𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Asalamu'Alaikum Malan inada Tambaya Kamar Haka Malan Tsakanin Liman Da Ladani Waye Yafi Samun Lada Awajan ALLAh.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
An sami Saɓani Akan Wannan Mas'alar. Wasu Suna
Ganin Ladan ya fi Liamn Samun Lada. Waɗansu kuma suna Ganin Liman ya fi Ladan
Samun lada.
Wadanda suke
Ce ladani ya fi Limami Samun Lada suna ganin Cewar!
👉 Duk wanda ya Ji kiran sallah, Kuma ya zo ya yi sallah ko
ya tashi ya yi sallah, ko da ba a Wannan Masallcin ba, To fa Malam Ladan yana
da Lada Akansa. Sabida ya Tunatar da shi Cewar lokacin sallah yayi.
👉 Duk wanda ya Ji kiran sallarsa zai Bayar da Sheda akan
Sa a Ranar Alkiyama. Hatta Mala'iku Zasu Bayar da Shedar Ladani a Ranar
Alkiyama. Haka Dabbobi da Tsuntsaye da Kwari da Aljanu.
👉 Ladan yana Tayar da Mutane daga barci don su Bautawa
Allah. Har da Shi Kansa Limamin Malam Ladan Ne yake Tayar da shi.
👉 Ladani yana Korar Shaiɗanun Aljanu a Daidai Lokacin da
suka Ji Kiran sallar da yakeyi.
👉 Ladan Zai Kira Sallah kuma ya Jira har zuwa Lokacin
Sallah yayi, Har Zuwan Limami Wannan Masallacin. Shima wannan Jiran da Ladan
zaiyi, Ana Rubuta Masa cikakken Ladan sallah.
👉 Ladani Shi ne wanda zai zo ya Buɗe Masallaci ya tsaftace shi, ya Kunna Futulun Masallci. Wani Lokacin ma ya share Masallcin Kafin Zuwan Kowa da Kowa.
HUJJAR WAƊANDA SUKE GANIN LIMAMI YA FI LADANI SAMUN LADA SHI NE.
👉 Shi Limanci Aikin Annabawa ne. Daga wannan Ban san Wani Abu ba. Sabida haka Da Kace Wanene ya fi Daraja Tsakanin Liman da Ladan, Kai Tsaye Zance maka Liman Shi ne Mai Daraja ta Farko. Amma Samun lada Kam Ina Ganin Kamar Malam Ladan Yafi Malam Liman Samun Lada. Amma a tawa Fahimtar Fa. Sabida Manzon Allah ﷺ Ya ce DA MUTANE SUN SAN abin da YA KE CIKIN LADANCI NA DARAJA , Ma'ana Kafin ka zama Ladani, DA SAI an yi ƘURI'AH SANNAN IDAN KA CINYE ZA KA ZAMA LADANI.
Allah shi ne Masani.
Zauren Tambaya
Da Amsa Abisa Alkur'ani Da Sunnah. Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Za ku iya
bi ta Links ɗin mu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/BSA30hdZD7V3WSJF8WVwUj
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi.
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.