Shin Yi Wa Mamata Addu'a Da Sigar Jam'i Yana Kai Wa Kowannensu?

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu alaikum wa rahmatullah malam. Tambayata ita ce idan mutum yana da mamata da yawa in zai yi masu addu'a gaba ɗaya zata kai ma kowannesu ƙabarinsu?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa'alaikumus salam, ‘yar uwa yin addu'a ga jama'a masu yawa a sigar jam'i tana isa zuwa ga kowannensu kamar yadda idan aka ambaci sunayensu ma yake isa gare su.

    Addu'o'in da Annabi ﷺ ya yi, wani lokacin yakan yi a sigar mutum ɗaya, wani lokacin yakan yi a sigar jam'i. Saboda haka idan mutum ya ce Allah ya jiƙan iyayena da suka rasu, ko Allah ya jiƙan ‘ya’yana da suka rasu, ko Allah ya jiƙan duk musulman da suka riga mu gidan gaskiya, to ana fatan addu'ar za ta iske kowannensu gwargwadon yadda Allah ya so.

    Allah S.W.T ne mafi sani.

    Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.

    Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/CƘ9TMXMrWDx1y7sYye2znU

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.