Wacce Addu’a Ya Kamata A Riƙa Yi Wa Ƙananan Yara?

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu alaikum, malam don Allah ina da tambaya, shin akwai wata addu'a da ake ma jaririya a farji idan an haife ta, namiji ba zai taɓa kusantar ta ba in dai ba mijinta ba ne?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Ni dai a iya ɗan ƙaramin sanin da Allah ya ba ni ban san wannan addu'a ba, kuma ban taɓa jin ko labarinta a wajen malamai ba, sai dai kawai abin da na san ya tabbata daga Annabi ﷺ shi ne abin da Imamul Bukhariy ya ruwaito, wato hadisin Abdullahi ɗan Abbas cewa Annabi ﷺ yana nema wa jikokinsa Alhasan da Alhusain tsari da wannan addu'a kamar haka:

    "أُعِيْذُكُمَا بِكَلِمَاتِ اللَّهِ التَّامَّةِ مِنْ كُلِّ شَيْطَانٍ وَهَامَّةٍ وَمِنْ كُلِّ عَيْنٍ لَامَّةٍ".

    Ma'ana:

    Ina neman maku tsari da kalmomin Allah cikakku daga dukkan shaiɗani, da dukkan wata dabba mai dafi, da kuma dukkan wani kambin ido mai cutarwa.

    Bukhariy a hadisi mai lamba 3371.

    Wanda ba zai iya yi da Larabci ba yana iya yi da Hausa, ko da duk harshen da mutum ya fi iyawa, idan da Larabci za a yi, kuma ya kasance yaro ne namiji shi kaɗai, wajen "أُعِيْذُكُمَا" sai a ce 'أُعِيذُكَ', idan kuma yarinya ce sai a ce 'أُعِيذُكِ', idan kuma yaran sun wuce biyu sai a ce 'أُعِيْذُكُمْ'.

    Wannan ita ce addu'ar da ake yi wa yara, wadda ta tabbata daga Manzon Allah ﷺ Kuma in Allah ya so duk wanda yake yawan yi wa 'ya'yansa wannan addu'a Allah zai tsare su daga dukkan cutarwar mai cutarwa mutum ko aljan. Allah ya sa mu dace.

    Allah ne mafi sani.

    Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.

    Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/BSA30hdZD7V3WSJF8WVwUj

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.