SHIN YA HALATTA YIN LAYYA DA DABBAR DA AKA YANKEWA JELA DA KUNNE?

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Shin ya halatta yin layya da dabbar da aka yankewa jela da kunne?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    الحمد لله

    Dole ne mutum ya ban-bance tsakanin dabbar da aka yankewa jela da wacce aka yankewa kunne., Yanke jela baya tasiri wajan layya da dabba, Saɓanin Wacce aka yankewa Kunne abisa Zance na Malmai mai rinjaye.

    Ibnu Ƙudama ya ce: Dabbar da aka yankewa jela ta wadatar wajan layya, halittar tace haka, ko yanketa aka yi, Domin tawaya ce da ba ta tasiri a nama, kuma ba ta kawo cikas wajan manufar layya, kuma ba'a ruwaito hani akai ba.

    Al-Mugni (13/372).

    Ya ce: Wacce aka yankewa wata gaɓa, ba ta Isarwa wajan layya, kamar mai yankakken kunne.

    Al-mugni (13/371).

    Kamar Yanda Shaik Usaimeen ya fada acikin Sharhin Mumti'i (7/435).

    Da Jilsatul Hajji shadi na (108)

    WALLAHU A'ALAM.

    Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah, ta fahimtar magabatan kwarai.

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi.

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.