Wai Meyasa Bana Samun Amsar Tambayata A Wannan Group?

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀��𝐀

    Assalamu Alaikum. Mal Khamis da fatan ka tashi lafiya. Allah ya saka da alkhairi bisa ga gudummawar da kake bayarwa a wannan group mai albarka. Muna karuwa sosai. Amma ina da ƙorafina a wannan group nakan turo tambaya a wannan group mai albarka amma bana samu amsa. Ko me ya sa haka?

    Nagode

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Walaikum sallam warahmatahi wabarkatahu

    To yar'uwa Kiyi haƙuri duk wanda yaga/taga ba Amsa tambayarta ba to Bai cika ka'idojin group ɗin bane.

    Inhar Allah ya sa kin cika ƙa'idojinda muka gindaya a cikin group kuma kin jiramu har muka samu lokaci toh In shã Allahu komai jimawa zakiga anbaki Amsa.

    Dalilanda ke kawo jinkirin Amsa tambayar suna da yawa Daga cikinsu shi ne: AJIZANCI NA ƊAN ADAM wato kamar mantuwa gajiyawa da sauransu. Da kuma YAWAITAR SAƘONNIN MUTANE ta yadda kafin ka kai ga buɗe sakon wasu saƙonnin sun sake shigowa, domin dazarar an buɗe sakon mutum idan ba a san amsarba nan take ana cewa ba a san amsarba Idan kuma fahimtar tambayarne ba a yi ba Ana sake neman karin bayani.

    ▪️Kasancewar tambayoyi sun yi mana yawa bamu amsa tambayar da muka amsa Irinta a cikin group.

    ▪️ Bamu amsa tambaya da ba tada muhimmanci kamar fassara suna ko fassara mafarki da sauransu.

    ▪️A facebook bamu Amsa Tambaya ta comments sai ta private chat (inbox).

    ▪️ A WhatsApp Bamu Amsa Tambaya ta voice ko ta voice call ko video call.

    ▪️ Bamu Amsa Tambaya ta kira (phone call) Ko ta text message ko ta e-mail.

    Ku sani cewa, gaskiya ba za mu iya Amsar Tambayar kowa da kowa ba, saboda Tambayoyin suna da yawa sosai. a kowace rana tambayoyi sun kan iya kai 50 ko sama da haka, To kunga ba za mu iya Amsar su duka ba. Saboda haka duk wanda bai samu Amsar tambayarsa ba, to ya yi haƙuri.

    Wannan shi ne bayani game da korafinku a takaice.

    Daga karshe, Ku taya mu Yaɗa wadannan Fatawoyin da muke turawa a wannan Group, domin Yaɗa ilimi yana daga cikin Abubuwan da suke kusanta bawa ga Mahalicci. Amma Kuji tsoron ALLAH, kada ku kwafa (copy) ku goge wani abu daga ciki, ko da Links ne. Ga wanda yaga Gyara Ku sanar damu.

    Yazo a hadisi cewa duk wanda ya yi nuni zuwa ga Aikin Alheri, Ladansa kamar wanda ya Aikata Alherin ne. Manzon Allah ﷺ Ya ce: Na rantse da Allah, Allah Ya shiryar da wani a dalilinka, yafi maka Alkairi sama da a baka jajayen raƙuma.

    "Ku Tunatar Domin Tunatarwa Tana Amfanar Mumini"

    [Ƙur'an/51:55]

    ALLAH Ya Kara mana ilimi Mai Amfani, ya sa mu Amfana da Ababen da muke Rubutawa da kuma karantawa, ALLAH Yarda damu da Ayyukan mu. Allah ya sa faɗakarwan nan ta Amfani Al'ummah ga baki ɗaya. ALLAH Ya sakawa kowa da mafificin Alkhairi. Ya haɗa fuskokinmu a cikin Aljannah.

    Ameen Ya Hayyu Ya Ƙayyum🤲🏻

    Daga Admin:

    𝐌𝐚𝐥. 𝐊𝐡𝐚𝐦𝐢𝐬 𝐘𝐮𝐬𝐮𝐟

    +2347042085123

    Zauren Tambaya Da Amsa Abisa Alkur'ani Da Sunnah. Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.