akan yi amfani da furenta wurin haɗa magani.

(d). Akan yi amfani da saiwarta wurin warkar da cutuka da dama.[8]

 

4.5 HANYOYIN SARRAFA ITACIYAR KUKA

Kusan komai na itaciyar kuka na da amfani da kuma yadda ake sarrafa su, tun daga ganyenta,sassaƙenta, saiwarta da ƴaƴanta kamar yadda zamu gani a sashen da ke bima wannan yanzu.

4.5.1 AMFANIN GANYEN KUKA

Garin Kuka

kamar yadda na yi bayani a baya cewa itaciyar kuka na da ganye mai launin kore, akan sarrafa wannan ganyen ɗanye da busasshe ta fuskoki daban-daban wurin haɗa maganin gargajiya na Hausa kamar haka:

               i.            Akan sha garin kuka da madara domin maganin gyambon ciki ( ulsa)

            ii.            Akan jiƙa garin kuka a bai wa marar lafiya ya sha shi hakanan idan mutum na fama da matsananciyar rashin lafiya an rasa gane abin da ke damunsa. Za a sha shi hakanan ba sai an tace ba da yardar Allah za a samu sauƙi

         iii.             Akan kwaɓa garin kuka da ruwa kaɗan a saka wurin da aka ji ciwo/rauni domin tsayar da zubar jini.

          iv.             Idan mutum ba shi da lafiya ana jiƙa garin kuka a bashi ya sha.

             v.            Akan yi turare da tsakin garin kuka domin maganin mayu.

          vi.             Akan daka ɗanyen ganyen kuka a tace a sha maganin gyambon ciki.[9]

4..5.2 AMFANIN SASSAƘEN KUKA

Sassaƙen Kuka

Sassaƙe shi ne bayan itaciya wanda ake amfani da ƙarfe, gatari kwashe, ko haƙori wurin ɗibar sa. Wannan kuma ya dangata ne daga doka da aka bai wa wanda zai je ɗibar sa.

Wasu daga cikin amfanin da ake yi da sassaƙen itaciyar kuka sun haɗa da:

               i.            Ana amfani da busasshen sassaƙen kuka wurin haɗa maganin ƙarfe. Za ɗebo sassaƙen kuka mai tsayi da faɗi sai a shanya tsawon kwana biyar, idan ya bushe zai naɗe, sai a dake a riƙa sha da fura ko nono.[10]

            ii.            Akan dafa sassaƙen kuka asha shi da zuma tsawon wata ɗaya domin maganin hawan jini.

         iii.             Aɓangaren ciwon hawan jini kuwa akan dafa sassaƙen kuka a sha shi hakanan tsawon wata uku.[11]

          iv.             Akan yi amfani da sassaƙen kuka wurin maganin cutukan fata. Akan shanya sassƙen kuka idan ya ɓushe sai a dake a haɗa da man shafawa ko a riƙa shafa hakanan a jiki, yin hakan ya na warkar da cutukan jiki.

             v.            Akan daka (sauɓe) ɗanyen sassaƙen kuka a haɗa da kwalin suga mai iyali a ba amare su sha domin ƙarin ni'ima.[12]

          vi.             Akan yi amfani da sassaƙen kuka wurin haɗa bauri da ake bawa jarirai, su kan yi ƙiba amma babu nauyi kuma ba sa ƙarfi.

       vii.             Akan dafa sassaƙen kuka a sa cikin kofi a riƙa bawa yara su na sha.

     viii.            A ɓangaren maganin mayu kuwa akan daka busassen sassƙen kuka a yi wanka da shi. Yin hakan na sa mayu ba sa ganin kurwar mutum.[13]

 

4.5.3 AMFANIN SAIWAR KUKA

Amfanin Saiwar Kuka

Saiwa wasu ƙanana da manyan jijiyoyi ne da su ke a jikin ɗan Adam da dabba da tsirrai da itace.

Ga wasu kaɗan daga cikin amfanin da saiwar itaciyar kuka ke yi.

               i.            1.Akan yi amfani da saiwar kuka wadda ta ratsa hanya domin mallake zuciya mace/namiji. Akan haɗa abinci da saiwar abawa saurayi/budurwa ya ci don mallake shi/ ta

            ii.            2. Akan yi amfani da saiwar kuka domin magance ciwon kunne. Idan aka haƙo saiwar za a dafa ta sai a bawa mai ciwon kunne ya sha, sannan a samu tsumma a riƙa sakawa cikin ruwan ana fitarwa ana dannawa gafen kunnen.[14]

'Ya'yan Kuka

4.5.4 AMFANIN ƳAƳAN KUKA

               i.            Akan yi amfani da ƴaƴan kuka wurin maganin basir. Akan jiƙa ƴaƴan kuka su jiƙa sosai sai a burke sannan a riƙa sha, yin haka ya na maganin basir.

            ii.            Akan yi amfani da ƴaƴan kuka domin sa nono ya yi kauri, za a haɗa ƴaƴan kuka ko garinsu da ƙanƙara.

         iii.             Akan tsotse garin da ke cikin ƴaƴan kuka ko a wanke sai a shanya idan su ka bushe sai a soya ƴaƴan sannan a haɗa da jar kanwa a dake su tare, sa'annan asa ruwa kaɗan a kwaɓa sai a riƙa ɗiba ana sakawa ga hauren da ke ciwo (haƙora).[15]

          iv.             Yara kan daka ƴaƴan kuka su sha domin ƙwalama.

 

4.6 NAƊEWA

A wannan babi an yi bayyani ne game da itaciyar kuka, tare da nuna irin yadda Hausawa su ke sarrafa ta ta fuskoki da dama. Haka kuma duk a cikin wannan babi an bayyana muhallin da ake samun itaciyar, tare da nuna hoto dan ƙarin bayani gameda wannan itaciyar.

BABI NA BIYAR : KAMMALAWA

5.0 SHIMFIƊA

Wannan babi zai yi bayani ne akan muhimman abubuwan da wannan ɗan ƙaramin binciken nawa ya tabbatar. Tare da bayar da shawarwari dangane da wannan bincike. Haka kuma duk a cikin wannan babi za a kawo manazartar wannan bincke.

5.1 SAKAMAKON BINCIKE

Haƙiƙa duk wani abu da aka gudanar a rayuwa akwai wata manufa da ake so aga an cimma, musamman bincike irin wannan. Kazalika da wasu nasarori da ake sa ran a cimma, ko za a cimma su a yayin da aka kammala shi.

 Daga cikin nasarorin da aka samu a wannan bincike ya tabbatar da abubuwa kamar haka:

a.   Binciken ya tabbatar da cewa itaciyar kuka ta taimaka ainun ga al'ummar Hausawa, ta fuskoki da dama domin an bayyana yadda su ke sarrafa ta wurin biyan buƙatunsu na yau da kullum.

b.    Haka kuma binciken ya tabbatar da cewa magani a wurin Bahaushe mahadi ne mai dogon zamani, domin har an samu nason sa a cikin adabin Bahaushe.

c.    Har ila yau an tabbatar da cewa itaciyar kuka ba itaciyar magani ba ce kawai, ta na daga cikin itatuwan da suke na magani kuma a wani wurin a matsayin abinci ga al'umma.

d.   Bugu da ƙari a binciken an tabbatar da a da ana gane kafuwar gari, cikarsa da tumbatsarsa ta kukoki.

e.   Daga ƙarshe binciken ya nuna cewa ba al'ummar Hausawa ba kawai har wasu daga cikin sassan na duniya, irinsu Asiya, Turai sun tabbatar da cewa itaciyar kuka mazaunin aljannu ne.

5.3 SHAWARWARI

Idan aka dubi wannan bincike za a ga cewa ya ƙunshi bayani ne na yadda Hausawa suke kallon itaciyar kuka, da kuma yadda suke sarrafa ta a rayuwarsu ta yau da kullum. Don haka nake ganin yakamata in bayar da wasu ƴan shawarwari kamar haka:-

a.  Yakamata a samu kwararrun masana masu sha'awar bincike, su bi silalen diddigin itatuwan da muke da su a ƙasar Hausa domin sannin alfanun da ke tattare da su. Domin a bayyanawa al'umma shi suma su amfana.

b.   Yakamata malamai masana al'ada da maganin gargajiya su zurfafa bincike a kan mahaɗi ko tushen maganin garjiya na ƙasar Hausa, domin share fage ko kakkaɓe ƙura ga malaman kimiya domin idan sun zo su ɗora.

c.   Kar mu biye wa zamani mu watsar da abincinmu na gargajiya, saboda wasu masana kamar Jinju da Bunza su na ganin duk abincin da Hauwasa ke ci magani ne.

