𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Malam na
kanji wasu mutane na fadar cewa ba ya halatta idan matar mutum tana da juna
biyu ya yi jima'i da ita har sai ta haihu meye gaskiyar maganar?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
To ɗan'uwa
ya halatta a sadu da mace lokacin da take da ciki, saboda fadin Annabi tsira da
amincin Allah su tabbata a gare shi : "Duk wanda ya yi imani da Allah da
ranar lahira, to kada ya shayar da ruwansa ga shukar waninsa" Abu-dawud :
1847
Ibnul kayim
yana cewa : "Wannan hadisi yana nuna cewa ciki yana kara karfi duk lokacin
da ake saduwa, saboda Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya
kamanta shi da shuka, ita kuma shuka tana kara girma, idan aka ba ta ruwa"
Tahzibussunan 1\193 .
Masana
likitanci suna cewa: ba a so miji ya dinga hawa kan matarsa lokacin da take da
ciki, zai fi kyau ta dinga yin goho yayin da za su sadu, ko kuma ya sadu da ita
ta gefe, saboda kwanciya a kanta yana iya wahalar da yaron .
Sannan
yawanci mata basu cika son yawan saduwa ba idan cikinsu ya girma, wasu
likitocin suna ba da shawara cewa a karanta saduwa a waɗannan lokutan.
Allah ne ma
fi sani .
Jamilu Yusuf
Zarewa
Ga Masu Buƙatar
Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/Du5LNx31U9hDi6RƘbbrzgW
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.