SHAIDAN YANA CIKIN MALA'IKU NE KO ALJANU?

     𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu alaikumus. da fatan Malam yana lafiya,.shin Shaiɗan yana cikin jinsin aljanu ne Ko Mala'iku kuma Dame Allah ya halacci mala'iku?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa'alaykumussalam, to ɗan'uwa malaman tafsiri sun yi saɓani game da haka zuwa maganganu guda biyu:

    1. Shaiɗan yana daga cikin mala'iku, saboda faɗin Allah a cikin suratul Bakara aya ta: 34, "Kuma ka ambata lokacin da muka ce da mala'iku su yiwa Annabi Adam (A.S) sujjada, sai suka yi sujjada, in ban da Iblisa da ya yi girman kai" toface Iblisa daga cikin waɗanda ba su yi sujjada ba, yana nuna cewa yana daga cikin mala'iku.

    2. Shaiɗan Aljani ne, saboda faɗin Allah maɗaukakin sarki "Kuma ka ambata lokacin da muka ce da mala'iku su yiwa Annabi Adam (A.S) sujjada, sai suka yi sujjada, in ban da Iblisa, wanda ya kasance daga cikin Aljanu ("Kahaf aya ta: 50) sai ayar ta bayyana cewa daga aljanu yake.

    Zance mafi inganci shi ne Shaiɗan aljani ne, saboda an halicce shi ne daga wuta, su kuwa mala'iku an halicce su ne daga haske, kamar yadda hadisin Muslim mai lamba ta: (2996) yake nuni zuwa hakan, sannan Shaiɗan yana da zuriyya, wacce take hayayyafa, mala'iku kuma ba sa haihuwa, wannan sai ya nuna ba daga cikinsu yake ba, Wannan yasa za'a ɗauki ayar suratul Bakara a matsayin tana nufin yana daga cikinsu ta fuskar zaman tare, amma ba ta fuskar halitta ba, sannan mala'iku ba sa saɓawa Allah, shi kuma Iblisa yana saɓawa Allah.

    Don neman Karin bayani duba: Tafsirin Ibnu-jarir 1/507 da Jami'u lada'if attafsir 1/278.

    Allah ne mafi sani.

    Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.

    Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah, ta fahimtar magabatan kwarai.

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi.

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

     

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.