Ticker

WAƊANNE SALLOLI NE MAI HAILA TAKE RAMA SU?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓

Assalamu alaikum malam don allah ina da tambaya, mene ne hukuncin macen da jinin haila ya dauke mata,cikin dare, shin za ta rama sallolin da ba ta yi ba a na ranar ko ba za ta rama ba?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salámu, malamai sun ce idan mai haila ta sami tsarki a bayan shigowar lokacin sallar Isha'i, to hakan ya lizimta mata yin sallar Isha'i, sannan kuma ya lizinmta mata yin sallar Magriba, saboda ana iya haɗa sallar Magriba da Isha'i a lokaci ɗaya a halin uzuri.


Haka nan, idan ta sami tsarki a bayan shigowar lokacin sallar La'asar, to a nan ma za ta yi sallar Azuhur da La'asar, saboda su ma Azuhur da La'asar ana iya haɗa su a lokacin halin uzuri.


Abdullahi bn Qudama Almaqdisiy ya ce: "Idan mai haila ta sami tsarki kafin faɗuwar Rana, to za ta yi sallar Azuhur da La'asar, idan kuma ta yi tsarki kafin ketowar Alfijir, to za ta yi sallar Magriba da Isha'i, saboda abin da Athram da Ibn Munzhir da wasunsu suka ruwaito da isnadinsu daga Abdurrahman bn Auf, da kuma Abdullahi bn Abbas, lallai su biyun nan sun ce a game da mai hailar da ta sami tsarki kafin ketowar Alfijir da gwargwadon raka'a ɗaya, za ta yi sallar Magriba da Isha'i, idan kuma ta sami tsarki kafin faɗuwar Rana, to za ta yi sallar Azuhur da La'asar gaba ɗaya, domin lokacin ta farkon shi ne lokacin na biyun a halin uzuri...".

Duba Almugniy (1/238).


Amma idan ta yi tsarki a bayan lokacin Asubahi ko bayan lokacin Azuhur, ko bayan lokacin Magriba, to a nan ba za ta yi sallah ba sai guda ɗaya, wato ita ce sallar da ta sami tsarki a lokacinta, saboda Asubahi da Azuhur da Magriba ba a haɗa kowace sallah da ɗayansu da take kafin su. Saboda haka 'yar uwa, macen da haila ta ɗauke mata cikin dare kafin ketowar Alfijir, to za ta rama sallar Magriba da Isha'i a bisa lura da wannan fahimtar.


Allah S.W.T ne mafi sanin daidai.


Jamilu Ibrahim, Zaria.


Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah, ta fahimtar magabatan kwarai.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/Du5LNx31U9hDi6RQbbrzgW

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments