𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum. Mutane da yawa sun yi min fatawa game da hadisin da aka ce Annabi SAW ya ce: "Duk wanda ya siyar da kasa, amma bai mayar da kuɗin da ya samu a kasar ba, Allah ba zai sanya masa albarka ba" Shin ya inganta, in ya inganta mene ne ma'anarsa??
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikumus salam. Wannan hadisin Ibnu Majah ya rawaito shi daga Huzaifah dan Yaman a lambata ta : (2482) da kuma Imamu Ahmad a Musnad (17990).
Masana hadisi sun yi saɓani game da ingancinsa. Malamai da yawa sun raunana wannan hadisin kamar Zahbi a cikin Mizanul i'itidaal 1/212, ya ce hadisin da Imamu Ahmad ya rawaito "Munkar" ne, hadisi Munkar shi ne hadisin da mai rauni ya Saɓawa amintattu a riwaya.
An tambayi Ibnu Uthaimin akan wannan hadisin, sai ya ce akwai dalilai na Sharia waɗanda suke nuna bai inganta ba, saboda idan mutum ya siyar da abu yana da ikon da zai yi amfani da kuɗinsa a abin da ya ga dama, zai iya siyan wani abu daban da kuɗin, ko kuma ya yi Hajji da su.
Ibnul Kaisarani ya lissafa wannan hadisin a cikin hadisan karya, Muhammad bn Darwish ya ambaci wannan hadisin a littafinsa: أسنى المطالب في أحاديث مختلفة المراتب sai ya raunana shi a lamba ta (1360). Shi ma Sindy ya raunana shi a hashiyarsa da ya yiwa sunanu Ibnu Majah.
Duk da dinbin waɗanda suka raunana shi a cikin magabata da malaman zamani sai dai Suyudi da Sakhawy malaman Karni na goma sun inganta shi, haka Kuma Albani a Silsila sahiha 5/336.
Inganta hadisi da kuma raunana shi Ijtihadi ne wanda ake gina shi akan Ka'idoji sanannu, sai dai malamai da yawa na Usulul fiƙhi da na hadisi, suna ganin cewa, idan aka samu cin karo tsakanin wanda ya raunana da wanda ya inganta, to ana gabatar da maganar wanda ya raunana, saboda yana da wani ilimi na daban da ya ɓuya ga Wanda inganta.
In mun kaddara hadisin ya inganta, to za a ɗauke shi ne a matsayin mustabbi, saboda ka'ida sananniya a ilimin USUL "Duk hanin da ya zo a babin ladubba ana daukarsa a makaruhi, in ba an samu wani dalili da ya fitar da shi daga hakan ba", wannan yasa a iya bincikena ban samu malami magabaci da ya ce haramun ne yin hakan ba.
Bajimin malƙmin hadisi Abu Hatim a cikin littafinsa; العلل ya rinjayar da cewa wannan hadisin maganar Huzaifah dan Yaman ce, kamar yadda ya ambata a 6/122.
Allah ne mafi sani
Dr Jamilu Yusuf Zarewa
Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah, ta fahimtar magabatan kwarai.
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi.
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.