Ticker

    Loading......

Shin Ya Halatta A Yi Karatun Qur’ani Don Neman Biyan Buata?

Karatun Alƙur'ani, Saboda Neman Biyan Bukatu ! !

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum, Malam ya halatta mu taru muyi karatun Alƙur'ani don Allah ya kawo mana sauƙi kan matsaloli daban daban?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikum assalam, Ya halatta a karanta Alƙur'ani a yi tawassuli da shi wajan tunkude bala'o'i, saboda shi karatun aiki ne nagari, kuma aiyuka nagartattu ana iya tsani da su wajan neman biyan bukatu kamar yadda hadisai suka tabbatar.

Anas Dan Malik daga cikin sahabban Annabi ﷺ ya kasance yana tara iyalansa ya yi addu'a Idan ya kammala karatun Alƙura'ni, wannan sai ya nuna babu laifi yin hakan, saboda aikin sahabi hujja ne, in ba a samu wani sahabin ya saɓa masa ba.

 Don neman Karin bayani duba Fataawa Arkanil Al-Al-Islam Na Ibnu Uthaimin: 354.

 Allah mafi sani.

DR. JAMILU YUSUF ZAREWA

Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/FBuwMyVjc2sGOEGLm0W7ed

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments