Ticker

6/recent/ticker-posts

Saurayina Ya Ce Kada In Faɗa Wa Kowa Yana Da Sana'a, Ni Kuma Na Faɗa, Shin Na Ci Amana?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum, malam tambayata ita ce, wata ce saurayinta ya ba ta amana akan cewa yana aiki, sai ya ce mata kar ta sake ta fada wa kowa yana da aikin yi ɗin, ita kuma 'yan gidansu kullum sun nace mata saurayinta ba ya sana'a ba ya aikin komai, ita kuma ba ta jin daɗi, sai kawai ta faɗi maganar yana aiki, gashi kuma amana ya ba ta ita kuma gashi ta faɗa. To shin malam ta saɓa alkawari ne ko ta ci amanarsa ne? Domin an ce babu kyau saɓa alkawari sannan kuma ta ci amanane ko yaya ne saboda ta faɗa ne irin babu yadda za ta yi ne, ta gaji da zancen mutane akan saurayinta ba ya Sana'a sai zaman banza.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salam,

To ai baiwar Allah ai ba zai yiwu ‘yan uwan su bar ta, ta aure shi alhali ba shi da sana'a ba, ko kuma su aurar da ita ga wanda ba su san takamaiman sana'arsa ba, don haka suka matsa domin susan sana'ar tasa, wannan shi ne kawai a tunanina. Saboda Abuhurairata ya ruwaito cewa Annabi ﷺ ya ce: "Idan wanda kuka yarda da addininsa da ɗabi'unsa ya nemi aure a wurinku, to ku aurar masa...". Tirmizhiy 1084, Ibn Majah 1967.

Yana daga cikin ɗabi'un mutum kyawawa ya zama yana da sana'a, wannan na daga cikin abin da zai sa a ba mutum aure, idan kuma mutum ba shi da sana'a, hakan shi ma zai iya sa a hana shi aure. Saboda haka nake ganin wannan ba za a sa shi a cikin cin amana ko saɓa alƙawari ba, saboda ai dama dole ne sai an san sana'arsa kafin a ba shi aurenta idan za a bi ƙa'ida, saboda kada a ba mai zaman kashe wando mata ta yi ta rayuwa cikin ƙunci ta dalilin lalacin miji.

Allah ne mafi sani.

Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.🏻

Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/IerSx3AH0ZSJyHIuIYfƙds

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments