𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaykum Don Allah Dr, shin ya Halatta ace an yi duniya don Manzon Allah (s.a.w)?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikum assalam, Ba'a yi mutanan duniya don Manzon Allah ﷺ ba, an yi mutanan duniya ne don su bautawa Allah.
Allah maɗaukakin sarki yana cewa a cikin suratu Azzariyat aya ta (56) "Ban halicci mutum da Aljan ba sai dan su bauta min, bana bukatar wani arziki a wajansu kuma bana bukatar su azurta ni"
Ayar da ta gabata ta bayyana dalilin da yasa Allah ya halicci mutane da Aljanu, wato bautawa Allah da kuma tsayar da tauhidi.
Babu wani nassi ingantacce yankakke wanda ya nuna an yi duniya saboda Manzon Allah ﷺ hakan kuma ba ya nuna an tauye manzon tsira.
Annabi ﷺ bawa ne daga cikin bayin Allah kamar yadda tarin ayoyin Al'ƙur'ani suka tabbatar da hakan, sannan shugaban 'ya'yan Annabi Adam kamar yadda ya tabbata a hadisai ingantattu a kundayan musulunci.
Ajjiye shi a matsayinsa da Allah ya ajjiye shi, shi ne daidai kamar yadda yake cewa "Kada ku wuce gona-da-iri wajan yabona kamar yadda nasara suka wuce a lamarin Isa ɗan Maryam"
Allah ne mafi sani
Dr. Jamilu Zarewa
Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah, ta fahimtar magabatan kwarai.
Shin Allah Ya Halicci Duniya Domin Manzon Allah ﷺ Ne?
𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum, shin wai da gaske ne cewa Allah (ﷻ) Ya halicci duniya ne
da dukkan komai domin Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam)?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumus Salam Warahmatullahi Wabarkatuhu.
Hakika wannan magana ta daɗe
tana yawo a bayan ƙasa, kuma ko shakka babu kan cewa Manzon Allah (Sallallahu
alaihi Wasallam) shine mafi daraja, da ƙima, da matsayi, da ɗaukaka a cikin halittu gaba
ɗaya, kuma shine ya
kasance cikamakin dukkan Annabawa sannan kuma shugabansu, dan haka wajibi ne a
yi masa biyayya akan dukkan abinda yazo dashi. Hakika shiriya tana ga wanda ya
bishi, kuma taɓewa da ɓata suna ga wanda ya saɓa masa: domin duk wanda
yayi masa biyayya to Allah ya yiwa, haka nan duk wanda ya saɓa masa to ya saɓawa Allah ne, amma duk da
irin wannan matsayi na Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) hakan bai
cireshi daga matsayinsa na bawan Allah ba.
To amma dangane da cewa Allah(ﷻ)
ya halicci komai ne saboda Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) wannan ba
gaskiya ba ne, domin wannan maganar taci karo da nassosi na Alƙur'ani
da sunna, ko da yake akwai wani Hadisi kirkirarre na karya da akace wai Allah(ﷻ) yace da Annabi
(Sallallahu alaihi Wasallam)
لو لاك
ما خلقت الأفلاك
MA'ANA
Ba don kai ba (Annabi (Sallallahu alaihi Wasallam) to da
banyi halittu ba.
Ko shakka babu wannan hadisin karya ne, abinda yake
tabbatacce a shari'a shine, Allah(ﷻ)
ya halicci dukkan komai ne don saboda a bauta masa, da kuma nuna karfin ikonsa
da iliminsa akan komai, kamar yadda Allah(ﷻ)
Ya ce
اللَّهُ
الَّذِي خَلَقَ سَبْعَ سَمَاوَاتٍ وَمِنَ الْأَرْضِ مِثْلَهُنَّ يَتَنَزَّلُ الْأَمْرُ
بَيْنَهُنَّ لِتَعْلَمُوا أَنَّ اللَّهَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ………
Allah(ﷻ) shine wanda Ya
halicci sammai 7, daga ƙasa ma ya halicci misalinta, domin ku sani cewa Allah(ﷻ) shine mai iko akan
komai…… (suratul Ɗalaq Aya ta 12)
A wata ayar kuma Allah(ﷻ)
Ya ce
وَمَا
خَلَقْتُ الْجِنَّ وَالأِنْسَ إِلاَّ لِيَعْبُدُونِ
Ban halicci jinsin aljanu da jinsin mutane ba sai dan su
bauta min. (Suratul zâriyat aya ta 56)
Hakika Allah(ﷻ)
ya faɗi dalilin da
yasa yayi halittunsa, dan haka tabbatacciyar magana itace, Allah(ﷻ) bai halicci duniya
saboda wani bawa daga cikin bayinsa ba kamar yadda dalilai suka nununa
WALLAHU TA'ALA A'ALAM
Mυѕтαρнα Uѕмαn
08032531505
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi.
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.