5.3 NAƊEWA

    Haƙiƙa komai ya yi farko sai ya yi ƙarshe, wannan shi ne ƙarshe wannan wannan bincike da na gudanar, mai taken ' Nazari Akan Itaciyar Kuka A Bahsaushiyar Al'ada'. Wanda a cikinsa aka yi bayanin abubuwa da dama, kuma an tsara su ne a jerin babi babi.

   A babi na farko an yi bayani ne dangane da manufar wannan binciken, da hasashen bincike, farfajiyar bincike, tare da bayyana matsalolin da aka ci karo da su a yayin gudanar da wannan bincike. Haka kuma an bayyana muhimmancin bincike da hanyoyin gudanar da bincike, duk a cikin wannan babin.

Babi na biyu kuwa, an yi waiwaye adon tafiya ne a kan bitar wasu daga cikin ayyukan magabata waɗanda su ka gabaci wannan bincike. An kuma bayyana hujjojin cigaba da wannan bincike.

Babi na uku kuwa, ya yi fashin baƙi ne a kan wasu daga cikin tubalan kalmomi da suka jiɓanci taken wannan bincike, waɗanda suka haɗa da : ma'anar Bahaushiya, ma'anar al'ada, magani, maganin gargajiya, tare da kawo wasu rassa daga cikin rassan adabin baka na Hausa wanda su ke magana akan magani.

A babi na huɗu kuwa a nan ne aka dake, aka sheƙe, aka rairaye wannan aiki. Domin a cikinsa ne aka yi bayani a kan itaciyar kuka, amfaninta ga al’umma, da bayyana muhallin ta, da kuma gudunmuwar ta a ƙasar Hausa.

 

MANAZARTA

 

Abubakar, A. T (2015) "Ƙamusan Harshen Hausa" Zaria: Northern

    Nigeria Publishing Company Limited.

Adamu, M. T. (1998). "Asalin Magungunan Hausawa da Ire-Irensu".

    Kano : Ɗan Sarkin Kura Publishers Ltd.

Ado, A. (2019) "Kimiyar Hausawa a Game da Yanayi da Muhallinsu:

   Nazari Kan Yanayin Damina a Jihar Katsina". Ɗanmarna

   International Journal of Multi-Disciplinary Studies, Vol 10. No 1.

   Pp:167-182. Sashen Harsunan Nijeriya, Katsina: Jami’ar Umar

    Musa Ƴaraduwa.

Bakura, A. R da Wasu (2019) " Muhallin Zogala a Magungunan Gargajiya

    na Hausa Gusau: Gamzaki Printing Press.

Bunza, A. M. (2020)." Kwartanci: Fashin Baƙinsa, Mafarinsa da

    Nau'insa a Ma'aunin Al'ada da Adabin Bahaushe" Takardar da aka

   Gabatar a Taron Ƙarawa Juna sani na Zangon karatu na farko a

   Shekarar 2020 a Sashen Nazarin Harsuna da Al'adu, Tsangayar Fasaha,

   Gusau: Jami'ar Tarayya.

Bunza, A. M.(2006)."Gadon Fede Al'ada". Lagos: Tiwal Nigeria Limited.

 

Bunza, A. M (2017). "Dabarun Bincike :A Nazarin Harshe Da Adabi Da

    Al'adun Hausawa".Zaria: Ahmadu Bello University Press Limited.

CNHN (2006). "Ƙamusan Hausa na Jami'ar Bayero" Kano: Ahmadu

    Bello University press.

Ɗangambo, A. (1984) “Rabe-Raben Adabin Hausa Da Muhimmancinsa

   Ga Rayuwar Hausawa Kano: Triumph Publishing Company.  

 

 Garba, S. A. (2017). "Nazarin Shirye-shirye a Kan Magani da Kiwon

    Lafiya a Wasu Gidajen Rediyo" Lead paper presented at the

   Intentional Conference On Hausa Traditional Medicine, Center for

   Research in Nigerian Languages, Translation & Folklore, Vol xxvii.

   Kano: Bayero University.

Gusau, S.M (2008) “ Dabarun Nazarin Adabin Hausa” Kano: Benchmark

   Publishers Ltd.

Imam, A. H. (2017). "Kanwa Uwar Gami: Tsokaci akan Kanwa Wajen

   Haɗa Maganin Gargajiya" Lead paper presented at the Intentional

   Conference On Hausa Traditional Medicine, Center for Research in

   Nigerian Languages,Translation & Folklore, Vol xxvii. Kano: Bayero

   University.

