Shin Ruwan Nonon Mace Najasa Ce?

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Malam inada tambaya Ance in nono ya taɓa Kaya, kayan ba zai yi sallah ba, to macenda take shayarwa Kuma ruwan nono yana zubamata dayawa har Yana Ɓata mata kaya. Shin duk lolacinda za ta yi sallah zata wanke jikinta ta canja Kaya? Koko yaya za ta yi?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    To baiwar Allah shi ɗan Adam babu yadda za'ayi ace da najasa ake shayar dashi kuma na san babu wanda zai yadda cewa da janasa ake shayar da yaro to yanzu don Allah ta yaya za a ce muku shi ruwan nonon najasa ne? Sabida haka shi nono Abinci ne halattacce Da Allah maɗaukakin sarki Ya samar dashi daga jikin mace domin shayar da ɗanta kunga kuma tayaya za'ace idan abinci ya taɓa tufafi ba zai yi sallah ba? Sabida haka waccan maganar kawai karyace domin bata da asali Babu wani nassi ingantacce da yace matar da take shayarwa idan nonon ya zuba a tufafinta tufafin ba zai yi sallah ba Wannan kawai tatsuniyace. kai ko da tunbuɗin da yara ke yi ba najasa bane zubar sa a tufafi baya hana sallah balle kuma shi ruwan nonon kan sa Sabida haka dukkansu tsarkakakku ne basa hana sallah kuma ko da ya zuba a tufafi babu laifi ta yi sallarta da kayan idan kuma taso sai ta wanke Amma dai wankewar ba dole bane.

    Amma su waɗanda suka ce najasane to kuce dasu su zo muku da hujja su ɗin idan sun kasance suna da gaskiya

    WALLAHU A'ALAMU

    Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

    𝐖𝐇��𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/BSA30hdZD7V3WSJF8WVwUj

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.