Ticker

Shin Ya Halasta In Naƙalto Ibadata Daga Mafarki?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum, Allah ya gafarta malam, wata rana ina bacci sai na yi mafalki, a cikin mafalkin sai na ji an ce min kullum in safiya ta waye kafin na ci komi, na dinga karanta bisimillah sau 7 ina tofawa a ruwa in sha, to ni kuma da na tashi sai na dinga yin hakan, to malam ya halatta na ci gaba ko na daina.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salam, ‘yar uwa karanta Bisimillah abu ne mai kyau kamar yadda duk Musulmi ya sani, amma inda matsalar take shi ne: Idan aka buɗe kofar naƙalto ayyukan addini ko ibada ta hanyar mafarki, to hakan zai iya kawo ma addini rikicewar al'amura, saboda ai ba a san wane ne yake ba da wannan umurnin ba, wata ƙila Shaiɗan ne yake neman da haka ya kai ki zuwa aikata abubuwan da ba su dace ba da sunan addini, saboda ba ta inda Shaiɗan ba ya ɓullowa mutum don ya ga ya halaƙar da shi, wani lokacin ta hanyar wata ibada yake ɓullowa mutum.

Saboda haka kawai ki daina yin wannan aikin da ba ki san wane ne ya ba ki umurni ba, ki dage da riƙon zikirin da Annabi ﷺ yake yi safiya da yammaci, da sauran zikirorinsa, lallai idan kika riƙe wannan na Manzon Allah ﷺ ɗin muna da yaƙinin za ki sami dacewa fiye da wanda ba a san haƙiƙanin wane ne ya ba da umurnin ba.

Sannan kuma yana da muhimmanci a riƙa karyawa da dabino guda bakwai kafin a ci komai a kowace safiya idan an sami dama, kamar yadda Annabi ﷺ ya tabbatar cewa duk wanda ya yi hakan wata cuta ta dafi ko sihiri ba za ta same shi ba. Amma a ruwayar hadisin Muslim an ce dabinon Madina ne, kawai dai idan ba a sami ta Madinan ba a yi amfani da wadda ake da ita.

Bukhariy 5445. Muslim 2047.

Allah ne mafi sani.

Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.

Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/JLojawdOWYsEOeSHZMNdjf

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments