Ticker

Shin Ya Halatta Wanda Kaje Baƙunta Wajansa Ya baka Gadon Matarsa Ka Kwana A kai?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Shin Ya Halatta Wanda Kaje Baƙunta Wajansa Ya baka Gadon Matarsa Ka Kwana A kai?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

الحمد لله.

Babu kokwanto dakin kwanan ma'aurata kebantacce ne na musamman, shi ne suturar mace, shi ne tsaronta wanda yake tsaronta a cikin gidanta, tana cire kayanta a cikinsa, tana kebewa da mijinta, yana cikin gurarenda datake aikata abun da bazata iya aikatawa awaninsa ba, cikinsa akwai kayan mijinta kebantattu, dakayan adonta datake ado dashi, dakuma Abun da yake da Alaƙa da kwanciyar Aure da mijinta, wanda bai kamata wani yaleka shiba, wannan Abun da muka Ambata shi ne asali bai halatta saɓa wannan ba.

Saidai ana samun wasu uzurori dasuke sanya sakarwa makusanci wata 'yar dama ta shiga wannan wajan, imma saboda ƙuntatuwar gida, Kodai Saboda Ƙuntatuwar ɗaki, Ko saboda bukatar Amfani da ɗakin baccin mata, saboda yafi sauran dakunan sutura, ko Wanin haka cikin Dalilai, saidai wannan damar tazama tacika waɗannan sharudda...

@- Bukata Mai tsanani akan hakan.

@- Rashin bayyana kebantattum tufafin Miji da mata, da dukkan Abun da Akejin kunyar bayyanarsa.

@- Wanda zakaiwa Sassaucin shiga ɗakin Matarka ya zama Aminctacce, wanda baka tsoran zai bincike akan kebantattun Abubuwam dake ɗakin, ko kai labarin ɗakin ga wani.

@- Iznin Mijin ko mata.

Wajibi ne abi umarnin kin yardar miji/mata, dakuma rashin saɓawa ɗayan wajan aje bako ya kwana ashimfir miji ko mata.

Bai kamata miji yashigar da kowa dakin Matarsaba, idan batasan hakan, sai idan takura tasa dole saika shigar da wani, ya kasance Wanda zaka shigar din Amintaccene, kamar Babarka ko ɗan'uwanka, dasauransu, wajibi ne ka tausasawa matarka kafaranta mata rai akan hakan.

Muslim Yaruwaito hadisi (1218) daka Jabir Bin Abdullahi Allah yakara musu yarda ya ce: (Kuji tsoran Allah Akan mata, domin kun karbesu da Amanar Allah, kun samu halaccin farjinsu da kalmar Allah, kunada haƙƙin kada su zaunar dawanda bakwaso akan shimfidarku, idan suka aikata hakan, kudakesu duka bamai raunata jikiba.

Ma'ana kada su girmama wanda miji bayaso da bashi shimfidarsa yakwanta akai, haka itama mace tana da Wannan haƙƙin kada ka kabaiwa wani gadon dakuke kwanciya da ita wanda bata so yakwana akai..

Sharhin Riyazul Saliheena (3/126).

Abun da Wasu suke ƙudurcewa cewa idan Wani yai bacci akan shimfidar miji, wai hakan yana haifar da Matsalolin Aure, wannan aƙidar jahiliyyah ce, dakuma canfi wanda ya kamata musulmi sukubuta daka gareshi, babu Abun da yake karfafa wannan Ashari'a, ko wani waƙi'i dayake gaskata hakan.

Saboda haka Sam bai dace kabaiwa bakonka dakin Matarka ko gadon matarka yakwana akaiba dasunan karramawa.

Sam Wannan baya daka cikin Karrama bako, yana daka cikin Abubuwanda suke zub da mutunci danuna rashin kishi ga Matarka dan haka dai badace ba, bai kamata ba.

WALLAHU A'ALAMU.

🖊 Tambaya da Amsa Abisa fahimtar magabata Nakwarai.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/Fb6ƙgYPXfEeHb8CD1SWAkK

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments