Ticker

6/recent/ticker-posts

Neman Addu'ar Samun Mijin Aure

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum da ftn malam Yana lfy. Dan Allah malam ina so a taimaka min da wata addu'a Wanda Zan dinga yi dan na samu mijin aure. Allah ya jarabceni da jinkirin aure shi ne nake neman taimako na addu'a ko Zan samu mafita.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

Abu na farko da zanyi miki wasici dashi shi ne ki Ƙara haƙuri da juriya bisa wannan jarrabawar da Allah ya dora miki. Ki sani cewa akwai wasu da dama waɗanda musibar da suke ciki ta ninninka taki. Kuma ki sani cewa Allah bai manta dake ba. Yana sane dake da kuma halin da kike ciki. Kuma da sannu zai yaye miki damuwarki cikin falalarsa.

Ga wasu daga Sahihan addu'o'i nan ki rikesu ki rikayi. In Shã Allahu zaki ga biyan bukata cikin sauki:

1. Ayah ta 3-4 a cikin suratut Talaƙ:

وَمَن يَتَّقِ اللَّهَ يَجْعَل لَّهُ مَخْرَجاً -وَيَرْزُقْهُ مِنْ حَيْثُ لَا يَحْتَسِبُ وَمَن يَتَوَكَّلْ عَلَى اللَّهِ فَهُوَ حَسْبُهُ إِنَّ اللَّهَ بَالِغُ أَمْرِهِ قَدْ جَعَلَ اللَّهُ لِكُلِّ شَيْءٍ قَدْراً

Yazo a cikin Musnad na Imamu Ahmad bn Hanbal, Hadisi daga Sayyiduna Abu Dharrin Al Gifariy (Allah ya yarda dashi) yace "Manzon Allah ﷺ bai gushe ba, yana karanta mun wannan ayar, sannan yace "YA ABA DHARRIN, DA ACHE DUKKAN MUTANE ZA SUYI RUKO DA WANNAN AYAR DA TA ISHESU".

(Aduba Musnadu Ahmad juzu'i na 5 shafi na 178).

Don haka ki rike wannan ayar ki rika yin wuridinta da kyakkyawar niyyah. In Shã Allahu zaki samu biyan bukata cikin sauki.

Bayan wannan akwai yawaita istighfari. Hadisi ya inganta daga Muhammad dan Aliyu dan Abbas ya karbo daga babansa, daga Ka kansa Sayyiduna Abdullahi dan Abbas (Allah ya yarda dasu) yace Manzon Allah ﷺ ya ce:

"DUK WANDA YA YAWAITA ISTIGHFARI, ALLAH ZAI SANYA MASA YAYEWA DAGA KOWACCE DAMUWA, DA MAFITA DAGA KOWANNE TSANANI, KUMA ZAI AZURTASHI TA INDA DUK BA YA TSAMMANI".

(Musnadu Ahmad juzu'i na 1 shafi na 248).

Ki yawaita sadaƙah domin itama hanya ce ta samun yayewar tsanani da kuma biyan bukatu. Sannan shima istighfarin ki rika yin daruruwa ko dubunnai a kullum.

Hakanan ki yawaita salati bisa Shugabanmu Annabi Muhammadu ﷺ. Shima babbar hanya ce ta samun biyan bukatu da yayewar damuwa in Shã Allahu.

Ina rokon Allah Maɗaukakin Sarki ya biya miki bukatunki ya yaye miki damuwarki, kuma ya azurtaki da samun miji nagari wanda zai rikeki cikin mutunci.

WALLAHU A'ALAM.

Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

NEMAN ADDU'AR SAMUN MIJIN AURE

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum. Tambayata itace Don ALLAH wacce Addu'a zanyi domin samun miji nagari cikin karamin lokaci? Allah ya jarabceni da jinkirin aure shine nake neman taimako na addu'a ko Zan samu mafita.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salam warahmatullahi Wabarkatuh

A iya karamin ilimin mu bamu san wata keɓantaciyar addu'a ba wacce Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wa sallam) ya koyar a karanta domin samun Miji nagari ko Mata tagari. Sannan kuma bai halatta ga musulmi yayi addu'a yace yana son Allah ya biya masa da bukatarsa nan take, ko kuma a lokaci qayyadadde. Saboda Shi Allah ba'a sanya masa lokaci a biyan bukatar mai addu'a.

Amma mutum zai duqufa yana rokon Allah ya haɗa shi da mata tagari ko kuma mace Allah ya haɗa ta da Miji nagari.

Addu'a itace makami mai kaifi da mumini/mumina zai/zata yi amfani wajen yanke duk wata matsala dake a gabansu.

Akwai wasu lokuta idan bawa yayi addu'a Allah na karɓa masa kai tsaye. Misali kamar sulusin dare na karshe kamar yadda ya tabbata a hadisi.

Yana daga cikin sharaɗin addu'a musulmi ya kasance babu haram a cikinsa (baici abincin haram ko abin sha na haram ba), musulmi ya kasance bai yanke zumunta ba, ya kasance baiyi gaggawa ba, kuma ya kasance ya zaɓi kyakkyawan lokacin yin addu'a, sannan ya nisanci Neman gaggawar karɓawa.

Ya tabbata a hadisi cewa; An Karɓo daga Abu Hurayrah (R.A) Yace; Manzon Allah (sallallahu alaihi Wa sallam) Yace: (Allah) yana karɓawa ɗayanku (addu'arsa) matuqar baiyi gaggawa ba, (shine) yace nayi addu'a (amma har yanzu) ba'a amsamin ba. (Bukhari, 5865.  Muslim, 2735).

Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) Yace : "hakika ubangijinku mai kunya ne, mai karamci ne. yana jin kunyar bawansa yayin da ya cira hannayensa ya rokeshi, ace ya mayar dasu ba tare da komai ba".

An karbo hadisi daga Buraidata (r.a) ya ce: Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) ya ji wani mutum yana cewa:

اللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ بِأَنِّي أَشْهَدُ أَنَّكَ أَنْتَ اللَّهُ لاَ إِلَهَ إِلاَّ أَنْتَ الأَحَدُ الصَّمَدُ الَّذِي لَمْ يَلِدْ وَلَمْ يُولَدْ وَلَمْ يَكُنْ لَهُ كُفُوًا أَحَدٌ

MA'ANA: "Ya Allah hakika ina rokonka, na shaida kai ne Allah, babu abin bautawa da gaskiya sai kai, makaɗaici, madawwami, wanda ba ya haifuwa kuma ba a haife shi ba, kuma babu wanda ya kai shi."

sai manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) ya ce: “Lallai ka yi roƙo da sunan da Idan aka yi roƙo da shi ana bayarwa, kuma idan aka yi addu'a da shi ana amsawa". mutane huɗu suka ruwaito shi, Ibn Hibban ya inganta shi.

Wannan hadisin na nuna mana kenan ana saurin Amsa addu'ar Wanda ya yi amfani da waɗannan sunayen kenan.

Saboda haka 'yar uwa Idan za ki yi addu'a, sai ki fara ambaton waɗancan sunayen, sannan sai addu'ar ta biyo baya.

Don haka ki kyautata tunaninki. Hakika Allah ya riga ya amsa miki. Kawai lokacin ganin abun ne bai Qaraso ba. ki Qara hakuri da juriya bisa wannan jarrabawar da Allah ya dora miki. Ki sani cewa akwai wasu da dama waɗanda musibar da suke ciki ta ninninka taki. Kuma ki sani cewa Allah bai manta dake ba. Yana sane dake da kuma halin da kike ciki. Kuma da sannu zai yaye miki damuwarki cikin falalarsa. ki sani kowanne abu yana da lokacinsa wanda Ubangijiya riga ya Qaddara agareshi. Kuma abubuwa suna gudana ne bisa gwargwadon yadda Ubangiji Allah Ya Qaddara kuma yaso su faru.

Muna rokon Allah yabaki Miji nagari mai addini mai kaunarki, Wanda zai zamo farin-cikinki ya zama sanyin idonki. Ya Allah Matanmu marasa Maza, Allah kabasu Mazaje na gari masu addini. Mazanmu marasa Mata, Allah kabasu Mata nagari. Ka albarkaci al'ummar Musulmai a duk faɗin duniya. Ameen Ya Hayyu Ya Qayyum.🤲🏻

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu... 

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/J1hm5Tw12uYBƙfaiPwf28l

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments