𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Wai
Dagaskene Aljani Yana Auren Mace, Idan Ya Aureta Hakan Yana Nufin Ba Ita Ba
Aure Har Mutuwa? Wadanne Alamomine Suke Tabbatar Da Aljani Ya Auri Mace?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
الحمد لله.
Tabbas
dalilai daka alƙur'ani da sunnah sun tabbatar da aljani yana shiga jikin Ɗan
Adam mace kona miji, sannan kuma hakika akwai wani nau'in aljani dayake auren
mace ko namiji ba tare da mutum yasani ba.
Amma ba
gaskiya bane cewa inya auri mace ba ita ba aure har mutuwa, na'am yana kawowa
mace ko namiji matsala wajan yin aure akan kari, ko kuma rabuwa bayan anyi
auren, yana shafar budurwa damai aure mace ko namiji.
Dalilan
Dasuke Saka Aljani Auren Mace Ko Namiji
Shaikul
Islam ibnu taimiyyah rahimahullah a cikin maj'mu'u fatawa ɗinsa ya ce:
Daka cikin
dalilan dasuke sa aljani ya auri mutum sune, so, ko sha'awa, ko tsoratar da
mutu.
Jinsin
wannan aljani na jinsin mata suna shiga jikin mace cikin mutane tana cutar da
ita da ta'addanci tana suranta mata cikin bacci kamar tana madigo da
'yar'uwarta mace, ko abokiyarta, kota dinga jin sha'awar 'yan'uwanta mata da
haka hartaji tana san mace 'yar'uwarta so na sha'awa.
Haka aljani
na miji yanaiwa mutum irin wanann illar har mutum yatasirantu dahakan ya auka
cikin liwadi,
DALILAN
DAKESA ALJANI YASAMU NASARAR SHIGA JIKIN MUTUM HARYA AURESHI.
Daka cikinsu
shi ne idan mutum yaburge aljani wannan zaisa aljani yaita bibiyar mutum wajan
wasanni da guraren kazanta ko shiga banɗaki koyin fitsari a gidan tururuwa, ko
wajan saduwa, ko mace tadunga shigar bayyana tsiraici kirjinta da guraren
shawarta duk abayyane, har aljani yaga yasamu wata kofar shiga jikin mutum.
- Kambun
baka ko hassada, maikarfi, daka aljani ko mutum, suna sanya aljani yasamu damar
shiga jikin mutum.
-Yiwa mutum
sihiri, wani yaiwa mutum sihiri, Musamman idan aljani da bokan yawakilta
namijine jikin mace, ko mace ajikin namiji, wannan shi ne galibin abun da yafi
faruwa. Wanann nau'in yakasu kashi kashi
Akwai shirin
alfasha aiwa mutum sihiri dan adunga alfasha dashi.
ko Sihirin
soyayya, shima kashi-kashi ne akwai wanda za a kashewa mutum sha'awa ko tada masa
sha'awa.
Wakilta
mazinacin aljani gawanda akaiwa shihirin yadinga alfasha dashi dare da rana.
-Wakilta
aljani bayahude ko kirista ga wanda akaiwa sihirin, musulmi.
- Aljanin
yaiwa mutum sihiri danya dunga saduwa dashi.
- Nisantar
Allah, da wulaƙanta salloli koƙin yinsu, da dulmiya cikin abubuwan da aka
haramta, wannan yakan yiwa aljani saukin shiga jikin mutum.
- idan mutum
da kansa yanemi mu'amala da aljani wato ya zama boka.
-karanta
litattafan bokanci da mu'amala dasu.
Irin wannan
aljani idan yashiga jikin mutum mai yakeyi
Wannan
nau'in aljani yana iya yin komai ajikin mutum, tadowa da mutum wutar sha'awa,
kawatawa mutum alfasha dason zina, da kalle kallen maza, in macece da kalle
kallen mata, inna mjine Hakan zaidunga faruwa ga mutum cikin kutse ba tare daya
so hakan ba.
harkisa
aljanin yanayi yadanganta da yanayin aljanin kafiri ko musulmi, wani zakaga
musulmine yanasa mutum aikin ɗa'a dabin Allah, aljanin yana taimaka masa wajan
san aikin alkhairi, amma tare dahakan shi aljanin yana biyan bukatarsa ajikin
wanda yashigeshin, yana iya kasancewa kuma kafiri yadinga yiwa mutum makirci,
cikin ibadarsa, aljanin dayake jima'i damace yana iya yin komai wanda mutum
zaiji alamun yana yare da Shaiɗanin aljani.
