Shin Ana Shawo Halayen Mahaifiya Ta Nono?

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu Alaikum malam. Barka da yini don Allah Ina tambaya shin da gaske ne yaro yana ɗauko halin mahaifiyarsa mai kyau ko mummuna ta dalilin Shayarwa da ta yi masa?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa'alaikumus Salám, ‘yar uwa a iya abin da na sani babu inda ya tabbata a Alƙur'ani ko a ingantaccen hadisin Manzon Allah ﷺ cewa yaro yana ɗauko halin mahaifiyarsa mai kyau ko mummuna ta dalilin shayarwar da ta yi masa. Sai dai abu ne sananne a cikin mutane yaro yana iya koyon ɗabi'ar da ya taso ya sami iyayensa a kai, saboda su ne makarantarsa ta farko a rayuwa.

    Manzon Allah ﷺ ya ce:"Kowane abin haihuwa ana haifansa ne a kan daidaitacciyar ɗabi'a, sai iyayensa su mayar da shi Bayahude, ko Banasare, ko Bamajushe".

    Albukhariy (1385), Muslim (2658).

    Wannan na nufin duk wani abin haihuwa ana haifansa ne a kan kyakkyawar ɗabi'a, amma iyayensa ne sukan canja masa ɗabi'ar ta hanyar koyarwarsu, ya zama ya tashi da ɗabi'a maras kyau. Wato kenan ba a nono yaro yake shawowa ba, inda ana shawo ɗabi'a a nono, to da zai zama yaro zai shawo addininsa a nonon uwarsa kenan.

    Allah S.W.T ne mafi sanin daidai.

    Jamilu Ibrahim, Zaria.

    Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/J1hm5Tw12uYBƙfaiPwf28l

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.