Shin Zan Iya Auren Wanda ya yi Zina Dani?

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Saurayi Da Budurwane Sukayi Zina, Shin Za su Iya Aure Ko Akwai Wani Sharadi Dasai Anyi Tukun?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    الحمد لله الهادي إلى صراط القويم.

    Wajibi ne akan wanda ya yi zina yatuba zuwaga Allah, zina babban zunubine daka cikin manyan laifuka masu hallakarwa, wanda shari'a ta zo daharamcinsu datsoratarwa mai tsanani ga wanda ya aikatashi Allah maɗaukakin sarki Ya ce:

    ﻭَﺍﻟَّﺬِﻳﻦَ ﻻ ﻳَﺪْﻋُﻮﻥَ ﻣَﻊَ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﺇِﻟَﻬًﺎ ﺁﺧَﺮَ ﻭَﻻ ﻳَﻘْﺘُﻠُﻮﻥَ ﺍﻟﻨَّﻔْﺲَ ﺍﻟَّﺘِﻲ ﺣَﺮَّﻡَ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﺇِﻻ ﺑِﺎﻟْﺤَﻖِّ ﻭَﻻ ﻳَﺰْﻧُﻮﻥَ ﻭَﻣَﻦْ ﻳَﻔْﻌَﻞْ ﺫَﻟِﻚَ ﻳَﻠْﻖَ ﺃَﺛَﺎﻣًﺎ ﻳُﻀَﺎﻋَﻒْﻟَﻪُ ﺍﻟْﻌَﺬَﺍﺏُ ﻳَﻮْﻡَ ﺍﻟْﻘِﻴَﺎﻣَﺔِ ﻭَﻳَﺨْﻠُﺪْ ﻓِﻴﻪِ ﻣُﻬَﺎﻧًﺎ {سورة الفرقان.}

    Bayin Allah nagari sune waɗanda basa kiran Allah dawani wanda bashiba, basa kashe randa Allah yaharamta akashe sai inta can-canci kisan basa aikata laifin zina, duk wanda ya aikata dayan wadancan munanan Ayyuka zairiski zunubi maitarin yawa. za a ninka masa azaba ranar Alkiyama zai dawwana a cikinta awulakance.

    Sannan Allah yawajabta yiwa wanda yai zina uƙuba anan duniya ya ce:

    ﺍﻟﺰَّﺍﻧِﻴَﺔُ ﻭَﺍﻟﺰَّﺍﻧِﻲﻓَﺎﺟْﻠِﺪُﻭﺍ ﻛُﻞَّ ﻭَﺍﺣِﺪٍ ﻣِﻨْﻬُﻤَﺎ ﻣِﺎﺋَﺔَ ﺟَﻠْﺪَﺓٍ ﻭَﻻ ﺗَﺄْﺧُﺬْﻛُﻢْ ﺑِﻬِﻤَﺎ ﺭَﺃْﻓَﺔٌ ﻓِﻲ ﺩِﻳﻦِ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﺇِﻥْ ﻛُﻨﺘُﻢْ ﺗُﺆْﻣِﻨُﻮﻥَ ﺑِﺎﻟﻠَّﻪِ ﻭَﺍﻟْﻴَﻮْﻡِ ﺍﻵﺧِﺮِ ﻭَﻟْﻴَﺸْﻬَﺪْ ﻋَﺬَﺍﺑَﻬُﻤَﺎ ﻃَﺎﺋِﻔَﺔٌ ﻣِﻦْ ﺍﻟْﻤُﺆْﻣِﻨِﻴﻦَ ‏ {ﺍﻟﻨﻮﺭ/2.}

    Mazinaci da mazinaciya kowanne daka cikinsu aimasa bulala ɗari, kada a yi musu wani sassauci a cikin addinin Allah inhar kun yi imani da Allah daranar lahira wasu jama'a daka cikin muminai su shaidi bulalar daza'ai musu.

    Yazo daka Annabi Sallallahu Alaihi wasallam a cikin hadisi ya ce: (ku karbi hukunce hukunce daka gareni Allah yakawo musu mafita, Saurayi da budurwa idan sukai zina ai musu bulala ɗari datsarewa shekara guda, bazawara da mai aure bulala dari dajefewa.

    Muslim (3199)

    Allah yaharamta Auren mazinaci namijine ko mace, ga muminai ya ce:

    ﺍﻟﺰَّﺍﻧِﻲ ﻻ ﻳَﻨﻜِﺢُ ﺇﻻ ﺯَﺍﻧِﻴَﺔً ﺃَﻭْ ﻣُﺸْﺮِﻛَﺔً ﻭَﺍﻟﺰَّﺍﻧِﻴَﺔُ ﻻ ﻳَﻨﻜِﺤُﻬَﺎ ﺇِﻻ ﺯَﺍﻥٍ ﺃَﻭْ ﻣُﺸْﺮِﻙٌ ﻭَﺣُﺮِّﻡَ ﺫَﻟِﻚَ ﻋَﻠَﻰ ﺍﻟْﻤُﺆْﻣِﻨِﻴﻦَ ‏{ﺍﻟﻨﻮﺭ/ 3}

    Mazinaci kada ya auri kowa sai mazinaciya irinsa ko mushirika, mazinaciya bamai aurenta sai mazinaci irinta ko mushiriki, An haramtawa muminai aurensu.

    Mazinata idan suka tuba, tuba nagaskiya Allah zai karbi tubansu zaikuma share abun da suka aikata na laifin zina, Allah bayan ya Ambaci narkon azaba akan mazinata sa iya ce:

    ﺇِﻻ ﻣَﻦْ ﺗَﺎﺏَ ﻭَﺁﻣَﻦَ ﻭَﻋَﻤِﻞَ ﻋَﻤَﻼ ﺻَﺎﻟِﺤًﺎ ﻓَﺄُﻭْﻟَﺌِﻚَ ﻳُﺒَﺪِّﻝُ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﺳَﻴِّﺌَﺎﺗِﻬِﻢْ ﺣَﺴَﻨَﺎﺕٍﻭَﻛَﺎﻥَ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﻏَﻔُﻮﺭًﺍ ﺭَﺣِﻴﻤًﺎ . ﻭَﻣَﻦْ ﺗَﺎﺏَ ﻭَﻋَﻤِﻞَ ﺻَﺎﻟِﺤًﺎ ﻓَﺈِﻧَّﻪُ ﻳَﺘُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻰﺍﻟﻠَّﻪِ ﻣَﺘَﺎﺑًﺎ ‏{ ﺍﻟﻔﺮﻗﺎﻥ / 71-70.}

    Sai waɗanda suka tuba sukayi aiki nagari waɗannan tabbas Allah yana karɓan tubansu yacanja musu aikin da sukayi abaya yakoma kyakkyawan aiki Allah yakasance maiyawan gafara maijinkai.

    Idan kun tuba, tuba nagaskiya yahalatta kuyi aure tsakaninku.

    Abun da kawai zakuyi kafin kuyi auren shi ne sai kinyi istibra'i wato haila ɗaya, dan agane kinada ciki kobaki da ciki. Idan akwai ciki sai kin haihu sai kuyi aure.

    Duba fatawa jami'ah lil mar'atul muslimah (584)

    Yahalatta kuyi aure idan kun tuba, amma sai kinyi jini ɗaya dan agane kinada ciki ko babu, idan kinada ciki bai halatta kuyi aure ba sai kin haife ciki.

    Muna rokon Allah madaukakin sarki yatsare Al'ummar musulmi daka fada cikin zina dasauran munanan laifuka.

    WALLAHU A'ALAMU.

    Zauren Tambaya Da Amsa Abisa Alkur'ani Da Sunnah. Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.