ALAMOMIN
DA'AKE GANE MUTUM YANA TARE DA NAU'IN WANANN ALJANI
1- Yawan mafarki,
amma mafarkin wanda yadanganci ganin namiji tsirara, ko ganin mace tsirara, ko
jima'i da muharrami damakamantansu.
2- Jin
sha'awa ba tare da wani dalili ba, kojin sha'awar muharrami, basaida Mai aure
ba kawai.
3- Ƙin miji
darashin sha'awarsa, in budurwace taji kwata kwata bata sha'awar namiji.
4- Jin kamar
ana jima'i damace ko ana mata wasa da farji kojin motsi afarjin, motsin maitada
sha'awane ko kawai motsin takeji, ko jin motsin jima'i.
6- jin kamar
wani yana biye dakai abayanka inkana tafiya kojin kamar wanine abayanka kuke
bacci tare dashi. Kojin kamar wanine kusa dake akan gado yake numfashi.
7- Namiji
yadunga jin mace tare dashi, ko cikin wandansa, koyajita cikin al'aurarsa.
8- Wasu
matan za su dunga ganin namji tsirara a nau'ika kala-kala, kuma yana saduwa da ita,
a cikin barci ko ido abude.
9- Miji
yadinga gujewa matarsa yadunga bacci nesa da ita, gabansa yadunga faduwa idan
takusanceshi, dasan zama shi kaɗai, sai ya shafe watanni masu yawa bai sadu da
matarsa ba.
10- Mata
tadinga gudun mijinta kuma tana yawan fitar ruwa daka farjinta, da kiyayya
dagadar da matsaloli da nauyin jiki, mace taji batasan ko shafa jikinta mijinta
yayi, watama hatta 'ya'yanta bataso su tabata, dasan zama ita kaɗai, dakwanciya
kamar tsirara tsirara, da dogon bacci nalokaci maitsawo.
11-Rashi ko
raunin gabobi ko saurin kawowa yayin jima'i, dajin ciwo karkashin cibiya, da
yatsu kamar suka daciwo da budewar dubura, dajin wani abu a cikinta.
12- Rashin
bacci da daddare, dazama lokaci maitsawo a cikin banɗaki, ko tirken dabobi
kozama wajan zub da shara.
13- Jin
kamshin turare a ɗaki ba tare da sanin daka ina kamshin yake tasowa ba.
14- Yayin
jima'i tadunga jin wanda yake jima'in nan da ita ba mijinta bane, ko bayan gama
jima'i taji wani yana jima'i da ita wanda ba mijinta bane.
15-Wasu yara
za su dunga bijirowa mutum yafarka yaga kayansa antube masa, yadunga hakaito
wani abu na jima'i wanda baisan ma'anarsa ba,
16- Jin
sha'awa mai tsanani dakarkatuwa zuwa luwadi ko madigo,.
17- Budurwa
tadunga kuka idan wani ya zo neman Aurenta, ko saurayi yaguji budurwa bayan sun
yi yarjejeniyar aure, da wasu uzurori waɗanda ba karɓaɓɓu ba, ko kuma inyatafi ba
zai sake dawowaba, tare dacewa mace tanada dukkan abun da ake son mace nakyawu
da kamala.
18- Mutum
yai iya yinsa amma kememe matarsa taƙi yarda dashi, yai aure yasaki, ko taki yarda
dashi saidai araba aurensu,
19- Namiji
yaji baya iya kallan mata, yakanji radadi ma idan yai magana da mace, ko gumi
yadunga keto masa, wasu suna ɗaukar hakan kamar kunyace, na'am akwai nakunya
akwai kuma na aljani, koya dunga jin motsi ajikinsa.
19- jin ciwo
al'aura da bayansa, dajin tafiyar wani abu kaman kiyashi ko da yaushe,
20- Jin ciwo
a azzakari ko makwallato, ko mahaifa, ko wajan bahaya.
21- Daka
cikin abubuwanda da'ake gane Aljanin dayake auren mutum shi ne karanta ayoyinda
dasuke zargin zina ko alfasha su kaɗai, yayin yiwa mara lafiyar/mara lafiyan ruƙya,
Suna tasiri akan aljanin, ko da aljanin yana cikin nau'in aljanu masu tashi
kamar tsuntsaye zai bayyana.
za mu dakata
anan in Shã Allahu za mu karasa kawo cikwan bayanin, munkuma tsawaita dan kada
mutakaita kuma adamemu da tambayoyi da suka shafi wannan janibin mukuma bashi
ne aikin muba.
🖊 Tambaya da Amsa Abisa fahimtar magabata Nakwarai.
Ga Masu Buƙatar
Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄��𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.