Jinju, H. M. (1990). "Maganin Gargajiya na Afirka Tare da Mai Da Ƙarfi a

    Kan Nazarin Itatuwan Magani na Hausa" (da Waraka). Zaria:

    Gaskiya Corporation Limited.

Karofi, I. A Da Aliyu, L. (2018) “Itatuwa Masu Guba a Ƙasar Katsina” Kadaura

    Journal Of Hausa Multi Disciplinary Studies. Kaduna: State university Vol. 1,

    No 4. Pp 167-182

Maimuna, M. K. (2013) “ Rashin Sani Kaza ta Kwana a Kan Dami: Tsokaci a kan

   Tsirrai da Itatuwan Ƙasar Hausa”, a Cikin Tabarbarewar Al’adun Hausawa, The

    Deterioration of Hausa Culture. Katsina: Organized by Katsina State History and

    Culture Bereau in Collaboration with Umaru Musa Yar’adua University. Pp 251

    -252

Megan, RND, L, D (2018). "Health and nutritional benefits of baobab".

    https://www.medicalnewstoday.com/articles/306445.php.

    retrieved on 13/2/2020

Sadik, T. G. (2019)."Binciken Tarihin Hausa:Labaran da Bishiyoyin kuka

    ke Sanar Mana "https//aminiya.dailytrust.com.ng/binciken-tarihin

    hausa-labaran-da-bishiyoyin-kuka-ke-sanar-mana/ an ziyarci

  Wannan Shafin 13/02/2020.

Yusuf, Shuaibu. (2018). "Amfanin Miyar Kuka A Jikin Dan Adam."

 https://hausa.leadership.ng/2018/06/08/amfanin-miyar-kuka-a-jikin

 dan-adam/. an ziyarci wannan shafin 13/02/2020.

 

 

 

MUTANEN DA AKA YI HIRA DA SU

 

Baba Lula. Mai Shekara 63. An yi hira da shi Ranar Asabar 22 ga Watan

   Maris 2020, a ƙofar Gidansa da ke Awala, Tudun Wada Gusau. Da

   ƙarfe 5:30 na Yamma.

Gwagwo Nasara. Mai Shekara 69. An yi hira da ita Ranar Lahadi 01 ga

   Watan Maris, 2020, a Gidanta da ke Zurmi. Da ƙarfe 5 na Yamma.

Hamisu Muhammad. Mai shekara 32. An yi hira da shi a Wayar Salula,

   Ranar Alhamis 27 ga Watan Fabreru, 2020.

Mama Hajo. Mai Shekara 61. An yi hira da ita a Gidanta da ke Awala

   Gusau Ranar Alhamis 20 ga Watan Maris 2020, da ƙarfe 8 na Dare.

Mati. Mai Shekara 70. An yi hira da shi a ƙofar Gidansa da ke Shiyar gora

  Zurmi. Ranar 02/01/2020, da ƙarfe 5 na Yamma.



[1]Kamar yadda jaridar Aminiya ta wallafa a shafinta na yanar gizo.

[2]Domin ƙarin bayani a duba jaridar Aminiya a shafinta na yanar gizo.

[3]Sakamakon ƙarin bayani da na samu daga Dr. A. R Bakura

[4]Baba Mati ya bayyana man haka a lokacin da na ke hira da shi.

[5]Mama Hajo ita ta shaida man haka a lokacin da nake hira da ita.

[6]A duba Wikipedia, 2019.

[7]Gwaggo Nasara ta bayyana man haka a lokacin da na ke hira da ita a gidanta.

[8]Kamar yadda Baba Lula ya shaida man a lokacin da na ke tattaunawa da shi a ƙofar gidansa.

[9]Na samu waɗannan bayanan ne daga wurin Baba Lula wani dattijo mai sana'anar bada maganin gargajiya

[10]Baba Lula ne ya sanar dani haka a sakamakon hira da shi

[11]Hamisu Muhammad ya saida man haka a wata hira da na yi dashi ta waya

[12]Mama Hajo ta shaida man haka a lokacin da na ke hira da ita.

[13]Hakazalika shima wannan laƙanin na same shin ne a wurin Baba Lula.

[14]Shima wannan na same shi a wurin Hamisu Muhammaɗ.

[15]Baba Lula ya bayyana man haka a lokacin da nake hira da shi.

Post a Comment

0 Comments