Shin Wacce Addu'a Ce Ta Dace Mai Ciki Ta Riƙa Yi?

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu alaikum malam, da fatan kana lafiya, dan Allah wace addu'a mai ciki za ta riƙa yi dan fatan Allah ya sauke ta lafiya, kuma Allah ya kawo haihuwa cikin sauki?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa'alaikumus Salam. ‘Yar uwa babu wata keɓantacciyar addu'a da na sani da ta tabbata daga manzon Allah ﷺ cewa ita ce mai ciki za ta riƙa yi, sai dai Annabi ﷺ ya koyar da addu'o'i da suka ƙunshi neman yaye duk wata damuwa, da cuta da ke damun ɗan'adam, daga cikin waɗananan addu'o'i akwai addu'ar da Annabi ﷺ ya koya wa Usman ɗan Abu Áss a lokacin da ya kai masa koken wani ciwo da ke damunsa a jikinsa tun lokacin da ya Musulunta, sai Annabi ﷺ ya ce masa ya sanya hannunsa a daidai inda yake masa raɗaɗi a jikin nasa, sannan kuma ya yi Bismillah sau uku, sannan sai ya karanta wannan addu'ar sau bakwai

    أَعُوذُ بِاللهِ وَقُدْرَتِهِ مِنْ شَرِّ مَا أَجِدُ وَأُحَاذِرُ .

    A'UZHU BILLAHI, WA ƘUDRATIHI MIN SHARRI MA AJIDU WA UHÁZHIRU”.

    Ma'ana:

     Ina neman tsarin Allah da ikonsa daga sharrin abin da nake ji (a jikina), kuma nake tsoro. Muslim 2202.

    Bayan wannan za ki iya haɗawa da "Hasbiyallahu Wa Ni'imal Wakeel", da Fatiha da sauran duk addu'o''in da za ki iya da Hausa ko da Larabci a kan Allah ya sauke ki lafiya, in Allah ya so za ki ga ikon Allah, da taimakonsa, kuma kina iya maimaitawa lokaci bayan lokaci.

    Allah ne mafi sani.

    Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.

    Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/Fc3hX6HoDt65aKhhKOiDpX

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.