Ticker

Shin Akwai Banbancin Tsakanin Sallar Mai Aure Da Gwauro?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Mene ne ban-bancin darajar sallar mai aure da wanda bashi da aure?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Aure yana tattare da falaloli da rajajoji masu tarin yawa waɗanda Alƙur'ani da Hadisai Ingantattu suka bayyana. A iya binkicenmu zuwa yanzu bamu samu wani nassi da yake nuni da fifita darajar Sallar Mai Aure da gwauro ba. Sallar Gwauro da ma gidanci Bata da wani ban-bancin daraja ko lada tsakaninsu. Wanda yafi iya sallah da kwatanta yinta yanda manzan Allah sallallahu Alaihi wasallam ya zo da ita, da yinta cikin jam'i a lokacinta shi ne abun dubawa wajan samun falala da darajar sallar mai gida da tuzuru.

Duk wanda yafi kiyayeta da cika sunnoninta da farillanta da mustahabbanta shi ne sallarsa zatafi daraja da falala... Aure ko rashinsa bashi ne ma'aunin gane darajar sallah ko rashinta ba.

Saboda haka Babu wani ban-banci daraja tsakanin Sallar Mai Aure da Gwauro. Wasu zantuka da kakeji ana cewa sallar Mai Aure tafi wanda bashi da Aure dara sau saba'in ko kaza da kaza, duk ƙare rayine da basu da tushe a cikin addinin musulunci. Yawanci Gafalallune suke yaɗasu, yawancinsu daka shafukan 'yan shi'a zindiƙai suke dakkowa su watsawa musulmi, saboda su dama ƙarya a cikin addininsu kamar kalmar shahadace a cikin Addinin Musulunci.

WALLAHU TA'AALA A'ALAMU.

Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/DIcJIƘrWyLP0oBOMSnDi5P

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments