Ticker

Shin Akwai Wata Kebantacciyar Addu’a Da Ake Wa Iyaye Da Suka Rasu?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalama alaikum, ina da tambaya kamar haka: Wace addu’a ake wa iyaye mamata a kowace sallah?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Ba wata katamaimiyar addu'a da aka ware aka ce dole ita ake so a yi wa iyaye mamata idan za a yi sallah, duk wata addu'a halastacciya da ake roƙon Allah da ita ga mamata za a iya yin ta da nufin Allah ya gafarta wa iyaye.

Ya tabbata a hadisin da Imamu Muslim ya ruwaito cewa; Aufu bin Malik ya ce: Annabi ﷺ ya yi wa wata gawa sallar jana'iza sai ya ji addu'ar da Annabi ﷺ yake yi ita ce:

اللهُمَّ اغْفِرْ لَهُ وَارْحَمْهُ، وَاعْفُ عَنْهُ وَعَافِهِ، وَأَكْرِمْ نُزُلَهُ، وَوَسِّعْ مُدْخَلَهُ، وَاغْسِلْهُ بِمَاءٍ وَثَلْجٍ وَبَرَدٍ، وَنَقِّهِ مِنَ الْخَطَايَا كَمَا يُنَقَّى الثَّوْبُ الْأَبْيَضُ مِنَ الدَّنَسِ، وَأَبْدِلْهُ دَارًا خَيْرًا مِنْ دَارِهِ، وَأَهْلًا خَيْرًا مِنْ أَهْلِهِ، وَزَوْجًا خَيْرًا مِنْ زَوْجِهِ، وَقِهِ فِتْنَةَ الْقَبْرِ وَعَذَابَ النَّارِ.

Ma'ana:

Ya Allah ka gafarta masa, ka yi masa rahama, ka kiyaye shi, ka yafe masa, ka karrama masaukinsa, ka yalwata mashigarsa, ka wanke shi da ruwa, da ruwan ƙanƙara, da ruwan sanyi, ka tsaftace shi daga kurakurai, kamar yadda ake tsaftace farin tufafi daga datti, ka canja masa wani gida da ya fi gidansa, da iyalan da suka fi iyalansa, da matar da ta fi matarsa, ka shigar da shi Aljannah, ka tsare shi daga azabar ƙabari, da azabar wuta.

Muslim 963.

Wannan addu'a ta kasance Manzon Allah ﷺ yana yi wa mamaci idan ya zo yi masa sallar jana'iza. Don haka ya halasta a ci gaba da yi wa mamaci wannan addu'ar da makamantanta ko da bayan yi wa mamaci Sallah ne.

Allah ne mafi sani.

Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.

Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/GUƙ2GCCzlcdL6nknƙLYYox

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments