Ta Sami Saɓani Tsakaninta Da Mahaifiyarta! Mene ne Mafita?

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu alaykum. Allah ya kara wa malam lafiya da nisan kwana. Malam !tambayata malam ita ce: Mahaifiya ce da 'yarta aka samu akasi aka samu matsala sai ita 'yar take cewa za ta je ta samu mahaifin maman nata ta fada masa abin da ya faru tsakaninta da mahaifiyar tata, sai mahaifiyar ta ce in kin fasa zuwa Allah ya tsine miki malam mene ne hukuncin tsinuwar? Malam kuma fa ba ta je wajen baban mamar tata ba malam, mene ne mafita?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa'alaikumus Salam, amin na gode da wannan addu'a. ‘yar'uwa abin da wannan ɗiya ta yi kuskure ne babba, bai dace mutum ya kai ƙarar mahaifansa ba ko da a wurin iyayen mahaifan ne, saboda yin haƙuri da abin da iyaye suke wa mutum ya fi masa alheri duk yadda ya kai ga rashin jin daɗin wannan abu, inda za a iya ɗaga ƙafa a kai ƙarar mahaifa wurin iyayensu shi ne inda iyayen suke take wa ‘ya’yansu wani haƙƙi na Shari'a da ba zai yiwu a bar abin a haka ba, ko suke saɓa wa Allah kuma aka tsoraci kada hakan ya kai su shiga wuta, misali iyaye Musulman da ba sa kiyaye Sallar Farillah, ko wasu haƙƙoƙin Allah makamantan haka, su ma ɗin ba kai ƙarar su za a fara yi ba, za a yi ta nuna masu haɗarin haka ɗin ne ta hikima da girmamawa, idan ya gagara ne sai a kai wurin waɗanda ake ganin ya dace.

    Yanzu wannan tsinuwa da ta yi wa ɗiyar ba a sani ba ko manufar tsinuwar har zuci ne ba, ko kuma a fatar baki ne kawai don ta hana ta zuwa wurin mahaifan nata ba, to mafita a nan ita ce ta je ta ƙasƙantar da kanta a wurin mahaifiyar ta ba ta haƙurin wannan ɓata mata rai da ta yi, idan kuma ba za ta iya zuwa ita kaɗai ba, to ta nemi waɗanda mahaifiyar take ganin girmansu su je tare a ba ta haƙuri, wannan shi ne mafita, kuma in Allah ya so za ta janye wannan kalma a kan ɗiyar.

    Allah ne mafi sani.

    Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.

    Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/Cnf26Ƙ8MPƙz9yUYU1nxƙRƙ

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.