Ticker

6/recent/ticker-posts

Tarihin Prof. Sa'idu Muhammad Gusau

Tarihin masana adabi, al’ada da harshen Hausa daga taskar Usman Muhammad Rabi’u A.D. (HAUSA BA DABO BA).

TARIHIN PROF. SA'IDU MUHAMMAD GUSAU

Daga
USMAN MUHAMMAD RABI'U A.D.
HAUSA BA DABO BA

Prof Sa'idu Muhammad Gusau

An haifi Sa’idu Muhammad Gusau a ranar 24 ga watan Maris 1952 a shiyyar Madawaki, bakin Masallacin Juma’a; unguwar Bube Attajiri da ke garin Gusau, Jihar Zamfara.

Farfesa Gusau ya fara karatun allon a gaban Mahaifinsa Malam Muhammadu Ɗankullum da Malam Husaini Kanoma da Malam Labbo Haruna Gummi da sauransu; inda har Allah ya sanya ya sauƙe Alƙurani mai tsarki tun yana da shekaru goma sha huɗu (14) a duniya.

Dagan aka sanya shi a makarantar Nizamiyya Islamiyya; a ƙofar gidan Ɗangaladiman Waziri Malam Attahiru daga 1965 zuwa Disamba 1969.

Ya zarce zuwa Kwalejin Sarkin Musulmi Abubakar, Sashen Koyar da Larabci da Addinin Musulunci (H.M.S) Sakkwato daga Janairu; 1970 zuwa Yuni, 1973.

A watan Oktoba na shekarar 1974 ya sami gurbin karatun Difloma a fannin Hausa da Larabci da Addinin Musulunci a Kwalejin Abdullahi Bayero Kano, kuma ya kammala a watan Yuni shekarar 1977.

Sannan ya ci gaba da karatun digirin farko (B.A Combined Honors) a Jami’ar Bayero Kano, daga Oktoba, 1977 zuwa Yuni 1980.

Bayan nan, sai ya sake komawa karatun digiri na biyu (M.A) a fannin Hausa daga Oktoba, 1982 zuwa Oktoba, 1983; A watan Mayu na shekarar 1989 ce ya kammala karatun digirinnsa na uku (Ph.D) a fannin Hausa; a Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya.

Farfesa Gusau:

Ya koyar a Makarantar Firamare ta cikin garin Talatar Mafara, wato Township daga Satumba 1973 zuwa Satumba, 1974. Ya koyar a Makarantar Horon Malamai ta U.P.E Wasugu, a shekarar 1977.

Sannan ya yi karantarwa a Kwalejin Larabci (S.A.S) daga Agusta, 1980 zuwa Yuli, 1981.

Farfesa Gusau ya riƙe muƙamin Mataimakin Shugaban Makarantar Horon Malamai (G.T.C) Zuru daga 1981 zuwa Satumba, 1982. Ya taɓa zama Shugaban Sashen Hausa (H.O.D Hausa) a Babbar Kwalejin Horon Malamai (A.T.C), Maru daga 1984 zuwa Satumba, 1985.

Daga watan Yuni na shekarar 1990 ya juya aikinsa na koyarwa zuwa Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya a Jami’ar Bayero Kano, a matsayin Malami mai daraja ta ɗaya.

A shekarar 1991, ya zama Babban Malamin Jami’a, sai a shekarar 1995 aka ɗaga shi gaba ya zama Mataimakin Farfesa. A ranar ɗaya ga watan Oktoba, 2000 ya zama Farfesa.

Farfesa Gusau ya yi rubuce-rubuce da dama a cikin muƙalu da rubuta littattafai da dama waɗanda suka shafi Hausa da kuma na Addinin Musulunci. Ya kuma halarci tarukan ƙara wa juna sani da dama, kuma ya gabatar da muƙalu da dama a tarukan.

Yanzu haka yana zaune a Kano tare da iyalansa (matansa da ‘ya’yansa da jikokinsa) (Gusau, 2020:91-92).

Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Yabo Gonar Makaɗi.

Post a Comment

0 Comments