WACE DABBA CE TA FI FALALA WAJEN LAYYA?

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Wacce dabba ce ta fi falala wajan layya?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    الحمد لله وصلى الله على محمد وآله وصحبه وسلم.

    Malamai sun yi saɓani akan dabbar datafi falala wajan layya tafuskar nau'in dabbar, Magana mairinjayen dalili ita ce:

    Dabbar datafi falala wajan layyah ita ce, Rakumi, sannan sah, sannan tumaki da akuyoyi, idan mata ne taguwa tafi saniya, saniya tafi tunkiya, tunkiya tafi akuya.

    Saboda Abunda yatabbata acikin shihul bukhari ( 2001) daka Annabi sallallahu Alaihi wasallam wajan bayanin falalar juma'a ya ce: ( Wanda yai wanka rananr juma'a wankan janaba sannan yai sammako zuwa masallaci asa'ata farko kamar yagabatar da sadakar rakumine, wanda yaje asa'a tabiyu kamar yagabatar da sadakar sah ne, wanda yaje asa'a ta uku kamar yagabatar da rago mai ƙahone, wanda yaje asa'a ta huɗu kamar yagabatar da za kara ne, wanda yaje asa'a tabiyar kamar yagabatar da kwai ne, idan liman yafito mala'iku zasu halarto suji khuduba)

    WALLAHU A'ALAM

    Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah, ta fahimtar magabatan kwarai.

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi.

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

     

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.