Ticker

SHIN ƊALIBIN DA YAJE WATA KASA KARATU ZAI IYA YIN KARASU..?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalam alaika warahamatullah wabrakatuhu Dr don Allah mene hukuncin dalibai masu zuwa wata kasa karatu shin zasu iya kasaru a can ?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wassslam alaika warahamatullah wabrakatuhu.

 Mu rike akida a musulunci hakika asalin kasaru mutum yana yin tane a garin da bazai jima cikinsa ba kokuma bazai ɗauki kwanaki a cikinsa ba misali Wanda yaje daurin aure ko kasuwanci da sauransu

Amma duk garin da yake mutum idan yaje zai dade cikinsa ma’ana  abin da ya kaisa zai dauki lokaci mai tsawo misali dalibin da yaje karatu zaiyi degree a wata kasa zai dauki shekara huɗu to anan bai halatta ya yi kasaru ba ya kamata dalibai masu karatu a wata kasa su kiyaye wannan ka’ida lokacin da yake karatu kasar domin shari’a ta ware adadin kwanakin da mutum zai iya yin kasaru idan ya tsinci kansa a wani gari

Amma idan ya yaje garinsu hutu ko kasarsu babu laifi zai iya yin tunda bazai dade ba zai koma karatunsa wannan shi ne zance mafi inganci daga malamai.

Allah shi ne sani 

Amsawa:

DR ABDALLAH GADON ƘAYA.

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah, ta fahimtar magabatan kwarai.

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments