𝐓𝐀𝐌𝐁A𝐘𝐀❓
Assalamu
Alaikum. Da fatan Malam yana cikin koshi lafiya
Ina da
tambaya kamar haka: Abokina ne ya Saki matar sa shika ɗaya Sai aka daidaita ta
dawo suka cigaba da Zama
Bayan wani
lokaci mai tsayi sai wata matsala ta sake faruwa har ya sake ta Saki biyu a
lokaci ɗaya, Bayan ta gama Idda sai yake shirin mayar da ita akan yaji fatawar
wani Malami cewar wannan Saki biyu a lokaci ɗaya yana matsayin shika ɗaya.
Malam mene ne gaskiya akan wannan fatawar?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikumus
salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.
Gaskiya
nidai ban san wani Saɓanin malamai game da wanda ya yi irin wannan sakin ba. Abin
da na sani, kuma na karanta kuma na ji daga bakin Malamai shi ne duk wanda ya
saki matarsa saki uku daban daban, sakin nan uku sun tabbata a kansa, babu wani
saɓani.
Da ache saki
ukun ya yisu ne a cikin lafazi guda, to shi ne wasu Maluman suke da saɓani a
kansa, suna cewa ana ɗaukarsa amatsayin saki ɗaya. Amma shi ɗinma mafiya
rinjayen Maluman Ahlus Sunnah wal jama'ah sun tafi tabbatuwarsa.
Tun daga kan
mafiya rinjayen Sahabban Manzon Allah ﷺ har zuwa kan Maluman tabi'ai da kuma
Shugabannin Mazhabobin nan guda huɗu duk sun tafi akan cewa saki uku cikin
kalma guda saki ne na bidi'ah amma kuma ana tabbatar dashi akan saki uku ɗin.
Kamar yadda
kuma duk wanda ya saki matarsa saki uku daban daban, ararrabe ɗaya bayan ɗaya,
ko kuma ɗaya daban, biyu daban shima duk ana tanbatar dashi amatsayin saki ukun
ne, babu saɓani.
Don haka
babu damar komawa har sai bayan ta yi wani auren kuma sabon mijin ya yi cikakkiyar
saduwar aure da ita.
WALLAHU
A'ALAM.
Ga Masu Buƙatar
Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/GcU1I5wjOB18K4PA6eURƘƘ
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.